JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Shigar nayi gaba ya bud’e baya ya aje jikkata sannan ya rufe bai shigo ba naji ya tsaya yana waya, duk abunda ya faru yake sanar da Abba wanda yakai sati biyu baya garin, ko kadan abunda ya faru bai mun dad’i ba Allah yaga zuciyata bana nufin kawo rikici acikin gidan su.


“A yanzu ne lokacin da ya dace na dauki mummunan mataki akan wad’anan yaran, daman shirun da nayi bayana nufin abun baya mun ciwo bane, na bari abun yazo irin wannan matakin don haka ku dukan ku ban ce wani yayi yunk’urin yin wani abu ba sai abunda na baku oda, ku sanya idanunku daga nan har sadda zai dawo da ita koma ina zai kaita, yadda uwarsu tabar gidan hai hata hai hata suma sai sun barsa har abadan abidina, uban da suke tak’ama dashi har suke izgilanci suke mun abunda suka gadama na rantse da Wanda ya busa raina saina rabasu dashi”

Wata dariya khalid da fareeda sukai yana cewa, “yanzu nakejin ki uwata mai kaunata, wannan shine abunda ya dace kiyi mu kuma zamu zauna dakon jiran umurninki”

Fareeda tace, “momy hankalina bazai kwanta ba muddin baki had’a da wannan jajakuwar yarinyar ba, tsanar da nake mata zai iya sani nasa aka kashe shegiya”

Murmushi momyn tayi tace, “yaro dai yarone, inkika kasheta aka ganoki kema kashekin za’ai, tunda nace ku saurareni ku jira lokaci.”

“Banso tabar gidan nan ban lasheta ba, tunda na dora idona akanta banda wani buri sai ganin na lashi zumarta, kyawunta kadai ya isa yaja hankalin duk wani lafiyayyen namiji akanta………..khalid ka rufen baki marar kunya kawai, koda wasa karna sakejin wannan maganar bakinka ku tashi kuje na gama magana daku”……………..

ina sake bawa masoyana hakuri akan wannan jinkirin, kun san komi saida lafiya ina fatan Allah yasa lafiyar ta dore na cigaba da muku posting, gashi nan dai babu yawa ayi hkr

Mom muhseen✍????
[8/14, 5:13 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.........17

Karfe tara muka iso wani gida mai kyau babban get ne aka bud’e mana muka shiga ciki, tashin ginin yai mana sallama duk yadda nake cikin rud’ani bai hana ni ganin tsananin kyan ginin ba, fuska duk hawaye sun bushe na kallesa, hararata yayi yana cewa “akoke kawai, ke komi na kuka ne wajenki”

Na sadda kaina kurin bance masa komi ba, bud’ewa yai yafito ya zagayo ya bud’e mun, kallon sa kufin nake da mamaki sometimes ina mamakin wasu abubuwan daga garesa……..”malama fito don Allah karki cinyeni da kallo”

Fitowar nayi ya zaga ya dauki jikkata dake baya ssnnan na bisa baya ina ta yaba gidan daya dauki hankalina, fitilune ta ko ina kuma akwai bene can sama gidan gaskiya babu karya binsa nai tayi har muka ratsa cikin babban falon inda mukai sallama.

Wata farar mata ce da yara guda biyu mace da namiji, sai kuma maigidan shima yana nan kallo guda nai masa naga fuskar yallab’ai Asaad ajikin tashi, mamaki sosai ya kamani yayin da dan danan matar da yaran suka fara murnar ganin mu, ko ince ganin yaya usy saboda ni basu sanni ba,

“Usy dan mama kaine da daren nan? Sannun ku karaso nan yan mata ki zauna”

Matar ta fad’a cikin sand’a na isa na zauna gefenta ina gaida ta,

“Lafiya lau yan mata, usy ina ka samu kyakkyawa haka”

Yaran duk sun baibaye shi suna masa surutu babansu ne yai musu magana sannan suka natsu, cikin ladabi na gaida shi shima ya amsa mun cikin faram faram sunata jan yaya usy da tsokana.

“Anty bakuwa na kawo miki zatai miki kwana biyu sunan ta Jannah”

Tana ta dariya tace, “masha Allah suna mai dadi, ba komi usyn mama”

Tatashi ta wuce kitchen don kawo musu wani abun, ya dubin yayan nashi yace kasa-kasa “yaya itace ajiyar Bros fa”

Zaro ido yayi yace, “dagaske usy?”

Murmushi yayi yana cews “wallahi kuwa yaya, to ya kaganta?”

