JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Yayanmu bai dawo ba sai wajen goma da rabi yana sharce gumi, yace “gwaje gwaje mukaje akai mashi, anci rabin kudin nan fa innamu gashi yanzu an shiga dashi wani daki an bani wannan takaddar zanje in nemo duk abunda suka rubuta”

“Babu komi sale kaje asai duk abunda ake buk’ata muga abunda Allah zaiyyi”

Haka ya juya yana tambaya ka nuna masa pharmacy,ya sai komida ake buk’ata sannan yaje yakai ya koma gefe yana jiran tsammani.

   *bayan awa uku*

Likitan ne ya kira yayanmu suka wuce office d’insa bamu san me suka tattauna ba abunda muka gani kawai shine yayanmu ya fito yana kuka, tunda nake ban tab’a ganin kukansa ba jarumin mutum ne mai dakiyar zuciya, tun daga haka naji zuciyata ta buga naji jikina yana sacewa inajin kamar xan fad’i, saurin tarosa innamu da zainab sukai silalewa k’asa yai yana zaman dirshen yana cewa,

“Shikenan innamu zamu rasa baba! Domin baba yana cikin hadari”

A rikice innamu take dukta fita hayyacinta tace, “kai sale ka natsu ka gaya mana abunda yake samun malam, don Allah natsu karka saka in zare”

Ya kamo hannun innamu yana kuka sosai yace, “innamu likita yace ciwon daji ya samu baba, kuma yai masa mugun kamo wanda idan ba’ai gaggawar yimasa aiki ta hanyar yanke kafarsa ba ba tantama zamu rasashi, innamu kudin aikin kadai daya gaya mun yasa na sadakar baba mutuwa zai, innamu wai…….wai……mil…..miliyan biyu zamu kawo, innamu ina zamu sameta? Bamu tab’a ganin ko dubu dari ba sai yau da muka bada jinginar gidanmu, ta ina zamu nemo miliyan har biyu”

Innalillahi wa inna ilahir raju’un Allahumma ajirni fi musibati wa’aklif li khairan minha!!!

Abunda na keta fad’a ina nanatawa kenan yayinda na silale k’asa dab’as ko ciwo banji ba, hawaye ne suka k’afe mun miyan bakina ya dauke, kukan innamu da zainab kurin kakeji yana tashi yayin da halin da nake ciki bai misaltuwa.

Bamu san iyakar lokacin da muka kwashe anan ba saida mukaji ana korar mu wai ba’a zama anan, farfajiya muka fito mukai cirko cirko cikin shakakkar murya innamu tace,

“Yanzu a wane hali yake ciki?”

Jikinsa ya mugun saki yace, “yana dakin gaggawa ana bashi treatment, yace zasu kula dashi na kwana uku idan bamu kawo kudi ba zasu koremu tare dashi”

Na sharce hayawane nace, “innamu miye amfanin gonakin ku keda baba, asaida mana muga idan zasukai yawan da ake buk’ata”

Girgiza kai tayi tace, “tunanin da bake yanzu kenan, duk da nasan ba zasukai ba ko rabi basuyi amman kila idan sukaga mun kawo wadannan din zasu tausaya mana su ansa”

“Yanzu ya zamuyi ina zamu kwanta, idan asuba tai zan sabko inje inga yadda za’ai d’in”

Innamu tace, “ga wasu bayin Allah can nasan suma jinya suke, zamu tambayesu ko zamu rab’a gefensu, saidai kai bansan ina zaka kwanta ba”

“Aa innamu naga masallaci waje zanje na kwana acan, kuyi amfani da tabarmar hannunku kuyi maleji zannuwan da kuka dauko saiku rufa dasu akwai sanyin sosai”

Hakan ce ta kasance kuwa basu hana mu ba muka shimfida yar madaidaiciyar tabarmar muka rufa da zannuwan, zuwa can saiga yayanmu ya dawo yace,

“Naga ba wanda yaci wani abu cikinku shiyasa naje na siyo mana abu da yan canjin da suka rage”

Nace”yayanmu kaida zaka koma gezawa gobe? Kana bukatar kudi”

Murmushin karfin hali yayi mani yace, “zasu isa kanwata”

Duk da bamuda natsuwa haka mukaci muka sha ruwa sai bacci ya sacemu, don akwai gajiya da rashin isassar natsuwa muka dunkule waje guda daka gan mu dole mu baka tausayi.


