JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Gani yallab’ai”

Kallona kurin yake yi har saida na risinar da idanuna can k’asa k’asa yace, “shine zaki tafi kibarni”

Wani irin ras ras zuciyata tayi idona akansa yana wani lumshesu yace, “bamuyi ban kwana ba fa”

Na sadda kaina ahankali nace, “yanzu zaka tafi ne?”

“Aa na fasa sai naga kinfara zuwa makaranta,”

Kasa kallon sa nayi kaina k’asa nace, “ba kace zaka had’ani da yallab’ai usman ba”

Muryarsa ta canxa sosai bacin ya matso kusadani har naji sautin maganar ya daki fuskata, yake cewa “Aa bazan iya ba, gara na ida ladata”
Saurin dagowa nai ina kallon cikin idonsa zuciyata fat fat take bugawa, meyasa ya canza haka? Sauke idona nai nace “zan……zan tafi……kar….taga na dad’e”

Iska yaja sannan yace, “inhar ina gari dakina yana cikin aikin ki pls, ki ringa gyara mun”

Abunda bai tab’a yi mun ba tunda ya daukoni shine rik’o hannuna wani azabar shock naji,idona a awaje na tsura masa su shima yana kallon nawa idanun, can kasa kasa yace “kibar kallona haka ki anshi abunda nake baki”

Saurin ansar key din da yake damun nayi na mik’e zunbur ya sake rik’eni yana fiddo wata yar mitsilar waya kamar loma yace, “duk sadda kike son jina call me, bacin ni ban ceki kira kowa ba kinajina?”

A tsorace nake kar wani yazo ya iskemu na daga kaina kurin kamar kadangaruwa, murmushi yayi yace “by by zan fita sai dare zan dawo”

Kwatanta mun hanyar da zanbi inje bangaren su babaah uwani yayi sannan na tafi jikin yana tsuma ina kerma, wannan wani sabon abune da ban san sa ba baitab’a mun ba tsawon kwana biyun da mukai tare…………………….

Mom muhseen✍????
[7/29, 3:22 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......11

Kamar wasa na fara sabuwar rayuwa a inda ko amafarki ban tab’a tsammani ba, idan na tuno kauyen mu na kuma kalli inda nake zaune sai dai ince ma Allah Alhamdulillahi, sai yanzu nake ganin yallab’ai Asaad baida wata manufa ta kawoni gidansu face cigaban rayuwata, domin daga sadda nazo zuwa yanzu ni kaina naji na d’an canza ba takurawa ko kadan, idan kaga an zageka kai kayi ba daidai ba ina fatan Allah ya bani ikon yimunsu daidai bakin kokarina, dakina kamar dakin amarya haka yake single room ne mai dauke da madaidaicin gado 6by6, ga wadrope mai guda biyu ta gadon sai madubi da toilet, babu abunda babu acikin dakin, har Ac dai akwai sannan sutura gasunan an aje sai dai ja zab’i wanda nakeso na sanya, wasu sun mun yawa saina ware su na aje idan na samu dama naje ga tela ya gyara mun,b’angaren aikina kuwa na saki jiki bakin rai bakin fama ina koyo don ma Allah yayini mai saurin fahimta, idan naga kuma abun zai mun wahala saina rubuta yadda bazan mance ba, inajin dadin aiki da babaah uwani matar akwai kirki ta daukeni kamar yarta, nima haka nakejin ta kamar innamu, kwana na biyu da zuwa mukaje da yallab’ai makarantar da zan cigaba da zuwa yai mun dukkan abunda ya kamata aka bani A class ss2, duk daukata makarantar gwamnati zai kaini sai na ganni wata Private ta had’u makatantar sosai gaskiya, a ranar kuma yai mun register a wata islamiyya dake nan cikin unguwar ba nisa sosai amman duk da haka sai na hau abun hawa kafin naje, washegari kuma saiga uniform dana bokon dana islamiyyar ina kitchen lokacin da daddare ne abunda zanyi ma Abba tuwon alkama da miyar danyar kub’ewa, shiyasa babaah uwani ta sakar mun aikin saboda ganin nayi masa ranar danazo ba asamu wata damuwa ba, miyar nake had’awa lokacin tasha naman karamar dabba sai k’amshi take sai naji kamar mutum tsaye bayana, gabana yai mugun fad’uwa saurin juyawa nai a firgice har ina yadda ma burkin hannuna,
Wannan sarkin ikon ne yallab’ai khalid ga isa da shegen fad’a, sannan ya faye kallo da yawa.

