JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajewa yai sannan ya d’an mun rad’a shima a hakan saida camera man ya dauka, bai damu ba yace mun “kinga kin korar mun yan mata na”

Zaro idona nai ina kallonsa, ya wani kashe ido guda yana cewa “dan sassauta pls sunyi mun girma da yawa”

Ba shiri na maida kaina k’asa, sannan akafara kokarin yanka cake d’in abokan sa sukaita karad’i ana wakar happy birthday, hannuna ya dora bisa nashi wanda ya rik’e wuk’ar dashi muka yanka tare, tafi akai tayi mana mai hoto bai huta ba shi kuma.
sannan ya cire wanda muka yanka tare ya nufo bakina dashi, marairaicewa nayi amman bai hana shi samun ga bakin ba, dole na gutsira sannan yabi abokansa yana basu wata dana lura tacika ta batse kiris ya rage ta fashe daya nufota sai kawai ta fice tabar wajen, atakaice dai ba a tashi wannan partyn ba sai eleven.

But d’insa da bayan motar cike suke da kyaututtuka kala-kala yunwa nakeji saboda banci komi ba a wajen banda lemu da guntun cake din daya bani, to amman bazan iya ce masa yunwar nakeji ba na bari mu isa gida bazan rasa abunci ba, tunda muka taho ba mai magana nidashi yayin da yake tukin kamar baida lakka ajikinsa, har saida nayi magana akan hakan.

“Yah usy baka da lafiya ne?”

Kamar jira yake yace “sosai ma”

Saurin kallon sa nai cike da son karin bayani, don nidai naga lafiya lau muka taho haka har aka gama partyn banga wani alamun rashin lafiya tattare dashi ba, na kasa hakuri nace “kamar ya? Bacin dazun kalau dinka kake”

Kamar zai kuka yace, “to yanzu kuma ba kalau nake ba jannah”

Na rausayar dakai kurin ban sake magana ba, naga alamar shagwab’ace kurin yakeji kuma ni bana cikin wadanda zai yima ita ehe,

“Bazaki tambayi meke damuna ba”

Ban Kulasa ba nace, “Allah ya sawak’a yah usy”

Murmushi yayi sunan da take kiransa dashi ba kadan yakejin dadinsa ba, sai ya amsa da cewar “Ameen jann……….mugun fad’uwar gaba naji asadda ya ce wannan jann d’in, don yallab’ai kad’ai ke kirana dashi kuma zanfi son ace shikad’ai zai dawwama yana ambatarsa, uffam ban sake cewa ba har muka iso gida a waje ya tsaya don daga nan gida zai wuce har na aza hannuna zan fita naji kamar daga sama ya rik’e gudan, arikice na juyo ina duban sa idanun sa sun lumshe sosai ya kwanta cikin sit d’in, muryata har rawa take nace “yah usy…………..Jannah”

Ya katseni da maganar da zan abu ya dauko abayan motar ya mik’o mun, “ba cinye hannun zan ba kike zare mun ido”

Bansan nai murmushi ba na anshi abunda yake mik’omun nace, “idan mutum yai birthday shi akeba kyauta ba shine yake bayarwa ba”

Murmushin ya sake saki yace, “bansan meke cikin kanki ba har yasa kika mance da ranar haihuwarki, Happy birthday beautiful! I hope you have a wonderful day filled with joy and happiness. Allah ya karo shekaru masu albarka”

Idona kamar zai fad’i saboda kallon sa danake surprise d’in yai mugun dukana, no wander a wajen taron mutane keta ban kyauta, na dauka duk nashine tunda shima ai yau d’in ranar zagayowar haihuwarsa ce, daker na iya cewa “yah usy wannan surprise haka? Wallahi na manta, thank you so much i really appreciate it ban San yazan na gode maka ba”

Yadda fuskarsa ta nuna kadai na gane yaji dadin kalamaina, gift din da ya bani nake jujjuyawa murmushi bai bar fuskata ba nace, “bansan me zan baka ba matsayin gift dinka kaima, abun yazo mun gagafa yah usy………bana son komi daga gareki jannah, abu guda nake so shine yardarki ki amunta dani I WANT TO BE UR BEST FRIEND, ina son na zama abokin shawararki kusancinki nake buk’ata daga haka bana son komi daga gareki, dare nayi kije zamu sake magana zuwa gobe by take care”

Rausayar dakaina kawai nayi na shige gidan shi kuma yaja motar ya tafi.

YAH USY SHINE MUTUMIN DAYA SONI YA KAUNA CENI ALOKACIN DA RAYUWATA TA SHIGA CIKIN GARARI,ALOKACIN DA NA RASA YARDAR KOWA NA RASA KAUNAR KOWA. MATSAYINSA A WAJENA BAZAI KWATAN TU BA…….KASHHHH KARNA KARAR MAKU DA LABARINA TUN ANAN KUCI GANA DA BIN MOM MUHSEEN ????

