JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda uwata innamu ta haifani ban tab’ajin abu irin wanda nakeji yanzu ba, shi kanshi kukan da nake naji ya canza sauti sake makale jikina nayi, saboda yadda nakejin wani yammmm, bai fasa maganar ba kamar ba shine yake mun ihu akai ba……….

“Jannah don Allah, please kiyi shiru I’m very sorry, nine na Saki kuka ko?”

Kaina na d’aga masa kurin ya lumshe idonsa yana jan numfashi, “to kiyakuri, stop crying kinji bazan sake ba”

Tausasan kalamansa dole suka saka kukan ya dauke wanda bansan ya dauke ba naji dai nayi shiru, sai ajiyar zuciya nake ahankali duk fuskana tayi zufa nak’i dagowa daga d’uk’en da bake, zaman dirshen yai gabana yana sauke ajiyar zuciya ahankali har inajin ta cikin kunnuwa,

“Jannah”

Naji muryarsa da babu kwari acikinta ya kirani, can kasa na amsa mashi yasake cewa “dago fuskarki”

Kunya nakeji bazan iya kallon sa ba, kukafa nasha sosai gabansa taya zan iya dago kaina in kallesa, “bazan iya hana kaina dago da fuskarki ba muddin baki dago ba”

Jin haka yasa ba shiri na d’ago amman ko kusa ban kallesa ba, ajiyar zuciya kurin nake sauke, baisa sadda ya furta, “ya subhanalallah!”

Zufar da tai yasaka duk gashin ya kwanta na goshinta lashes dinta sun manne sun kwanta, lips dinta sunyi jaaa gaba d’aya wani annuri take fiddawa, runtse idonsa yai kamar zai haukace ya danne yana cewa “bani wayar”

Ahankali na dauko na mik’a masa.

Ansa yayi yana ajeta gefe saboda baya son sake ganin wadannan hotunan, sune suka gigitashi haka bai san zai iya mata fad’a sosai ba amman tsananin zafin da yakeji idan ya tuna yadda akai hotunan kamar zai haukace, shiru mukai mu duka nidai sai ajiyar rai nake gashi nayi mugun takura so nake ya sallameni, don zan iya rasa kaina anan gashi kuma banga alamar zai ce na tafi ba, muryata nake gyarawa don ta shak’e can kasa-kasa nace masa,

“Zan je nayi aiki”

Na fad’a ba tare dana dubi inda yai daman dirshen ba, tazarar mu babu nisa daga inda yake naji ya mun magana cikin sanyin rai,

“Zaki tafi idan kin dago kin kalleni,”

Kamar ya sake tun zirani na maida kaina cikin guiwata kawai, don wallahi bazan kalli cikin idonsa ba bacin ya gama mun masifa yazo ya sani kuka shine zai tilasta mun kallonsa, me hakan zai amfane sa.

“Au shine kika maida kanki,? Idan usman ne ai bazaki k’i kallonsa ba tunda gashi nan a pics dinku kun yi kyau”

Dajin yadda yai maganar abun yana masa ciwo, ban san me zance na kare kanmu ba, nidai nasan har zuciyata babu abunda ke tsakanina da yah usy,

“Wallahi summa tallahi babu abunda ke tsakanin……….tashi ki tafiyarki please”

Ya katseni daga maganar da nake, ban hakura ba naci gaba da cewa “Yallab’ai ko Anty munirat zaka tambaya……….I said get up!!!”

Aguje na fita daga bangaren nashi har in bangazar Aneesa ban sani ba, ban tsaya bi ta kanta ba nai wuce wa ta dakina, gado na fad’a ina sake rushewa da kuka matsananci ban ankara ba naji ankira magruba, saurin tashi nayi naje na wanke fuskata na canza kaya xuwa na aiki sannan na fito zuws kitchen nasan Abba yasaka ran cin tuwona yau, hindu muka had’u a hanya ta biyoni har kitchen d’in tana mun magana.

“Yadai malamata, naga fuskarki tayi jaa kamar jan kosai”

Murmushi nayi ina kunna gas na dora ruwan tuwan na bud’e frig don duba abunda ke akwai,nake cewa “ko kuma jan fanke ba”

Darewa tayi bisa cabinet d’in kitchen din tana cewa, “nifa ban gane ba, yah usman nacan na k’unci ke kuma naga fuskarki alamun kinsha kuka mekuke b’oyewa?”

