JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta turo baki cikin shagwab’a “yaya ita ba karatu suke da yaya usman ba, ni kuma ba yayi dani ko”

“Zan mishi fad’a kema ya ringayi dake, ina jann d’in take tana kokari islamiyya kuwa?”

“Sosai ma Yaya kasan yanzu mun zama abokai, tare ma muke karatu idan akai mana k’ari, kwana biyin nan ne da bata nan bamuyi ba”

Yamutsa fuska yayi yace “ina taje? Ko gidansu taje usman bai gaya mun ba”

Ta bashi labarin d’an abunda ya faru da tafiyar su usman da jannah,
“Amman ban san inda ya kaita ba, muna dai had’uwa islamiyya haka a school ma muna had’uwa”

Sallama sukai da ita ya kira Abba sukai magana yake cewa zai dauki mataki sosai karya damu, zaima usman magana ya dawo da ita yayi haka ne don ta samu hutu.

Daga ranar bai samu lokacin magana da usman ba suka fara shirin buga wani wasan a kasan england, saboda muhimmancin wasa yasanya duk wayoyin sa a kashe suke duk kiran da usman yake masa baya samun sa, Asaad bai samu kanshi ba saida suka buga wasan daker suka sha sannan ne ya dawo hayyacinsa, ranar kamar an tuna masa da wani abu mai muhimmanci yai saurin duba kwanan wata, a zabure ya dauki wayarda time d’in yana bakin ruwa shida abokinsa ya kira usman.

“Bro’s kayi wuyar samu 2days”

“Baka kalli wasan mu ba da yan real Madrid a england mukayi sa ban samu lokaci ba wlh”

“Ayya bros wallahi na shafa’a kuma Abba bai sanar dani ba, fatan kun lashe su nasan inhar akwai Bros ba zasu kai labari ba”

Murmushi yayi yana ce masa, “ehy mana amman ai daker mukasha, yanzu dai ba wannan ba ya kake ina ajiyata?”

Yar dariya usman yayi ta yak’e yana shafa kanshi yace, “tana nan lafiya bros”

“Meyasa baka gaya mun abunda ya faru agida ba usman? Ban gaya maka duk abunda ya taso wanda yafi karfin ka ka sanar dani ba”

Ransa a dagule yace, “yah abun nasu ne fa yayi yawa bazan iya jurewa b……….runtse idonsa yayi jin yana shirin tafko katob’ara,

“Menene ba zaka iya jurewar ba?”

Ya yanko masa tambayar cikin sauri yace, “abunda su momy keyi ba zanso ace ina gani suna cutar da janna ba bacin kace nayi bakin kokarina”

Lumshe idonsa yayi yana jin wani irin feeling kamar yai tsuntsuwa yaje yaga jann d’insa, cikin serious talk yake masa magana, “ina ka kaita yanzu?”

Usman cikin yana yi marar dad’i ya amsa da cewa, “tana gidan yah hisham”

“That’s good, abunda zan gaya maka shine daga yau koma miye ya taso sanar dani kafin ka yanke hukunci, munyi magana da Abba komi zai kafa ka maidata gida insha Allah zan samu time ko yaya ne inshigo, na yaba da kokarinka sosai kuma ina bayanka akan ko sau d’aya karka barta tayi kuka, gobe shine ranar birthday d’inta kaima kuma goben ne naka, inaso ka shirya mata birthday zanso inaga tayi farinciki idan na dawo zanga pictures d’in, akwai kud’i dazan turo maka kayi amfani dasu please”

Ajiyar zuciya usman yayi yace “to yah insha Allahu za’ai duk abunda kace, yaushe zaka zo d’in?'”

Yana shafa kanshi cikin yar damuwa, “I don’t know usy,amman dai zan zo insha Allahu”

“Ka kula mana da kanka we miss u so much, har jann ma tana kewarka jiya dai da takai bango har tambayata tayi”

Wani kayataccen murmushi ya sauke yana lumshe idonsa yana jin wani irin yana yi, yace “I’m Eiger to see her face, me kace mata to?”

