JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

JANNAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kayi hakuri yallab’ai bazan iya rik’e kukan bane shiyasa nakeyi, amman nai alkawarin bazan sake ba ka gafarceni”

Sai lokacin ya d’ago idonsa yana kallona sunyi lumshe sosai kamar mejin bacci yace dani,

“Bazan so takura rayuwarki akan abunda bakya so ba, na dauka har ranki kin amunta ne shiyasa ban sake d’aga maganar ba, and na riga na sanar da momy cewar na samo mai aikin da zataji dadin aiki da ita, yadda take murna yasani jin dadin zuwa tafiya dake amman inhar kina ganin da takura please take this saiki hau taxi ki koma”

Ya idasa yana fidda huci saboda aganin sa yai doguwar magana data basa wahala sosai, duka hannayena na had’e alamun rok’o ina wasu hawayen nace cikin marairaicewa,

“Aa yallab’ai, na tuba kayi hakuri wallahi na amunce ba komi nake ma kuka ba sai rabuwa da su innamu, amman badan bana son zuwa ba don Allah kayi hakuri yallab’ai”

Lumshe idonsa yai sannan yace, “idan har na sake ganin hawaye a fuskarki yana nufin bakya son aiki agidan mu, kuma zan maida ke wajen su baba bana son shiga hakkin wani”

Cikin sauri na sake goge fuskata nace, “na rantse maka da Allah yallab’ai bazan sake kukan ba nai alkawari”

Kauda kai yayi yana murmushi kadan kafin yace, “mannir let’s go”

Ba wanda yasake cewa uffan sanyin motar da kamshin dake tashi kurin nake shak’a, kamshi biyune ya had’e acikin motar gana freshener ta motar ga kuma na yallab’ai wanda zuwa yanzu hancina ya haddace sa, tuni soyayyar turaren ta zauna araina inajin idan na fara samun kudi shine abu na farko da zan siya, garin a lumshe yake kamar za’aai ruwa shiyasa zafi yai yawa, gashi garin kano daman badai zafi ba, shiyasa sanyin motar yake ratsani inajin yar natsuwa araina ba abunda nake tunani sai rayuwar dazan fara cikin wasu mutane da ban tab’a kawo zan shiga cikin su ba, daga kalar unguwar kad’ai zaka tabbatar cewar masu kud’ine ke zaune cikinta, sunan unguwar sharad’a phase2 gidaje ne muke wucewa masu kyan gaske, har muka k’araso inda aka bud’e mana tangamemen get muka tura motar aciki, tabbas na jima da sanin yallab’ai dan gidan yan gayu ne, babba ne gidan plat house saidai daga maigadi banga kowa ba, saida motar ta tsaya sannan driver ya saurin bud’e masa ni kuma na bud’e na fito ina zare ido, gidan yai kyau sosai komi mai tsari da burgewa ga flowers nan sun zagaye gidan gwanin sha’awa,

“Around 4:00 zaka dawo akwai inda zaka kaimu”

Ya risina cikin girmamawa yace, “angama oga”

Har ya fara tafiya ya waigo yana kallona ganin nayi tsaye, da hannu yai mun nuni da intaho binsa nake kamar kwai ya fashe mun aciki, har cikin katafaren falon da yagaji da kayan alatu, basai na tsaya bayanin komi ba falon karshe ne har yai hanyar da zata kaishi bed room d’insa ya juyo yana ce mun,

“Ohh sheet, JANNAH”

saurin jiyowa nai ina kallonsa jin ya sake Kiran wannan sunan na d’azun,
“Zamu d’an jira zuwa anjima sai mu isa can main house d’in namu, zaki zauna anan ko na nuna miki inda zaki huta sosai”

Gabana naji ya fad’i kamar mai koyon magana nace, “nan d’in inane to”

Brief case dinsa dake sagale kan kafad’arsa ya sauke yana d’an smile kafin yace, “this is my house, kina tsoro ne kar inyi balango dake ko?”

Na Sadda kaina k’asa nayi ba haka nake nufi ba, kawai dai dagani sai shi anan kamar hakan ba daidai bane……………inkinga anan d’in u are ok ki zauna”

Ya idasa shigewa ciki yabar ni nan zaune ga Ac ankureta don wani irin rab’a falon yake dauke dashi, duk kusurwar dana kalla hotunan sa ne masu kyau har saika rasa wanne zaka tsurama idonka, kudun dunewa nai cikin karamar kujera ina ta tunani,har basan na kama bacci ba.

Sosai nai bacci a takuren duk da ga sanyin ac din, can cikin baccin naji kamar ana kirana daker na bud’e idona tsaye yake gabana cikin suit mai tree pieces,amman babu coat din saman saurin tashi zaune nai ina daidaita natsuwa ta, bansan iyakar lokacin daya dauka tsaye gabana ba,

“Azhar tayi zakiyi salla ne?”

