JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kalaman Babaah uwani sun ratsani sun taimaka mun wajen jin cewar ashe fa inda Allah,firgici da dimuwa yasa nafara fita hayyacina na mance da Allah subhanahu wata Ala,hawaye wani na korar wani labbana rawa suke tare da muryata nakamo hannunta na rik’e fam ina cewa cikin kuka,

“Bab…..Babaah uwa……uwani ji nake dam……dama in mut…..mutu kawai, na tsani Ray……rayuwata meyasa saini haka zata same……..sameni? Menai ma wani dazai hukuntani da wannan hukunci, Babaata har…..har rokon…….rokonsa nake na ringa hada shi…….hadashi da Allahn daya haliccesa, ina cew……cewa yaji tsoron Allah karya keta…….keta mun haddina………Amman baiji ba Babaata! Yasa…..yasanya karfinsa ya keta mun rig…..rigana”

Kukan ya hana na cigaba da magana har bansan shigowar sa ba,tsaye yayi bakin k’ofa rik’e da leda ga hannunsa, ni kuka Babaah uwani kuka shima yana hawayen jikina kar karwa yake ina cigaba da cewa,

“Baiji……bai….baiji tausayina ba haka ya ring……..yaringa gana mun azab……zaba, ina zan saka Rayuwata da wannan………wannan abun? Amman kince mun Allah yana jina ko babaah ta………..”

Duk mai saurarena saiya fashe da kuka, idan kaga yadda nake karkarwa ina zubar da hawaye kamar famfo duk taurin ranka saika matse, rungumeni tayi tana bubbuga bayana tana lallashina.

“Tabbas Allah yana jinki murjanatu kuma zai saka miki nan bada jimawa ba”

Ita tabani rubutun nashanye sannan muka wuce toilet da ita ruwa mai zafi ta had’a mun, tana tambayata zan iya yin wankan kaina kurin na d’aga mata,tace “to ki gasa jikinki kafin kiyi wankan akwai d’inki jikinki kinjiko kibi sannu”

Wankan nake ina zubar da hawaye na mance ma da bayi nake, ina magana ina rokon Allah ya saka mun, “yah Allah banyi wani abuba,banda laifi ban tab’a kusantar zina ba, kana gani ka saka mun da gaggauwa”

Harna gama ina kuka hawaye sun kasa barin idona,kayan daya siyo tamik’o mun na saka sannan nayi alwalla na fito ta shimfid’a mun abun salla na hau na zauna,don bana iya tsayuwa juwazata iyakayar dani.

Sallar nake ruwan hawaye na zuba ban damu ba, haka na cigaba dayi bansan iyakar lokacin dana d’auka ba ahaka na dad’e cikin sujjada ta ina addua ina kuka ina kai kukana wajen lillahi warasuluhu,nasan kuma yanajina yana saurarena saida naji numfashina zai dauke na sallame, abinci ta tusa mun gaba tana bani tana kara kwantar mun da hankali na, har naci na k’oshi duk da ba wani ci nayi ba haka naji ya isheni, naman dake ciki kadan naci tabani ruwa nasha tace, “Asaad mik’o mana magungunan can tasha”

Jikinsa na rawa ya dauko yazo wajenmu ya durk’usa yana bud’e ledar hannunsa har rawa yake, ban gigin kallon fuskarsa ba saboda kukane zai kubce mun, idan na tuna yadda muka rabu cikin farin ciki aranar ban sanin kuka yazo mun, amman abu guda ne yake gigita tunanina idan na dora idona akanshi yanzu, shine turarensa da yake amfani dashi wanda nake masifar so shine naji ajikin mutumin daya hark’e mun ajiya, amman kuma kunnena bazai mance muryar mutumin ba, alokacin da yake ce mun.

“ki taimaka mun kibarni nayi, in banyi ba mutuwa zanyi”

Nai iyakar nazarina bansan muryar ko waye ba,tabbas muryar yallab’ai ko acikin hauka nake idan najita zan gane, hakan yasa nagane ba shibane to amman waye? Shikadaine wanda nakejin turarensa ajikinsa bantab’a jin wani yayi amfani dashi ba,ajiyar zuciya na sauke sadda yake mik’o mun maganin daya b’allo, sha na ringayi har ya gama ballowar daidai Abba da usman sun shigo kaina k’asa yake kurin bana son kallon ko wane namiji ayanzu don naji na tsani kowane namiji, uffan na kasa cewa Abban wanda yaita jera mun sannu kaina kurin na d’aga, Yah usman yai mun magana yana can rab’e jikin k’ofa muryarsa na kerma yace “Jannah sannu,yajikin naki”

