KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Saida tashiga bayinma taga batada salla daman tun jiya takejin ciwo ciwon ciki, brush kawai tayi tai wanka da ruwan zafi sosai tafito daure da towel tanada feeling ciwon ciki kadan kadan dayake ita batada wanan serious ciwon aran nan saidan dan ciwon ciki kadan hakanan, wani black mickey riga tasaka, t-shirt ne amman irin na baccin nan babban gaske daya saukan mata har guiwa, batabi takan kama gashinta ba tasake shi ahaka yana lilo abinshi, komai ma bata shafa fa tasaka slippers dinta tabude kofan dakinta tafito ahankali, dakin Grandma tayi ganin bata ciki yasa tamaida kofan tarufe tai hanyar stairs tana sauka kasa, ganin Grandma zaune kan kujeran dakin rikeda Al Qur’ani tasaka glass a idanunta tana karantawa yasa takarasa wajenta zama kusada ita tayi ahankali batare datai magana ba tana sauraron yanda Grandma ke karatun anatse Akuma hankali Aya ta dire sanan takalli Du’a din alamun ya akayi, ashagwabe tana wani turo baki kaman yar baby tace “Grandma good morning cikina naciwo kadan kadan, MP ne, kinada magani”? girgiza mata kai Grandma tayi tace “bari zansa akawo miki, yanzu tashi kidebo ruwan lipton a flask kije daki kisha saikidan kwanta kafin lokacin zuwa office yayi” gyadamata kai tayi ta tashi dinning tayi cup tadauka tadauki flask ta tsiyaya ruwan shayi dayasha kayan kamshi sanan tadauki spoon tasa a cup din tawuce tai stairs tana tafiyan nan nata ahankali tana kallon shayin da kamshin shi sai ratsa mata hanci yakeyi, tsayawa tayi chak jin wani irin sanyi ya ratsa kafafunta dakenan abude zuwa jikinta gabaki daya, wani dan kara tafitar daga bakinta ashhhh sanan taduka kaman wacce zatai ruku’u tana duba kafafunta tana daga kafanta sama tana duba tafin kafan kota taka kankara ne ganin babu abinda ta taka yasa ta dago tacigaba da tafiya ahankali tana hawa stairs din zuwa karshe tashiga falon sama daidai Asad shima yafito daga corridor hanyar dakinshi yashigo cikin karamin falon yana lazy tafiyan nan irin na wayanda suka sha bacci, wani irin hada idanu sukayi dagashi har ita, chak ta tsaya tana kallonshi da duka idanunta awaje kaman zata hadiyeshi da ido, yana sanye da kayan jiya dataganshi dasu a hotel dinnan bambamcin kawai shine babu jacket din suit din da neck tie da alamu yaciresu ne, farin long sleeve t-shirt din ciki ne kawai ajikinshi daya bubbude boturan gaban rigan har zuwa kasan kirjinshi kana iya gashin kirjinshi dasuka kwanta lubbb idanunshi sundan tashi da fuskanshi lips dinshi sunyi pink yirrrr alamun yasha bacci sosai looking a bit scattered kaman ba shiba, yanda take kallonshi haka shima yake kallonta da wanan expression nashi dinan dabaka taba gane takamaimen wani yanayi yake ciki.

Wani irin rawa hannun data rike mug din shayin ta dashi ne yashiga wani irin rawa tana kallonshi jikinta na bar bar da batasan mesaba takasa koda motsi, tundaga kafa yakalleta zuwa kai saikuma ya basar kaman bai ganta ba yacigaba da tafiyanshi normal normal yazo tagefenta zai wuce kamshin da jikinshi keyi yawani yi splashing akan fuskanta wani irin salubewa mug din hannunta yayi ruwan shayin ya bare some of it yazuba akan kafanta kofin yay wani kara yahau tsalle yana tsaltsalleke stairs kafin daga bisani ya tarwatse, wani irin runtse idanunta tayi gam jin yanda kirjinta ke bugawa dum dum kaman zai fita jinta kusada shi kaman jikinshi zai gogi nata yattsun kafanta namata radadin zafi amman takasa ihu sabida yanda tashiga wani yanayi, wani irin beating kirjinta yakeyi tanajin sahun tafiyanshi yanabi ta gefenta yawuce yay stairs abinshi mayen kamshin turarenshi yagama wanke mata numfashi yasauka daga stairs din yay falo abinshi.

