KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

KYAWUNA JARABTA TA
✍️M SHAKUR

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.

LITTAFIN NAN NAKUDI NE BUT FOR NOW INA FREE PAGE SO U ALL CAN SHARE.
subscription is 500 idan kinaso kibiya nasaki a group zaki turo 500 into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.

S-SQAURE FASHION AND MORE GIDANE NA HIJABAI DA HADADDUN DOGAYEN RIGUNA NA DINKAWA, KUNSAN MA MENENE TANA WANI PROMO NA FREE DELIVERY KOWANI GARI KIKE IDAN KIKASAI KAYANSU ZATA AIKOMIKI DA KAYAN KYAUTA, DON MAGANA DA ITA KO CHATTING NATA UP DAN SAYAN KAYAYYAKIN SU CLICK ON THIS LINK wa.me/+2347030037697

Free page
EPISODE 1️⃣

Tudun Yola, Kano!
Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba’a dade da tarewa cikiba.

Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house dinan, tsakar gidan mai bala’in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y’ay’a sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai bala’in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.

Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude kofa ya shiga ciki.
Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi 60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida dayake budewa yana karantawa.

gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very fat gwanin ban sha’awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.

Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa tace “this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad” kiran sunan shi datayi yasa duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi “Ya Hamad good morning” batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan yazauna agefenshi yace “ina kwana Abba” sanan yakalli matar dake gefenshi yace “Ina kwana Mum” daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai tace “your food is ready Daddy Hamad” jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama Hamad yace “inka kaisu kabiya musu kudin makaranta” sanan yajuya yakalli matar dake gefenshi yace “me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane”? dasauri tace “kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa” daga chan sama aka amsa, wasu yan mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi yace “bari nakaisu Abba” gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana ba, sanan yawuce yafice.
Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki batare da an bari sun hada ido da Mami ba. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.

Duk suna zaune afalon harya gamacin dumamen tuwon yadauki ruwa yasha, Dan gyaran murya matan dake zaune kusada shi tayi Mum tace “Alhaji nace bari namaka tuni, kaga duka duka bikin Nana bayan Babban salla da sati uku ne, gashi lokaci nata matsowa yanzu baifi wata daya bikin ba, nasan dama kariga kabada kudin kayan daki, cha kayi daman wanan satin zakaban kudin kayan kitchen, kaga idan kabani nida Zainab saimu shiga kasuwa yau muyo siyayyan koya kika gani Zainab”? Mum tama Mami dake zaune tana sauraransu magana, gyadamata kai tayi sanan tace “eh hakane Abban Hamad” ruwa yadauka a cup yakara kaiwa baki yasha sanan ya ijiye cup din, hannu yasa a aljihu yaciro bandir din yan dubu daya guda biyu yabata yace “kinemi wata kijeda ita kasuwa, Zainab bazata iya zuwa ba itakeda girki, kuma yau lahadi ina gida” yana fadin haka yatashi yawuce sama duk suka bishi da kallo, saida taga yashiga dakinshi sanan tabata rai tace “Alhaji Alhaji bantaba ganin kafaffen mutum irin shiba wlh” tashi tayi batare data kalli Mami ba tai stairs tabude bangaren ta tashige dan saman bangare biyune nata dana Zainab saikuma dakunan yaransu guda uku, na maza kanana dana mata kanana saikuma na yan matan suma dakinsu daban.

Ahankali Mami ta tashi ta tattare duka kwanukan takai kitchen sanan tasa Mai aikinsu Uwani tazo tashare falon ta kunna turare sanan tai sama itama bude dakin mijin nata tayi tashiga bata wani dade aciki ba sanan tafito, direct dakin yan matan tayi ahankali tabude kofar, dakin nada dan fadi gashi a gyare Kal Kal, gadaje ne guda uku irin nayan boarding jere adakin kowanne da bangaren nashi saiga wardrobe na bango da kayan kowa keciki, bin kan gadajen tayi da kallo ganin babu kowa kai yasa takarasa shigowa dakin tareda maida kofan tarufo sanan tashigo ciki takaraso tsakiyan dakin saikuma ta tsaya turus tai shiru tana kallon gaban gadon dake tsakiyan dakin, wata faran budurwan yarinyace azaune akasa tabama dakin baya tana kallon bango tadaura kanta kan kafafuwanta ta, nimai rubutu M Shakur banmasan mutum bane awurin ba saida naga Mami ta tsaya turus tana kallon wajen, wani irin silk black gashin kaman na yar India ne zube awajen yana taba tiles din kasan daki sabida yanayin zaman datayi tsabagen tsayin gashin, sai farin kafanta sol mai bala’in kyau da dogayen fararen farcenta dababu komi akai sai uban haske kaman ana wankesu da madara. “Du’a” jin ankira sunanta yasa tadago kanta daga kifen dasuke akan kafafunta dasauri batare data waigoba jin muryan Mamin ta, dan Jim Mami tayi tana binta da kallo sanan asanyaye tace “inkin gama kukan ki tashi ki tattare gashin nan naki ki kulle kisa a hijabi kije Abban ki nakiranki yana dakin shi” tana maganan tawuce tafice daga dakin tarufo musu kofan.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button