Mom muhseen✍????
[8/16, 5:13 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......19

Koda na dawo daki cire kayan jikina nayi saboda daman kagare nake na cire akwai nauyi, wanka nayo nazo na shirya cikin kayan bacci na riga da dogon wando, inayi ina tunanin abunda ya faru yau saidai inyi murmushi kawai, duk yadda baso zuwa ba na samu kaina cikin jin dsd’i, amman dana tuna gobe zan koma gidan momy sai inji gaba daya hankalina ya tashi addua kurin nakeyi, inda so samune ace naje naga su innamu kafin na koma gidan momyn, tunda ba lallai ta barni ba idan na koma din.

Zama nayi najingina da gado na tankwashe kafafuna gift din yah usy na dauko na ke bud’ewa ba abunda ke tashi sai kamshin turarensa ke tashi, shima ba daga nan ba indai wajen bulbula turarene amman har yanzu banji irin na yallab’ai ba.

Bansan sadda bakina yace, “wow this is so beautiful bungles, yan hannu ne manya masu kauri guda biyu kalar golden, sai agogo mai dan karen kyau itama golden color, fuskata dauke da murmushin jin dad’i yah usy yana matukar hidimta mun, baya gajiya da siya mun abu.
Saida na gama gwadawa sannan na maidasu cikin dan akwatinsu na maida cikin jakkata da nagama had’ata don tafiya gobe, na dawo na kwanta yar wayata na lalubo in duba time idona ya sauka akan missed call da wata no mai + a mugun zabure na tashi zaune, jikina har rawa yake tabbas duk duniya babu mai kirana saishi tunda ya bani wayar shi kadai yakirani kuma tunda ya tafi ba wanda ya sake kirana, yau kuma da naga kira ya tabbatar mun da cewar yallab’ai ya kirani yadda jikina ke tsuma har mamaki nake, tabbas inada kud’i sosai akan layin hannuna na rawa na soma bin number da aka kira da ita, kiran shiga yake amman ba a dauka ba runtse idona nai na sake jarabawa amman har ta gama rurinta ba’a dauka ba, raina yaimin babu dad’i ainun saboda na saka ran jinsa sosai, kira uku nai ba’a dauka ba sai na hak’ura kawai.

Bazan iya cewa ga iya lokacin dana dauka kafin bacci yazo mun ba, nasan dai na dad’e sosai karshe ban saan sadda nayi baccin ba.


      *ASAAD*

Tun daga ranar daya sauka spain baida lokacin kanshi, kasancewar dogon hutun dayazo yayi agida yasanya yana isowa ba’a bashi wata damar zama ba balle tunaninta ya gallabesa, training suke ba kama hannun yaro ba zama in dare yayi yazo ya kwanta gajiya ce take masa yawa daya fara tunaninta baisanin bacci ya sace shi, bai samu kanshi ba saida suka gabatar da wasan da yan wata k’asa cikin ikon Allah kuma sune sukai nasara, alokacin sunan sa ya k’ara yin shura ba a Nigeria ba ba acan spain d’in ba saboda kwazonsa da hazak’arsa, ga tarin kud’i da yake samu kamar hauka a lokacin da suka buga wasan Abba har can yaje kuma ya kalli wasan d’an nashi yana sakeyin alfahari dashi, saida ya kwana uku sannan ya bar kasar bai sanar da kowa cewar yazo ba sai usy, a sadda ya samu kanshi yake lokacin hutawa sai tunanin ta ya zame masa tamkar abokin rayuwarsa, duk inda zashi duk inda zai shiga itace mak’ale acikin zuciyarsa daidai da rana guda bai tab’a jin zai kirata ba, saboda a wannan lokacin baya da wani buri daya wuce ace jann ta samu ingantaccen ilimi wanda zata tsaya da kafafunta, watan watarana zata dauki nauyin dawainiyar iyayenta da ita kanta, tun yanzu idan ya rikita mata zuciya da soyayyarsa ba zata samu damar maida hankali akan karatun ta ba, shiyasa duk irin halin da yakejin sa aciki game da ita yake jurewaa, inhar yaji tana lafiya bakin usman hakan kad’ai yana sama sa natsuwa, kuma duk bayan sati biyu yana kiran principal d’insu yaji ya yana yin kokarinta, yadda yake samun good information daga garesa ba kadan yakejin dadin hakan ba, hakan yasa yaji bazai iya neman ta ba ya rikita mata zuciya don tabbas inhar ya kirata sai taji ajikinta, ya sama ransa cewar ba zaije gida ba akalla sai sunyi weac, ko kadan baya hutawa wajen turama usy kud’in hidimarta baya jiran karshen wata yayi daya samu daya tura mashi, sun dad’e basuyi waya da usman ba shine kwana biyu duk abunda yake faruwa yana sanar dashi wanda zai bashi shawara ya bashi wanda kuma zai dauki mataki ne nan danan zai dauka, kwatsam abakin hindu yaji cewar jannah bata gidan momy ranar da sukai video call yake mata fad’an rashin maida hankali a makaranta, cikin son jin ya Janna take yace mata “ga jann nan tama fiki maida hankali, in baki wasa ba zata baki mamaki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button