Ana gama asuba yaya ya tafi gezawa mu kuma muka tafi ganin jikin baba, Allah yaso anbarmu mun shiga saida bamu dad’e ba akace mu fito, tabbas ana bashi kulawa ina kyautata zaton inhar akai aikin zai warke da iznin ubangiji, don babu cutar da bata da magani.
Ba wanda bai kuka ba ganin baba kwance an saka mashi abun shakar iska,kafar kuwa an zaizayeta duk ta koma wata iri alamun jiya an tsotse ruwan an fitar an masa gyara saboda ya samu sauki,ga drip nan an mak’ala mashi bacci yake sosai.

Fitowa mukai muka samu wajen hantsi muka zauna, da yake yayanmu ya bamu kud’in kalaci mutanen da muka kwana kusadasu naga yarinyar zata fita waje nace, “innamu bari na bita na siyo mana koda kunu da kosai ne”

“To ki kula dai”

“Kuma babanku ne baida lafiya ko?”

Inji yarinyar da bata wuce sa’ar zainab ba, murmushi nai mata nace”Ehy, kefa”

Sai naga zatai kuka tace, “muma babanmu ne muka kawo,ya samu lalurar shanyewar barin jiki saka makon faduwa dayai”

Cikin jimami nace, “Ayya Allah yabashi lafiya kibar kuka,duk zasu samu sauki kinjiko”

Ta d’aga kanta kurin mukaje muka siyo muka dawo, akan hanya ne take cemun.

“Kinsan me baiwar Allah, yayarmuce duk ta jawo wannan abun, saurayinta ta bari yai mata ciki taita b’oyewa ba asani ba daga karshe aka gane yanzu haka wannan watan take haihuwa, abunda ya jefa baba cikin wannan halin kenan……………

Mom muhseen✍????
[7/18, 9:26 AM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

   ????️..........3

Idona a warwaje nake kallon yarinyar mamaki ya cikani nace, “a wani gari kuke?”

“Muna bunkure”

Na jinjina kai nace, “Allah ya kyauta ya shiryata da masu halinta, kuyi mata addua ba hantara ba kinjiko, Allah yaba babanku lafiya”

Ta wuce wajen su nima na yanke na nufi wajen su innamu, zainab na hango tataho daga bayi kafin ta iso nake ba Innamu labari tace,

“Haka rayuwa take murja kaddara babu inda bata kai mutum, duk abunda kaga ya samu wani karkayi masa dariya ko ka aibata shi domin baka fi karfin Allah ya jarabeka ba kaima,kiyi mata addua kawai”

Na rausayar dakaina ina cewa to innamu, zainab ta k’araso muka zauna muka ci kosan da kunun naje na maida rubar kunun na dawo muka dasa zaman jiran yayanmu.

Bai iso ba sai da akai sallar azahar duk ya fita hayyacinsa,tausayin sa ya kamani hakika da babu yayanmu da mun shiga uku, innamu kamar tai masa kuka tace “sale ka kuwa karya tunda ka tafi?”

Girgiza kai yake yana cewa, “innamu bata wannan ake ba,kinga kudin nan daker da sid’in goshi suka bani dubu dari shidda da goma sha biyar, innamu ko miliyan fa basuyi ba ya zamuyi? Wallahi nadauka zamu samu miliyan daya kila inda sunkai su tai makemu suyi masa”

Idonsa na taruwa da ruwan hawaye nima na share hawayen nace, “muje mu samesa yayanmu, arashin tayi ake barin arha idan muka rok’esa zaiji tausayin mu,”

Murmushin kunci innamu tayi tana cewa, “murja kenan, ke kinga alamun tausayawa anan tunda muka zo? Banajin zasu anshi kudin nan a haka”

Zainab ta lafe jikin innamu tace, “innamu kibari suje su gwada”

Ta ce, “shikenan kuje Allah ubangiji ya taimake mu ya dora mu kansu”

Cikin sauri sauri haka nida yayanmu muka shiga cikin asibitin kamar zamu kifa, araina addua kurin nake ina rok’on Allah ya kawo mana d’auki, dana tuna yana iya koromu da kudin sai inji zuciyata tatsinke, yanzu ina zamu samu sauran kud’in? Muba wasu dangi ba balle muje ayi mana karo karo, haka muke dai iyakar mu talauci ma baibari mun samu masu huld’a damu ta mutunci ba,kyara da tsana kawai ake nuna mana…………….tunanina ya tsine alokacin da muka k’araso bakin kofar office d’in likitan, saidai kuma agark’ame yake wata nurse tazo ta bud’e ta shiga data fito tana rufewa muke tambayarta,

“Don Allah likita ina wannan likitan yaje ne? Wajen sa muka zo”

Wani k’azamin kallo take mun nida nai mata maganar,sannan ta kauda kai tace atakaice, “baya nan yaje gida cin abinci”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button