JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Abba ne gefen Asaad hakuri kurin yake bashi yana bashi baki, don ya jima da sanin cewar yana Son yarinyar tunda shi ba yaro bane, momy da aneesa suna zaune waje guda sai khalid dayaja tunga wayarsa kurin yake dannawa hankalinsa kwance.

Kusan awa guda kenan da suka kawota asibitin, kamar gawa haka suka daukota, saida akai rikicin gaske kafin aka ansheta saboda sunce case din rapping babban case ne saida d’an sanda suke duba mutum, Abba hankalinsa tashi yayi don in akace a sanyo yan sanda sunan sa ne zai lalace, siyasar sa kuma ta tab’u shiyasa yai duk yadda zaiyi aka ansheta, a ransa kuwa soyake ta farfad’o duk wanda yai wannan abun inhar acikin gidan yake babushi babu koma waye, yagaji da wannan masifar tayima yan aiki fyade acikin gidansa shekara hudu ana fama da abu guda to yagaji hakan, wannan karon dole ai bincike agano ko waye………..likitan da suka shiga da Jannah ce ta fito dayake macece fuskarta a kuntace kafin ma tai magana Abba da Asaad sun mik’e sunbi bayanta zuwa office, yadda kukasan tafasashen ruwa haka jikin Asaad ke kerma yana jijjiga, saida ta gama rubutu cikin file din Jannah sannan ta dago tana cewa, “Alhaji anzalinci yarinyar nan, wannan case d’in bai kamata abarshi haka ba, ka kuwa san irin raunin data samu? Anan asibitin gaskiya ban tab’a samun wanda akaima zalinci irin wannan yarinyar ba, ansaka karfi sosai wajen yimata fyad’en, don haka zamu kira police yanzu”

Ta fad’a tana fara danna telephone dake bisa table dinta, cikin zafin nama Abba ya dafe wayar cikin tsoro yake mata magiya yana cewa, “doctor ki rufa mun asiri wannan case din na cikin gidana ne,idan yan sanda suka shigo ciki ina cikin damuwa sosai, wallahi da kaina zan dauki tsatstsauran mataki akan koma waye,dole zanyi bincike sosai wannan abun bazai tafi haka ba insha Allahu”

Asaad yana jikin k’ofa ji yake kamar ya kwashe Abba da mari, taya za’ai ya hana a sanar da hukuma wannan abun, kodan ba yarsa bace akaima wa? Tausan kanshi da kanshi yake saboda komi ma zai iya faruwa idan ya bud’e baki yai magana, jayayya akaitayi tsakanin Abba da doctor daker da sidin goshi ta hakura sannan ta soma masu bayani.

“Ta samu tear in and out, mun kwashe awa wajen yimata d’inki, sannan abun ya bugeta sosai don tunda aka samu ta farfad’o fizge fizge kurin take in ba’a sa’a ba kwalwarta na iya tab’uwa, munyi dukkan abunda zamuyi yanzu haka Allurar bacci mukai mata saboda ta d’an samu natsuwa ko yayane, rashin yin baccin zai iya sawa zuciyarta ta buga zamu rik’eta anan na kwana biyu muga yana yin jikin nata, ga magunguna da ku siyo da allura sai bill din da zakuyi yanzu”

Abba ne ya amsa yana mata godiya suka fito, Asaad zubewa yai bakin kofar yana kerma hawaye na kwarara daga idonsa, “Abba mezance da iyayenta? Wane irin zalincine wannan akai mata,wallahi tallahi ko waye saina kashe shi! Bazan kyalesa ba kuma nasan ko waye zai aikata wannan abun…………”Aa Asaad wannan hukunci bakaine zakayi shi ba, kabar komi Hannuna wannan karon dole indauki mataki sosai akan wannan abun, kayi hakuri kar ka yanke hukunci cikin fushi,mu samu ta dawo hayyacinta shine fatan mu sannan duk abunda za’a sai ayi”

Daker ya shawo kanshi suka je suka biya kudin aka sai magungunan suka je suka ba nurse din dake cikin dakin, ta taga yake lek’enta hawaye masu zafi suna zubar mashi ba yadda Abba baiyyi dashi ba yazo suje gida k’iyawa yayi dole aka barshi nan shi kad’ai, daga baya aka turo babaah uwani don ta zauna da ita, a ranar usman shima ya kwanta mugun zazzab’i amai ba kakkautawa ba arziki shima aka kawosa ranga ranga, cikin shida Asaad an rasa wanda abun yafi dukansa saida ya kwana guda aka sallamesa yai muguwar rama kamar yai shekara yana ciwo,don yafi Asaad zabgewa ainun shi firgicewa yai gaba d’aya ma kamar wanda yafita hankalinsa,ko wanka bai karayi ba daga randa abun ya faru abinci sai Abba ya tsaresa sannan zaici kadan, ranar da aka cika kwana biyun na farka daga wannan dogon baccin.