Shima uffan bance masa ba duk mukai tsitt Abban yace bari yaje yaga likitan, kwanciya nai kan cinyar Babaah uwani inajin kamar innamu ce nake kwance bisa cinyarta, likitar sallama ta bada tana cewa na ringa shiga ruwan zafi sau biyu a yini sannan na kula da shan magunguna na,Abba ne yake amsa mata muka taso Babaah uwani ce ke rik’e dani har mota, motar Yah Asaad muka shiga usman sa Abba suka shiga ta Abban tare da drivernsa, mu kuma Yah Asaad d’in ne yaja mu zuwa gida motar shiru kamar mun zama kurame har Allah yasa muka iso gidan lafiya, muna tsayawa wani gigitaccen kuka ya kubce mun saboda dan danan abun ya dawo mun,rikicewa yai shida Babaah uwani hakuri suke ban sunata lallashi, yake cewa “bamu da abun da zamuyi maki ko mu baki daya wuce hakurin nan Jannah,kowa yasan an cuceki don Allah kiyi kibar kukan nan”

Daker na hakuri saida Abba yazo yasaka baki sannan muka taho da Babaah uwani har cikin babban falo, momy Khalid fareeda da Aneesa sai hindu duk suna falon,yadda momy ke nan nan dani yaban mamaki amman na nuna babu komi, zata fara magana kenan Abba yace “not know hafsat,mubarwa gobe kuma”

Yashige ciki yabarmu ciki muma muka shiga ina hawaye nace, “Babaah kije dani dakin ki bazan iya zama acan ba”

“Daman bazan barki ke d’ayaba ai murja,muje dakin nawa”

Inajiyo dariyar fareeda a falon ina mamakin irin tsanar da take mun, bayan ban kashe mata kowa ba ban hana mata komi ba,kwanciya nai kan katifarta ita kuma ta fita don dora sanwar dare.

Abba da Yah Asaad da Hindu ke zaryar zuwa dubani, yah usy kamar yana tsorona daga bakin kofa yake mun sannu sai yajuya Hindu kuwa nan ta tare tana talallashi tana bani hakuri, karshe bacci ya daukeni.

Saida na sake shiga ruwan zafi kafin safiya, da safen ma ta sake had’a mun na shiga nasha magunguna na sai naji na samu sauki sosai da ga rad’ad’in da nakeji.


Gaba d’ayan mu muna falon saboda kiran da Abban yayi muka fito nida Babaah uwani saboda na danji sauk’i, ina iya tafiya da kaina amman a hankali nake takawa har cikin falon, had’a ido mukai da Yah Asaad da ido yai mun sannu na jinjina kai masa kaina kurin,yayin da gabana ke muguwar fad’uwa saida kowa ya gama hallara sannan Abban ya fara yana tambayata cikin wani irin yanayi,

“Jannah zaki iya mana bayanin abunda kika akan abunda ya faru dake”

Jinai kamar ya fama mun inda yake mun ciwo, hawaye suka balle mun cikin kukan na fara gaya masu daga sadda na shigo gida bayan rabuwar mu da Yah Asaad, har zuwa sadda na kwanta kukana ya k’aru sosai momy tace, “kibar wannan kukan na munafurci kicigaba da yimana bayani”

Mamakin maganarta nayi sosai sai ban kulata ba nacigana da cewa, “dakin akwai duhu sosai bazan iya ganin fuskar ko waye ba, sannan ta karfi ya sanya mun bai barni nasamu wata makama ba, abu biyune kawai na rik’e daga mutumin shine kamshin turarensa da kuma maganar dayai mun,ita kuma ban san muryar ba basan kuma kota waye ba”

Na cigaba da share hawayena ina cewa, “alokacin da muke kokowa dashi naji wani k’amshi turare irin na Yah Asaad jikinsa, cikin muryar da bansanta ba yake cewa ki taimaka mun inyi, in banyi ba mutuwa zanyi abunda yace kenan daga nan bazan iya sanin meyafaru ba,nasan dai naita rok’onsa akan ya kyaleni ya rufa mun asiri amman bai sassauta mun ba,abunda zan iya tunawa kenan Abba”

Muryan momy kawai naji tana cewa, “kaji ko Abba? Kaji abunda ta fad’a cewar kamshin turaren Asaad taji, na gaya maka Asaad ne yai wannan abun shiyasa duk yabi ya gigice haka,idan kuma nai masa musu ya furta da bakinsa kafin na bayyana hujjojina”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button