JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Saurin kallonta yayi yar dariya ta sanya shi kuma ya dan shafa kanshi yana cewa, “na ganki mana, sannu da kokari”

Ta amsa mashi da cewar, “bakomi yah Asaad aikina ne ai, duk sadda kaga dama ka kawo mun ita zan ringa gyarata”

Harararta yai yana saka hannunsa aljihu ya fiddo wata envelope yana cewa, “ga ladar aikin ki to”

Ja baya tayi tana cewa, “haba dai Yah Asaad, don Allah ka bari ni badan ka biya ni nayi mata ba, ai taren tafi karfin haka”

Sake kallona yai na sadda kai kurin ina wasa da yatsuna, yace “indan baki ansa ba bazanji dadin sake dawo miki da itaba”

Daker ta ansa tana masa godiya sosai sannan tai mun sallama tatafi, shi kadaine babu driver ya zagaya wajen kofar mai zaman banza ya bud’e mun yana kallona, nima kallonsa nai sai na kasa cigaba da kallon nashi na tako ahankali na shiga sannan ya rufe, ya zagaya ya shiga yatada motar muka tafi………………….

Pls aringa hakuri dani da karancin page insha Allah idan na samu dama zan ringa kara yawansa ngd da kaunarku gareni.

Mom muhseen✍????
[7/25, 2:57 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......8

Muna hanya akai sallar isha’i saboda tukin da yake kamar wanda bashida kuzari atattare dashi, nidai tunda na shigo bance uffan ba kamar an rik’e harshena ko gaidashi kasawa nai, munyi nisa da tafiya ne naji yace mun,

“Kin kalli madubi kuwa?”

Yana kallon hanya yai mun maganar, kaina k’asa nace cikin sanyin murya “ehy na kallah”

“Mekika gani to”

Dan kallonsa nai a sace na maida kaina kasa nai shiru bance komi ba, shima din kamar bazai magana ba sai kuma yace,

“Kema kinga yadda kika canza ko?”

Can kasan mak’oshi na ansa da “uhm”

Daga haka bamu sake magana ba har muka iso gidan nashi, muna fitowa iska ya taso ashe hadarine kwance garin, cikin sauri ya dauko ledojin dake baya ganin sun masa yawa yasa na anshi guda, ya bude gidan muka shiga.

Zubewa yai cikin kujera ya aje ledojin k’asa yana d’age kanshi sama, nima gefe naja na zauna injin yadda gabana yake fad’uwa, a duk sadda muka kasance nida shi agidan daga jiya zuwa yau sai inji gabana yana mugun fad’uwa, tsoro yana kamani na takure waje guda inajin yadda ruwa yake sauka kamar zai keta rufin ya shigo, jinai kamar zan fashe da kuka dama can tsoron ruwa gareni, in ana ruwa zainab nake kwakumewa har agama.

Fuskata na sanya cikin kafafuna ina shashshekar kuka ahankali, saboda ruwa ake inajin harda kankara, ko jiyai ina kukan yai saurin tasowa,

“Jannah, jannah kuka kike? Me akai miki? Akwai abunda nayi maki ne?”

Girgiza kai kurin nayi saboda ban san me zance masa ba, ayadda naji muryarsa duk a kid’ime yake,

“Don Allah kigaya mun, baki son gidan nan ko? Bakijin dadin zaman nan ko? Kiyi mun magana don Allah”

Cikin shashshekar kukan murya na rawa nace, “Ruwa nake jin tsoro”

Bai san sadda yaja gefe ya dafe kaiba, murmushi yana kubce masa ya dau lokaci yana murmushin kafin yace, “please Jannah stop crying, ruwan nan fa bazai miki komi ba,”

“Idan akayi tsawa har suma inayi, don Allah ka kaini inda bazanji karar sosai ba”

Dariyarsa yake dannewa yace, “ok saikin daina kukan sannan”

Shiru nai inajan majina da ajiyar zuciya, hakan baisa na daina jin tsoron ba mik’ewa yai yace “biyoni”

Haka na bisa kamar jela har zuwa dakin danai baccin rana, bude mun yai na shiga ya shigo yana rufe tagogin na sliders, ya Saki labulen da yake manya ne labulayen dakin, sannan ya kunna na’urar dumama daki ya jiyo yana kallona, har sannan fuskarsa da murmushi yace “kinajin karar sosai har yanxu”

Girgiza kai nayi yace, “kiyi salla bari na kawo miki abinci”

Yaja kofar ya fita wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, agidan mu na saba kwano ne ko silin babu idan ana zuba wannan ruwan jinake har cikin yan cikina, akwai ranar da akai wata tsawa agarin mu har gidaje suka fad’i da bishiyoyi, tun ina shekara goma lokacin, a sannan har suma nayi daga lokacin Allah ya sanya mun matsanancin tsoron ruwan sama, saboda in anayinsa da wuya ba’ai tsawa ba.

