JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Wasa wasa yallab’ai hidima yake mana har yanzu, kullin sai yazo ganin baba kuma da abunda zai kawo mana, sannan ya tambaya idan akwai bukatar kudi ko ance babu bai hana ya ciro ya mik’a ma yayanmu, baba kanshi har kuka yai saboda duk duniya bai tab’a samun wanda ya taimakesa kasa da irin taimakon da yallab’ai Asaad yake mana ba, kuma koda yaji cewar zan koma gidansu na ringa masu aiki bai hana ba yabada goyon bayansa sosai, ya kuma yi mani nasiha mai shiga jiki, satin baba biyu aka sallameshi muka dawo gida, yayanmu yatai gezawa ya dauko duk abunda muke buk’ata don wanda yasai gidan har ya fara korafi,ranar da yayanmu yaje ranar yasa aka rushe gidanmu na gezawa,
Babu abunda zamu cema Allah subahanahu wata’ala sai godiya domin shine yayi mana komi,gashi baba ya samu lafiya sai dan abunda ba’a rasa ba, bayan sati da dawowar baba gida yallab’ai yai ma yayanmu ciku ciku da takardunsa na secondary ya Jana jarabawar jamb kuma cikin ikon Allah ya dan samu makin da ake so, sannan ya fara nema masa admission a wata makaranta dake nan cikin kano BUK, bai gaya ma innamu cewar ga ranar da zaizo ya daukan ba saidai muka ji abun kwatsam kamar saukar aradu.

Inata wanke wanke wurin karfe biyar na yamma lokacin wata doguwar rigace jikina ta atamfa duk da ta dan sha jiki bai hana tayi mun kyau ba, kallabin rigar dana daura bai hana dogon gashina fitowa ba jelarsa guda hud’u tana reto ga bayana, fuskata fresh take daman ni bana kwalliya daga vesilline bana saka mata komi ko powder bana sakawa, amman a haka mutane ke ganin kyauna yayi yawa kamar aljana,sannan a shekaru dukkan wata gab’a ta jikina ta gama bud’ewa, girma ya bayyana sosai tattare dani, inada k’ugu wanda ya fidda shape mai kyau, basuyi yawan nan ba haka dai sunyi d’as dasu, shiyasa bana son siket don shine idan na saka yake fidda surar jikina, inada kirji sosai amman ba irin wannan girman garesu ba daidai na budurwa dai, kuma jikina ko ina farine kadanne baza’a kirani zabaya ba, don duk gidan nafisu haske haka idanuna bakake ne sosai farin kwayar idon ma kamar ruwan kindirmo, inada kyawawan idanu nima na san hakan, ga girar ido idan na dan sauke idona kasa zaka dauka bacci nake saboda yadda suke kwanciya, dumpul dina guda a side din Dama, lotsawar har tai yawa ko abinci nake ci yana nan ko kuka ko ma minake saiya fito, karma ace dariya ko murmushi.
Haka zainab take saidai nakan fita wasu abubuwan kadan, gaskiya duk wanda zai ganmu kyanmu ne farko da yake daukar hankalin mutum,shiyasa muke samun matan dake tsanarmu,
Zainab ce take kwashe shara baba da innamu suna cikin falo suna kallo, ina sharar wajen lokacin na gama wanke wanke mukaji sallama, dakatawa nai da sharce ruwan saboda yadda naji muguwar fad’uwar gaba, duk sadda zo gidan nan ko inji muryarsa gabana mugun faduwa yake,
Duk na diririce nace ma zainab,

“Kije kiduba”

“Yaya murja yallab’ai Asaad ne”

Kauda kai nai ina cigaba da sharar nace , “ki shigo dashi ki sanar da innamu zuwan sa”

Karfin hali na sanya na dago ina gaidashi, kamar ko yaushe cikin sanyinsa da natsuwa ya amsa mun, amman yau da ido ya amsa d’an lumshe su yai ya bud’e sannan ya isa cikin falon da su innamu suke,

“Sannu da zuwa yallab’ai maraba lale bismillah ka zauna”

Cikin girmamawa yake gaidasu ita da baba ina daga waje na kasa shigowa, nadai lab’e bakin kofa daga waje baba ne yace masa,

“Sannu da kokari yaro kaji, Allah ubangiji yai maka albarka”

Baba ya fad’a lokacin da zainab ke ajiye wasu manyan ledoji guda biyu, da yake sadda take masa iso yace ta je mota wajen driver ta anso kaya, suna ta ajiye a gefensa.

