JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Zama tayi gefen gadona tana cewa, “dakin ki tsaf tsaf gwanin sha’awa”

Ina murmushi na dauko nawa qur’an din na zauna na jingina ina cewa, “ai naki yafi nawa tsaf tsaf da yin kyau”

“To muyi musanya mana”

Na zaro ido ina yar dariya, “muyi karatu kinjiko da wuri zan tashi aikina yawa garai”

Mun fara karatun na cikin natsuwa ina biyawa tana nanatawa, haka mukai tayi har saida ta iya feji guda da ake binta, taita godiya tace “daga yau tare xamu ringa karatu har da sauran darussan pls jannah”

Na ce”laaa miye na wani please, ba wani abu indai kin samu lokaci sai muringayi irin wannan lokacin”

Daga haka taimun saida safe tatafi, nai addua na kwanta amman fafur idona babu bacci zuciyata ta bud’emun wani sabon shafin tunani yallab’ai, ban san har sai yaushe zuciyata zata ciresa ba saidai idan ban kad’aice ni kadai cikin tunani ba, a lissafina yanzu satin sa uku da tafiya zuwana gidan kuma nakai wata guda cib, inso samune naje gida amman karya nake nima na san ba zasu barni ba lokacin zuwana baiba, da tunanika kala kala barawo bacci ya saceni.

ina godiya da uzirin ku masoyana, ku kara hakuri dani kuna mun adduar samun lafiya insha Allahu dana idasa warkewa zaku jini akai akai, amman yanzu banyi alkawarin yin posting kullin ba wannan ma karfin haline ngd sosai????????

Mom muhseen✍????
[8/12, 3:37 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......16

Tun daga wannan lokacin nida Hindu muka zama abokai sosai har dakina zata sameni muyi fira sosai, don mun ware ranar da zamu ringa tilawa asabar da lahadi da daddare, saboda bana samun lokaci yanzu shukra sai taga dama take zuwa kuma ba komi takeyi ba, baba azumi kuma tayi tafiya zuwa kauyensu dagani sai babaah uwani kamar zan mutu idan akace Friday tazo, Fareeda da yaranta nan suke weekend dinsu kuma fa acikin garin nan take, ba karamar wuya nake ciba Allah ma yasani, shiyasa na rame sosai kayana duk sun mun yawa.

yaya usy rannan naga yanata kallona saboda yadda yaga duk na fige na lalace, time din na kawo ma momy gasashen naman da tasaka na gasa mata, fareeda ce take cewa bayan na juya baya zan shige ciki “momy wai baki lura da mutuniyarki ba? Duk ta bi ta k’are shegiyar”

Idonsu ya rufe sun mance da usman a falon momyn tana danna waya tanaa cin naman tace, “tukunna ma”

Murmushi fareeda tayi tana cewa, “ko kefa momy haka nake so, amman dai kinyi kamar bakisan meke faruwa ba”

Aneesa ce tai gyaran murya duk suka kalleta a siyasance tai masu nuni da usman dake cikin falon, mik’ewa kurin yai ya bar musu falon baice komi ba, kitchen na koma ina ta kokarin dora girkin dare ga gugar momy can dakina tana jirana kayan sunkai kala ashirin da biyar, in ban gamasu daga nan zuwa safe ba na shiga ukuna………..”Jannah”

Atsorace na juyo saboda ban zaci wani anan ba, kuma daman irin wanan lokacin khalid ke matsanta mun, yaya usy ne nai ajiyar zuciya nace “yah usy kana son wani abune”

Lumshe idonsa yai kamar yadda yallab’ai asaad keyi, naga kuma sunyi wani iri fuskar sa daure babu walwala cikin cunkusasshiyar murya yace, “mekikeyi?”

Nace”dinner zan had’a cus cus ce da miyar kaza sai salad dazan yanka yallab’ai khalid kuma yace yana son nai masa wainar fulawa”

Runtse idonsa yai yana kallona ya duba agogon kitchen din yace, “kinci abincin rana?”

Na girgiza kai ina sadda kaina kasa, ya sake cewa “kinyi sallar magriba?”

Nace”so nake na dora sai naje nayi”

Ransa a b’ace yace, “aje ki fito nan”

Idona a warwaje nace, “yallab’ai momy zatai fad’a idan ban girkin nan ba”

Wani kallo yai mun yace, “umurnin momy yafi nawa kenan? Nace umurninta yafi nau kenan saboda ita ke biyanki?”