Jujjuya idona nai ina cewa araina wace irin tambaya ce wannan? Nace masa “ehy zanyi”

“OK muje na nuna miki hanya”

Yana gaba ina biye dashi har wani corridor wani daki ya tura single ne sai toilet kawai ga gado nan harda mirrow da wadrope,dakin so need ba wani hayaniya kominsa kalar light blue da white ne,

“Inkika gama saki hau gadon kiyi baccin sosai, za’a kawo miki abinci”

Kallonsa nayi cikin natsuwa nace, “nagode yallab’ai”

Ya amsa mun da idanun sa, wanda na gane hakan dabi’arsa ce ba da wani abu yake yi ba, jan kofar yai ni kuma na wuce na shiga bayin,a rayuwa ta ban tab’a shiga ban daki irin wannan ba to a ina zan shigesa ma? Lallai akwai kayan more rayuwa a wannan duniyar, da tab’e tab’e na gano yadda zan kunna ruwan yazo nai fitsari cikin kwamin wankan na kora da ruwa sosai, sanaj nai alwallar inayi ina kallon kaina a madubi kamar tab’ab’b’a, wai madubi a bayai kai jama’a.

Akwai karamin kafet shimfid’e a dakin nan nayi sallar ina yin addua sosai Allah ya kareni da sharrin dake cikin wannan aikin, ya sadani da alkairin dake cikinsa duk mai nufina da sharri Allah ya nisanta ni dashi, ba jimawa akai knocking naje na bud’e kuku ne ya mik’o mun abinci a tire ya juyawarsa kurin,

Komi akwai cikin tiren harda ruwa da spoos fork da normal spoon, kallon abincin nai tayi yayin da miyauna kamar zai jalalo k’asa, harda wani dafaffen nama yaji dahuwa yai ligib,na fara cin shinkafar ina lumshe idona ina korawa da lemu mai dan karen sanyi, ga nama zuk’u zuk’u acikin shinkafar saida naji cikina babu waje sannan na tsaya, nasha ruwa na gyaza ina hamdala rufe sauran nayi naja gefe ina istigfari da hailala.

Na dau lokaci inayi sannan na tashi na cire hijabin na hau gadon na kama bacci kamar Allah ya aikoni, har wani gyara kwanciya nake saboda dad’in gadon…………………

Mom muhseen✍????
[7/22, 2:45 PM] Mom Muhseen????: ????JANNAH????

{A TRUE LIFE STORY}

E.W.F

By
Mrs Bb
mom muhseen

wattpad name
Humaira3461

    ????️.......7

Bubbuga kofar da ake yasa nai firgigi na diro ina bud’e kofar tsaye yake duka hannuwan sa cikin aljihun wandon sa na suit din daya saka dazun, idonsa kurr akaina sai zare ido nake kamar an rik’e bakina na kasa cewa uffan, ashe wajen saukowa na baro kallabina acan, sannan da zan kwanta na cire hijabina kamar an tuna tar dani na juya da sauri ina figar hijabin na saka ina hadiyar wani miyau nace,

“Kayi hakuri yallab’ai bacci ne ya daukan”

Idonsa ya lumshe sannan cikin sassanyar murya yace, “kiyi salla sai mu wuce”

Harya ya juya ya dawo yace, “please kiyi sauri fa”

Kai na d’aga masa kamar wata sakara, ajiyar zuciya na sauke na je nayo alwalla na kabbara sallar, koda na gama saida nayi azkhar dina na yamma sannan na fito ahankali nake karema corridor din kallo, anbi an k’awata sa da abubuwa masu kyau, a falo na iske sa zaune computer ce yake ta dannawa sallama nayi masa sannan na risina yadda nake idan ina gaida babba,

“Yallab’ai ina wuni, na fito”

Sakin fuskarsa yai ya amsa mun cikin kulawa,naga alamar mutum ne shi mai son girmamawa rufe computer yayi yana cewa,

“OK muje daman ke kadai muke jira”

Binsa nayi har waje saida na fito ya rude k’ofar entrance din yana tilla ma driver makullin, ya cafe yana bude motar ya adana sa, kamar yadda muka zo dazun haka muka tafi yanzu ma.

Ko acikin motar wayarsa babba mai kyau yake dannawaa wani lokacin kuma yana ansa kiran waya, na fahimci normally nature dinsa ne wannan sanyin jikin, sa yin abu cikin natsuwa sosai bayada hayaniya ko kadan, ko magana yake silently yakeyi inyana waya saika natsu sosai inkana kusa dashi kakejin abunda yake fad’a, lab’e baki nai nace araina halan haka yan gayun suke?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Leave a Reply

Back to top button