Runtse ido usy yayi yace “shashantar da maganar nayi kurin, Allah ta damu please kadawo”

Wannan karon dariya yayi yace “dole ne ma, duk da ba haka naso ba inzo a time din da basu gama makaranta ba, amman bazan iya dakatar da zuciyata ba sai nazo usy”

Da haka sukai sallama yana kwanciya cikin yashin da bakin ruwan, abokin nashi yace “be a man mana Asaad”

Idonsa a rufe yake maganar, “inda ace kaga fuskar yarinyar koda sau d’ayane ba zaka ga laifina idan na shiga wani yanayi ba, ahakan ma ni nasan ina jarumta”

Dariya yai masa yace “miye amfanin wahalar da kanka da kake kuyi aure mana……….”Aa shareef wannan burin bana yanzu bane, inason na cika mata nata burin kafin nawa ya cika yar marasa karfi ce hasali ma wanzu wata garesu shine ya kawo sauyi kadan tattare dasu, na daukota daga gidansu zuwa namu saboda ina son na inganta rayuwarta fiye da tunanin ta, tabbas ranar farko na kamu amman na b’oye har sai naga ta cimma manufa a rayuwarta, don haka dole na zama namiji wajen jure feelings dina don samun cikar burinta”

Jinjina kai shareef yayi yana cewa, “Allah ya cika maku burinku, yadda kake fadar kyaunta akwai risk Allah dai ya kareta daga sharrin makiya”

Ranar birthday din wurin eight na dare dukai waya da usy yace masa gashi nan zaije ya dauketa, cikin damuwa yace “please usman karfe goma ka maidota gida, bana son dad’ewar nan kanaji na”

“To yah insha Allah da wuri zan dawo da ita gida”

A Daren bai bacci ba time to time ya na duba agogo, duk da akwai banbancin awanni tsakanin Nigeria da nan kasar na kusan 2 hours, sadda ya kira usy yaji sun dawo acan kasar karfe shabiyu,su kuma can goma na dare ne yaima usy kira yakai biyar bai dauki wayar ba,hankalinsa yai mugun tashi har yaji bazai iya hakuri ba ya soma kiran jannah itama bata dauka ba, hakan ya tabbatar masa basu dawo ba hankalinsa ya kasu kashi babu adad’i, wannan daren bai runtsa ba acikin daren kawai ya shirya jikkarsa ya tura sakon daukar permission asubar fari sai airport shareef ma bai sani ba.

Ayi hkr ba yawa????????

Mom muhsen✍????
[8/18, 2:17 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......20

Usman tun kafin su tafi party wayarsa take silent bai bita kanta ba har aka kammala partyn ya dawo da jannah, gabaki d’aya yana cikin wani shauki kasancewarsu daren ranar jinsa yake daban, sannan kasan zuciyarsa yanajin tamkar yana yin abunda ba daidai ba amman kuma bai iya hana zuciyar tasa abunda take umurtarsa da yayin, wanka yayi yaci dan wani abu saboda yunwa ya kunna computer yayi abunda zaiyyi ya kashe yaje ya kwanta, ko kadan ransa bai bashi wayarsa silent take ba kuma bai dubata ba balle yaga tarin missed call din yayansa, ya dad’e bai bacci ba saboda tunanin sallamarsa jannah abun har kasan ransa yakejin sa, duk tarin yan matansa baijin wannan abun akansu anya yayima kanshi adalci kuwa???

Da wannan tunanikan barawo ya sace sa.


Makara nayi sosai don ban tashi ba sai wurin karfe shidda da kwata, a firgice na diro na ruga toilet nai wanka had’e da alwallah sannan na fito na tada sallar, har nakan kance rabon dana makara sallar asuba gaskiya bazan iya tunawa ba, amman jiyan nan saboda rashin kwanciya da wuri dole gashi na makaran,lumshe idona nai nai jimmm zuwa can na bud’e su ina rarumo wayata na soma bincikar koya kira da daddare ban dauka ina bacci, amman babu alamun ma anyi kiran jikina yai sanyi sosai, banyi k’asa aguiwa ba na sake kiran wannan karon sai akace ma akashe take jinai kamar marar lafiya gaba d’aya gana cikin yana yin jin dad’i, ban fita ba duk da inajin motsin Ramma Anty sai bakwai take dawowa shirin makaranta na farayi don gaf ake da fara exams d’in third term, na mance ban sanar daku position dina ba na first term DA second, na first term nayo na goma ni banma zaci zanyi kokari haka ba duk daukana zan je gidan karshe ne, second term kuma nayo na biyar wannan karon na zage sosai ina burin ace ko banyo na daya ba to karna wuce na biyu, saida na gama shiryawa sannan na wuce dakin su shareefa na iske har an musu wanka, idasa shiryasu nayi ramma ta wuce don kammala breakfast don yayan shima fitar wuri yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button