D’anyen kifi da kayan miya na fiddo inso nayi masa miyar kub’ewa danga da kifi, na fara gyara kifin ina wanke shi nace, “babu komi fa,kin cika bincike”

“Ba wani bincike gaskiya nakeson sani, wallahi jannah duk wanda yaga idonki saiyace kinyi kuka karki b’oye mun pls,ki daukan yar uwa kuma kawarki,wata kila zan iya baki shawara”

Maganarta yasa naji kwalla sun silalo mun, nai saurin gogewa saida na gama wanke jifin na tsaneshi, na hau gyaran kayan miya zanyi greeting dinsu ta ansa tana yi mun, na dauko kub’ewar ina gurzawa kamar bazance komi ba na daure nace, “Hindu yallab’ai Asaad ne, na kasa fahinttar abunda yake zarginmu dashi, tunda ya sauka yau yake ta d’acin rai yanzu ba dad’ewa daga wajensa nake fad’a ya rufeni dashi, wai yah usy ya bud’e mun ido meke tsakanin mu, wallahi hindu babu komi tsakanin mu, shifa ya damk’a amanata hannunsa meyasa zayyi wannan abun, dan uwansa ne fa shin zaiji dadi yaji irin zargin da yake mana?”

“Kibar kukan hakanan don Allah, Yah Asaad tsoro yakeji Jannah koda bashine ba ko waye dole zaiji tsoron faruwar wani abun, ke ba kamar kowacce mace bace na shaida hakan, Allah yai miki kyawun da ko mace yar uwarki zataji kin dauke hankalinta, inaga namiji ba kowane namiji ne zai iya kauda kanshi akanki ba, kuma kina da tabbacin cewar shi yah usman bai da wani feeling akanki? Kin shiga zuciyarsa? Karkiyi saurin daukar zafi da Yah Asaad don Allah shi yana ganin akan daidai yake, duk sadda mukai waya dashi baida wata magana sai cewar kuyi karatu hindu shine kadai gatan da zamu iya tsaya maku kanshi, karatun y’a mace yana da matukar muhimmanci shiyasa nakawo jannah nan gidan ba domin aiki kad’ai ba, bana son tun kuna kananun ku soyayya ta rude maku idoku kasa yin karatu in kukai hakuri komi yana da lokacinsa, acikin kalamun sa na fahimci Yah Asaad baida wani buri a kanki Jannah face yaga kinyi karatu tuk’uru baya son wani abu ya d’auke miki hankali daga wannan burin”

Bada hankalina kad’ai nake sauraren hindu ba harda zuciyata da dukkan kunnuwana, kuma maganganun sun ratsani ainun nace mata “Hindu wallahi ko kadan Yah usy bai tab’a nuna mun yana sona ba, balle har bakisa yakai ga furtawa, yana bakin kokarinsa wajen ganin na iya dukkan abunda ake koyar dani, da taimakon sa na samu har nakai matakin dauko position dinda ban tab’a tsammani ba, nidai har raina nasan Yah usy ba sona yake ba”

Murmushi tayi tana cewa, “shikenan tunda kince haka, lokaci shine xai nuna mana hakan amman don Allah karkiji haushin Yah Asaad shine yake kan daidai”

Kusan tare mukai akin dinner da hindu, bayan na gama tuwon Abba muka d’ofa jullof d’in jallar makaroni mai kwai da alayyahu tasha magi sai k’amshi take, a ranar banga wani canji na b’acin rai akan fuskar kowa ba hasali ma santin girkina kawai ake, karma ace Abba don har kyauta yayi mun yaban dubu biyar, kud’in da nake samu bana komi dasu illa tarawa inaji araina kamar akwai ranar da zasuyi mun amfani, har albashina bana tab’a komi sai d’an abunda ba’a rasa ba, wanka na sake na gyara jikina nai shirin kwanciya sai ga kiransa…………….

Mom muhseen✍????
[8/20, 2:44 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......22

Kallon kiran nai tayi kamar shine a gabana, babu abinda yake dawo mun cikin kaina sai hirar mu da hindu d’azun, tabbas nasan yana da gaskiya aduk maganganun sa to Amma wannan zafin da ya d’auka yayi yawa, miye laifin yah usy fisabilillahi ya bashi amanata ya rik’e baitab’a cutar dani ba, duk da inaji kasan zuciyata cewar Yah usy he is in love for me, Amman banda tabbas d’in hakan tunda bai fito fili ya sanar dani ba, inhar dagasken sona yake miye laifina aibani na sanya shi yasoni ba dazai huce haushin sa akaina, wata zuciyar take ce mun “to in kishin ki yasa duk yake wannan abun fa?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button