Yadda naji bana jin karar ruwan sosai yasa na sauke ajiyar zuciya, na rab’e baki gadon ina haka sai gashi ya dawo, tire ne dauke ga hannun sa saurin tashi nayi na ansa cikin sanyi nayi masa sannu,

Ya amsa mun da “yawwa, kinyi sallar kuwa?”

“Zanyi in nagama ci”

Saboda yunwa nakeji sosai alokacin, kamar bazai tafi ba yai tsaye jikin k’ofa ni kuma ina tsakurar soyayyen dankalin turawa da aka soyasa tare da kwai, ga yar miya mai dadi a saka asaka, sai nama balago sai kamshi yake sai lemu da ruwa kasa sakewa nai ganin bai tafi ba, zuwa can yace mun a sanyaye “daga gobe ba lallai mu sake had’uwa time to time ba”

Ahankali nake kallonsa na had’iye abunda nakeci nace, “zakayi tafiya ne?”

Lumshe mun idonsa yai sannan ya bud’e yana cemun, “Daman ba mazauni bane ke kika zaunar dani”

Sake kallonsa nai cikin mamaki zanyi magana ya rigani, “I mean hidimar ciwon baba da kuma daukarki zuwa gida Yasa ban koma da wuri ba”

Rausayar da kai nayi bance komi ba duk da inada tambayoyin da nake son nayi masa, na kasa ne idan na kallesa yana mun kwarjini sosai sai inji na kasa fadar abunda ke bakina,

“Talk to me”

A d’an karatun da nayi inadan jin wasu words din na turanci, cikin rashin fahimta nace “me zance?”

Kallona yake tayi sannan ya cigaba da magana, “kina son tambayata na gani a idonki”

Ai saiya sake sani zaro idanun nawa har naso kwarewa, nasha ruwa sannan na ji sauk’in d’an guntun tarin danai,

“Im sorry nasa kin kware”

Jinjina kaina nayi kurin sannan yace, “zanje inyi salla naci abinci, in kin gama zan sake dawowa”

Ya fice ba tare dana oya fad’ar koda A ba, wannan mutum shu’umi ne na jima ina nazarin maganganunsa haka dai naci na koshi na tashi na shiga toilet don yin alwalla, nazo na fara sallar magriba nai isha’i na had’a sa shafa’i da wutir, na daga hannuna ina rok’on ubangijina neman sa’a da dacewa, da neman kariya daga dukkan masu sheri, don sosai nake cikin zullimin zuwana cikin mutanen da ban tab’a ganin su ba, ina shafa adduar naji yai knocking tashi nai na bud’e masa duk da abud’en take,da alama kayan bacci ne jikinsa don naga masu taushi ne rigar hannunta dogo wandon har wuce guiwa yake, yai kyau sosai duk abunda yasa yana masa kyau ainun,hanya na bashi duk da inajin gabana yana fad’uwa ba abunda ke tada mun hankali irin mu kadaice nidashi agidan nan, bakin madubi yai tsaye yana rubugume hannun sa bayan ya ajiye wata leda mai kaya aciki,

Gefen gadon na koma na zauna ina jin yadda zuciyata take bugawa da karfi, duk munyi shiru kamar ba zamuyi magana ba, jinjina kai yayi yana dan murmushi mamakinta kurin yake yadda kusan halinsu guda.

“Injinki fa”

Na kallesa ahankali ina sassauta muryata, “nifa ba abunda zance maka”

“Aa ni nagani cikin idonki dazun”

Girgiza kai nake kamar kadangaruwa, “Aa ba haka bane”

Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauki ledar yazo ya ajeta gabana duk fuskarsa ta canza, sannan ya juya mun baya yana magana a sanyaye cikin yana yinsa,

“Na dauka akwai tambayar da kike son kiyi mun shiyasa na dawo, saboda daga yau zuwa gobe ba lallai ki sake ganina a kusa ba, ga kaya nan kiyi amfani dasu goben ki tashi da wuri 9:30 zamu fita”

yana gama fad’ar haka ya bud’e k’ofar yasa zai fice………….”kaji”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button