“Ohhh I’m sorry na baki tsoro ko?”

Ajiyar zuciya na sauke ahankali ina risinawa wajen ce masa,

“Ina wuni yallab’ai”

Wajen frig ya wuce yana bud’ewa yace, “lafiya, me kike girkawa?”

Cikin rashin sakin jiki dashi nace, “Abba nake ma tuwo na gama miyar nake kad’awa”

Jinjina kai yayi yana zuba ruwan a cup yana sha, so nake yabar kitchen din na cigaba da aikina, ina juyawa zai cigaba da kallona hakan yana samun faduwar gaba………”ki cigaba da aikin ki mana”

Jikina a amace na juya ina cigaba da aikin amman tabbas inaji ajikina kallona yakeyi, Allah ne ya ceceni ya jefo yallab’ai Asaad kitchen d’in, yana ganin sa yaja wani dogon tsaki yana wuce wa ya fice binsa da kallo yallab’ai Asaad yai harya fice, kashe gas din nayi ina juyowa muka had’a ido fuskar sa babu annuri yake kallona, sai na sadda kaina k’asa ina risinawa nace,

“Ina wuni yallab’ai”

Kin ansawa yai ya juya yana cewa “ki sa meni part din”

Dafe kirjina nayi ina ambaton sunan Allah, wadannan mazan suna son haukatani, shirya tuwon nai cikin wormers miyar ma na juye ta cikin cooler na jera su cikin wani dogon tire kayatacce sannan na dauka na nufi can bangaren momy saboda da dare acan yake dinner,
Knocking nayi daga bakin k’ofar, bud’ewa akai naga Anty Aneesa na gaidata tana yatsina ta amsa mun,

“Daman Abincin Abba ne na kammala”

Hanya ta bani na wuce cikin falon momyn tana zaune kafa daya kan d’aya, na isa inda nake ajewa na ajiye ina risinawa na gaidata,

“Momy ina wuni”

“Lafiya lau jannah sannu da kokari”

Na amsa mata da “yawwa nagode”

Har nakai k’ofa zan fita naji tace mun,

“Jannah zonan?”

Cikin ladabi na dawo na durk’usa k’asa gabanta, Aneesa nata danna wayarta, yanzu ko kallona bata sonyi inko tsotsai yasa muka had’a ido to na shiga ukuna don idan lailayo zagi ta narka mun sai naji kamar na fashe da kuka, shiyasa ko hanya bana son tana had’amu da ita………….”khalid ya mun korafi bakya gyara masa dakinsa”

Kaina k’asa nace, “momy daman baki lissafa mun da dakinsa ba shiyasa, amman kiyi hkr zan fara daga gob………..don uwarki sai an lissafa miki? Keba yar boyi boyi bace?”

“Aneesa ya Isa haka bana son hauka”

Momyn ta katseta da fad’ar haka, ban dago ba amman zagin ya b’ata mun rai uffan bance ba saida momyn tace,

“Daga goben ki fara kinjiko?”

Kwalla ya cika idona nace a raunane, “insha Allah”

Haka na fito ina had’e hanya harna kusa dakina na natuna da kiran da yallab’ai Asaad yai mun, saida na goge kwallar sosai sannan na tura k’ofar na shiga, sassanyen kamshin falon da sanyin Ac ya ratsani sai naji na dan samu saukin ciwon da ke zuciyata, kwance yake cikin doguwar kujera ga tv nata surutu kwallo ce yake kallo,ya dora hannunsa saman goshi sa idonsa rufe sallama nayi na durk’usa daga gefen kujerar da yake muryata tai sanyi kalau nace,

“Yallab’ai gani”

Kamar baijiba ya jima baice komi ba sai can ya ce ba tare daya motsa daga yadda yake ba,

“Sai yanzu kika ga damar zuwa”

Cikin sauri da son kare kaina “Aa wallahi momy ta tsayar dani bada niyya nayi ba kayi hakuri”

Sai lokacin ya bud’e idonsa yana kallona na sadda kaina kurin, naji yana mun mgana ahankaki, “me ya samu muryarki? Kinyi kuka ko?”

Kasa had’a ido nai dashi ina girgiza kai nace, “Aa babu komi”

“Karki koyi karya pls”

Bance komi ba kuma ban dago da kaina ba,tome zance masa? Ince masa Aneesa na zagina? Na had’a su fad’a daga zuwana, aa bai dace ba dole na koyi kauda abu da b’oyesa araina.

“Kayanki na amso miki gasunan ranar monday zaki fara zuwa makarantar, ranar kuma zan tafi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button