Na rufe bakina kamar zan kuka nace “na ratse da Allah Aa yaya usy kayi hakuri”

Hanya ya nuna mun yace, “to zoki wuce muje”

Na aje komi jikina a mugun sanyaye na fito gaba ya sanyani har d’akina ya tsaya wurin mirrow yana kallona yace naje nai sallar, toilet na shiga nazo nayita duk yana cikin dakin, hankalina duk a tashe yake na sallame ko addua banba naga ya dauko mun wata jikka dake cikin dakin, ya bud’e wadrope dina ya dauko kaya ba adadi yanata zubawa, idona a warwaje na ke kallonsa harya gama sannan ya dubeni,

“Ki biyoni, salan kuma kiyi mun gardama”

Yai waje a guje na bisa bayan na rufe d’akin na dauko yar wayata da kullin saina duba kozan samu kiran yallab’ai asaad, afalon mukai karo da khalid yai mun wata fizga yana cewa,

“Gidan ubanwa zaki? Ina wainar danace kimun?………..saidai yaji ankaima hannunsa bugu daga fizgar dayai mun yaya usy ne kuma yai hakan, idonsa kamar wuta yake nuna sa da yatsa cikin kakkausar murya yace, “karka sake tab’a ta, ita ba asharariya bace irinka, waina kuma ha zatai ba aiba jakarku bace”

Ya nuna mun hanya yace “zoki wuce muje”

Fareeda tai saurin tashi tana shan gabansa tace, “ina zaka kaita usman? Ai nan shine dolenta tunda ta fito neman kudi, kuma dole tayi aiki kamar jakka tunda kudi take so, ko a banza zata samesu………..karki gaya mun magana ki kama kanki nan gidan mune, kije kiyi wannan ikon agidan mijinki amman ba nan ba, akan me zaku ringa azabtar da yarinya ehy? Meta tsare ku dashi to ba abunda ya dameki da inda zan kaita matsa ban waje”

Sororo take kallon sa tana nuna kanta zatai magana momy tace, “fareeda zoki wuce ciki”

Har ta fara magana tace, “momy yazaki………nace ki wuce ko”

Afusace tai cikin bangaren momyn khalid yace mun yana zaro mun idonsa, “wuce kije kimun abunda na sanya ki ko in karyaki anan wajen………..idon yaya usy jajawur jijiya tafito kansa sosai yace masa, “ba zatayi ba, ni nace ba zatai ba inka isa kai wani ne agidan nan don Allah ka tirsasata tayi………kai ni kake gaya ma magana zan ci ubanka yau inga abunda za’ai”

Dasauri momy tataso ta shiga tsakani ranta amugun b’ace cike da tsawa tace, “khalid shiga hankalinka nace ko! da usman din zakai fad’a kamar wani abokin ka?”

Cike da bala’i yace, “ehy dashi zanyi, ki kyale inci ubansa in ballashi inga abunda za’ai………..bakai ba ko ita bata isa ta tab’a fatar jikina dasunan duka ba, don Allah kaida ita inkun haihu bismilla”

Wannan tashin hankali tuni ya sanya ni kuka ba abunda jikina keyi banda rawa kamar mazari, fuskar momy kamar an aiko mata da sakon mutuwa bata tanka ma usman ba, ta figi hannun khalid tace “wuce kabar nan wajen inhar nina haifeka”

Kamar kubu buwa haka yabar falon, ta juyo da kallonta akansa suna ma juna wani irin kallo kamar zasu cinye juna, sannan tace “idan baka son jawo ma kanka tashin hankali ka aje wannan jikkar kabar wajen nan, Janna aiki tazo kuma dole tayi aiki agidan nan tunda ni nake biyanta ba kyauta take mun ba, idan kuma so kake tabar gidan nan shikenan ka dauketa ku fita kagani”

Ta juya zata bar wurin yace, “ke awa zaki koreta agidan nan? Idan abaya kin kori wasu ita wannan baki isaba, kuma aiki zata dawo ta cigaba dayi kamar yadda tafaro amman ba irin wannan ba da kuke sakata kamar baiwarku, wannan karon duk makircin ki karya kike.
Jannah zata dawo daram amman saita huta sannan”

Ya dubeni yace “tashi ke kuma”

Dole na tashi ina jan majina nabisa har compound, motarsa ya bud’e yana kallona “shiga”

Kukana ya sake dawowa sabo na had’e hannuwana alamun rok’o da magiya ina cewa, “yaya usy ka taimaki rayuwata don Allah kayi hakuri in koma, bazan so wani rikici ya barke agidan nan sabodani ba, banzo don na ruguza maku zaman lafiya ba don Allah…………please ya isheni don Allah ki shiga mota nace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button