Innamu da kanta ta kawo masa ruwa pure water saidai babu sanyi saboda babu frig, cikin natsuwarsa yace “sannu mama”

“Yawwa yallab’ai”

Baisha ruwan ba, inda sabo mun saba da halinsa bai tab’a shan wani abu ba tunda yake zuwa, dakin yai shiru kamar ba abunda ya kawosa saida ya gama isar tashi sannan yace,

“mama nazo tafiya da JANNAH ne yanzu”

Wani dammm naji a zuciyata har saida na rufe manyan idanuna, kafin kuma in fara tunanin wane irin suna ne wannan ya kira? Allah yasa bani bace tunda ba sunana naji ya ambato ba, ban gama tunanin ba naji mama tace masa,

“Yallab’ai murja dai ko?”

Duk da ban ga fuskar sa alokacin ba nasan murmushi yayi sannan naji yace, “ehy ita d’in nake nufi, na takaita sunan ne saboda yana mun tsawo”

Kwalalo ido nai jin abunda yace, watau sunana ne yake masa tsawo kenan shiyasa zai b’ata mun suna, na turo baki kamar suna gani na kafin inji baba yace,

“Hakan ma babu laifi, murjanatu! Kina ina zo yaki”

Jinai kamar zan zura aguje amman na daure na fara sand’o kamar zan kama fara na shiga da siririyar sallama, bina yai tayi da kallo har na isa inda baba yake na durk’usa cikin ladabi, kamar dai yadda muka saba idan innamu ko baba wani yai kiranmu, kaina a k’asa inata alwallar k’udaa sannan naji mama tace mun,

“Yallab’ai ne yazo zai tafi dake yanzu”

Dagowa nai ina sauke idona akanshi kamar yadda na samu kwayar idonsa mai lumshewa akaina, saurin maida kaina k’asa nayi ina cewa cikin tattausan lafazi,

“Innamu ashirye nake da tafiyar”

Duk sunji dadin maganarta baba yace, “yaro ga amanar y’ata murjanatu nan na damk’a ahannunka, don Allah ka kula mana da ita kuma zuwa wane lokaci zata ringa ziyartar mu”

Calmly yace, “insha Allah baba zata ringa ziyartar ku, zan fidda lokaci da kaina zan ringa kawo maku ita”

Sukai hamdala sannan mama tace, “jeki had’a kayanki…………no need mama ita dayanta zamu tafi akwai komi acan da zatai amfani dasu”

“To Masha Allahu, Allah ya Kara girma da daukaka, Allah ya tsare ke kuma ki rik’e amana don Allah murjanatu, banda daukar abunda ba abaki ba, duk da nasan halinki amman dan adam na canza wa akodayaushe, don haka ki iya talaucin ki kikuma rik’e mutuncin kanki da namu”

Sosai innamu ta kara mun nasiha sannan ba shiga na dauko hijabina inajin wani dunkulellen abu ya tsaya mun ga mak’oshi, na san kuka ne na kewar su innamu banda damar yin sa ayanzu don zan tayar masu da hankali, Brown din hijab na sanyo ina kokarin danne abunda nakeji, muka fito bayan naima baba sallama innamu da zainab har kofar gida suka raka mu, yayanmu baya nan amman nabar sallahu ace masa na tafi kuma zanyi kewarsa, idona cike da kwallah muka bar kofar gidanmu…………………..

Mom muhseen✍????
[7/21, 10:37 AM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......6

Kukana kamar jira yake mubar cikin unguwar ya fito fili na saka fuskar cikin tafukan hannayena ina rera kukan sosai sautinsa na fita ahankali ina jan shashsheka, atare dashi duk abaya muke zaune driver ne yake jan motar, na kasa danne abunda nakeji jinake kamar ina tunkarar wani gagarumin abune, ya zanyi bazan kuma yima innamu musuba baba ma bazai lamunta ba,sosai nake kukan don shine zai fitar mun da mikin dake cikin raina…………….”tsayar da motar nan mannir”

Nan take naji yaja uban burki daya sanya na zabura na d’ago ba tare da niyya ba, fuska duk ta lalace da hawaye nake kallon sa ko sau d’aya bai dubeni ba can cikin sanyin murya yace,

“Kina iya fita ki koma gidanku”

Tsitt nayi saboda maganar tashi ta dokan,duk da hakan shine abunda nake so amman kuma bazan iya aikata hakan ba, me zanje nace masu? Saurin goge fuskata nayi ina girgiza kai cikin raunin murya nace masa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button