Duk a munafurce suke maganar, murmushi yayi yace “shegen nan ya iya gane gane har ya gano wannan tsaleliyar haka, amman miye labari nasan akwai dalilin kawota nan?”

“Muje ciki kaji komi yadda akai,nama sanar da Abba don kar ya koma ta tsara masa munafurci”

Tashi sukai yaya usy na cemin “bari na zo jannah”

Rausayar dakai kurin nayi suka barni nan ni kadai har ta dawo,
“Ayya jannah ke kadai ko”

Ina murmushi nace “babu komi Anty”

Lafiyayyen Irish ne soyayye da kwai ga yar sos a sama anyita da kifi, sai kuma dambun nama da ruwa da lemu, jinai yunwa tai mun sallama inhar ina nan bazan sake ba har naci na koshi, sai nace mata “Anty inaso nayi sallar isha sannan”

Tace”to ba damuwa muje ciki inkika gama saiki acan zaifi”

Dasu ta bini ni kuma na dauki jikkata nabita, gidan karshe ne wajen had’uwa gaskiya, daki guda ne yaji kayan gado masu kyau ga labulaye nan da fitilu masha Allah, tace “to ga toilet nan inkina bukatar abu don Allah kimun magana karkiji komi”

Nace”to Anty nagode sosai”

Zama nai naci nai hani’an saboda sosai nakejin yinwa tun kalacin safe banci komi ba, nai hamdala naje na wanke bakina na dauki kayan na fidda kitchen din na same ta ansa tayi tace, “aida kin barsu zanzo na dauka”

Nace”Aa haba ni miye amfanina”

Wanke wanke take na tayata munayi har muka gama muna fitowa suma suka fito yaya usy yace, “Anty munirat ni zan wuce dare na karayi zan dawo gobe na duba ajiyata”

Tace”to usyn mama saika dawo din, kanaji da wannan ajiyar taka dai karka damu zan kula maka da ita”

Had’a ido mukai dashi yace, “zaki rakani ko?”

Ya na iya dole nabisa zuwa inda ya aje motar tashi tsaye yai ya rungume hannu yana kallona sai naga tamkar yallab’ai ne yake kallona, sadda kai nayi bance komi ba saida ya gaji naji yace,

“Baki tambaye ni nan ina ne ba”

Nace”ai nasan ba zaka tafi ba saika sanar dani”

Murmushi yayi yana cewa, “Jannah kenan, nan gidan yayana ne mai bin Bros sunan sa Hisham, zaki zauna dasu har sai wannan ramar dakikai ta koma inba haka ba bazaki koma wancen gidan ba Allah ko”

Zaro idanuna nayi yace”yes haka nake nufi, don haka ki saki jikinki nan ma gidane ba abunda zaki nema ki rasa kuma su sunada kirki ba kamar wadancen ba”

Na rausayar dakai bance komi ba,

“Watau bazakiyi magana ba kenan”

Murmushi nayi saboda nasan haushin wannan shirun da nake masa yake nace, “to yaya usy zan zauna din nagode sosai da kulawa”

Iska yaja sannan yace “zan ringa zuwa kullin ina ganinki”

Saurin kallonsa nai saboda yadda yai maganar so silent gently, sai na maida kaina kasa nace “to yaya usee Allah ya kaimu”

Lumshe idonsa yayi yana cewa, “duk uniforms dinki suna nan na sanyo miki, gobe zanzo mu wuce school”

Nan ma rausayar dakai nayi, kamar bazai tafi ba daker dai ya shiga motar yace “Good night jannah”

Daker na kakalo maganar nace, “ok by”

Saida ya fita nikuma na koma cikin gidan zuciyata cike da wasu abubuwa da na kasa ganesu.


Lamarin yaya usee ya fara daure mun kai abubuwa ne yake mun da kwalwata ta kasa daukar su, kaina yana kullewa ba wani abune na tashin hankali ba amman hakan yana rikita ni, misali yawan kallon da yake mun ina yana mun magana kamar yana lallashina, duk wani abu daya shafeni cikin hanzari yake yinsa idan muna zaune ko muna wani darasin yaita jan abun saboda kar agama da wuri, tun da nazo gidan yaya Hisham shine zai kaini makaranta ya kaini islamiyya, shine siyo mun wancen kawo mun wancen daidai da rana guda bai tab’a mun maganar yallab’ai Asaad ba, rannan da na cika sati biyu agidan na rakosa xai tafi da daddare na kasa hakurin danne abunda yake damuna tun tafiyar yallab’ai, kamar dai yadda ya saba yai shiru yana kallona sai nayi amfani da wannan damar nace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button