Ahankali nake bud’e idona ina sauke su akan rufin silin din dakin, idanuna kawai nake juyawa ina kokarin gane inda nake Motsin da naji ne yasa na juyar da kaina gefe inda naji motsin, bakina da naji ya bushe yai mun nauyi naji nace, “Babah uwani”

A firgice ta juyo kaina ganin nice yasa ta saki hijabin da take linkewa tayo kaina a guje tana murna ga kuma hawaye nan sun cika idonta,
“Murjanatu kin farka ko? Sannu murja,sannunki ubangiji ya kara miki lafiya”

Kallonta nake kamar wadda tatashi daga hauka bangane metake fad’a ba, na dubi hannuna naga an saka carnula drip nata shiga, na dawo da kallona kanta cikin shakakkar muryata da bata fita sosai nace, “ina ne nan Babaah? Menene ya sameni ake samun ruwa?”

Kuka Babaah ta fashe dashi wiwi kamar karamar yarinya, sosai take kukan ta kasa cewa komi ban san me take ma kukan ba, sai na yunk’ura zan tashi naji na kasa bayana ya rik’e da k’uguna, sannan daga can k’asana naji ya daure ga wani zago zogi da nakeji a wajen, koma wa nayi na kwanta ina rufe idona na fara tunanin meya saman?tun daga safiya zuwa rana da marecen, fadana da yallab’ai,tafiyata dashi zuwa gidanmu, dawowar mu har zuwa fallasa soyayyarmu da mukai rabuwar mu dashi na tafi zuwa cikin gida, tiryan tiryan nake tuna komi naje na dafa indomi na dawo nayi fitsari tare da wankan tsarki,na koma dauko indomin na dawo daki…………..jinai zuciyata ta dage ta buga da karfin gaske, saboda abunda ya faru dani bayan kwanciyataa bacci cikin wata irin gigita na fasa wata irin k’araa mai sauti mai firgita duk wanda yajita, Babaah uwani aguje ta fita daga d’akin hannuna nasaka na fincike drip d’in tare da carnula jini ya samu damar fita ba kakkautawa, ihu kurin nake ina kururuwa ina dukan bango hular da aka sanya mun na fice gashina ya watse kuka kawai nake ina dukan bango, Babaah uwani ce suka dawo tare da doctor da Asaad sun tsorata matuka da ganina cikin wannan halin, doctor kasa tab’ani tayi saboda fizge fizgen da nake jinake dama in mutu bana son na bud’e idona inganni ina cikin wannan duniyar, “kaga ka rik’eta saka auduga danne hannunta dake zubar jinin, daman nasan hakan saita faru shiyasa nake zullumin farkawarta”

Inji doctor d’in kwalla ne suke layi a fuskar sa jikinsa na rawa ya iso inda nake, k’amshin turarensa na naji ya sake haukata yana yina saboda shine abunda hancina yaji mun alokacin da ake aikata mun wannan zalincin, wata irin bangaza nai masa ina son dirowa daga gadon, kokowa muke dashi duk karfinsa amman ina neman gagararsa yadda bake kuka nake zubar kwallah shima kwallar yake zubarwa, muryarsa na rawa yake mun magana.

“Please Jannah, please stop crying ki natsu bakida lafiya,don Allah ki natsu ki taimaka mun kibar wannan abun, bakida isassar lafiya karki jawo wani abun kuma”

Lallashina yake yayinda hawayensa suketa kwaranya ahankali kuma na fara sakin jikina saboda gajiyar danai, nishi nake ina jan numfashina dake neman daukewa, turarensa ne natsani injisa cikin hancina a duniya yanxu ba abunda nake tsana sama da turaren jikinsa, sannan na tsani inganni raye ban mutu ba, so nake ya sakeni yak’iya saboda gani yake sake buge bugen zanyi, cikin masifa da kufula na fizge ina cewa, “ka saken! Karabu dani nace!!, wayyo Allah na nashiga ukuna innalillahi wa inna ilahir raju’un, hazbunallahu wani imal wakil ya Allah na rok’eka ka dauki rayuwata, don Allah ka dauki rayuwata bazan iya ba Allah ka taimakeni na mutu, na tsani duniyar nan da duk mutanen dake cikinta, wayyo Allah na nabani na lala…………..hannunsa ya saka ya rufe mun bakina, duk kokarin kwacewar da nake na kasa, duk wanda ke dakin saida ya zubda kwallarsa kafin kuma Abba ya shigo shima hankalinsa tashe, yadda naketa kuka ina surutu duk da rufen bakina dayai baisaka na fasa maganganun ba, zuwa can kuma naji juwa na daukata numfashina yana daukewa daga haka ban sake sanin inda kaina yake ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button