Sai alokacin tabude idanunta wani irin zama tayi a kasan wajen dagudu takama kafarta tadaura akan cinyanta tana hura yatsunta dake mata radaddin azaban zafi sosai tana kuka sosai amman mara sauti tana hura kafan…….

Zama yayi kusada Grandma dake karatu abinta har lokacin, murya chan kasa irin nawanda yasha bacci sosai yakoshi dinan yace “good morning Grandma” saida takai Aya sanan tai addu’a tarufe Al Qur’ani takalleshi tace “wanan bacci dakasha haka kaga yanda kai subu subu kuwa kaman wanda yay kwana uku yana bacci” dan murmushi yamata tareda lumshe ido yabude baice komiba, tashi tayi tace “bari kaga nakawo maka shayi mai zafi kasha zaisa kadan saki ko” gyadamata kai yayi yana kwanciya kan kujeran data tashi kaman wani dan yaro, itakuma tai hanyar dinning harzata wuce saikuma idanunta suna sauka kan mug daya gangaro zuwa nan stairs na kusa to the last dasauri takalli sama ganin Du’a zaune tana hura kafa tana share hawaye yasa tace “subhanallahi Du’a meya sameki kike kuka haka? Ince badai kin koma kafarki ba shine baki kirani ba” tai maganan tana hawa sama, tana kaiwa wajen takarbi kafan tana kallo aiko gashi nan yatsun sunyi jajir alamun sunsha ruwan zafi, hannunta takai takama kafadar Grandma tana kuka sosai mara sauti tace “Grandma zafi wlh” dasauri Hajiya tashiga kwalama Razika kira. “Razika Razika” Razika dake daki fitowa dagudu tari jin Hajiya na kwalamata kira, turus ta tsaya afalon tana kallon Asad dake kwance abinshi idanunshi bude kaman yasan ta inda zata fito kenan kallonta yayi shima, fitowa Shemau tayi ganin Asad yasa dasauri tadan rusunna tace “ina kwana” gyadamata kai kawai yayi batare data amsaba hakan yasa Razika itama tace “ina kwana” ko kallonta baiyiba yadaura idanunshi kan TV dasauri duk sukai stairs, Grandma tace “kawomin zuma Razika Du’a tazuba shayi akafa” dawani irin sauri tajuya tace ” to” zuman dake dinning tadauko tadawo sama, karba Grandma tayi tashafamata sanan takalleta idanunta sunyi jajir tace “sannu dena kukan to” gyadama Grandma kai tayi tana share fuskanta takalli Razika tace “kaita dakinta ke Shemau biyoni ki debi wani shayin ki kaimata saiki gyara wajen nan” duk amsawa sukayi da to sanan tawuce kasa, Ganin Asad na nan inda tabarshi yasa tace “wai jikata ce shayi ya bare ayatsun kafarta take kuka shegen raki irin na Du’a bawani konewan kirki bane bafa, itace jikata datazo daga kano yar wajen Zainab, bari kaga nabaka shayin ka”.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

      ✍️ M SHAKUR 

This book is 500 nakusan gama free pages, you can join the group by paying 500 into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na wa.me/+2347012181461 sainai adding naki to the group.

free page
EPISODE 2️⃣8️⃣

Zubomai shayin tayi a mug dakanta sanan tadawo kusada shi kafanshi tadauka tace “sit up my friend” dan murmushi yamata yatashi yazauna tareda mika hannu yakarbi shayin yace “thanks Grandma, you are the best you know that right” murmushi tamai tace “nasanar da Ammin ka kana nan, ya TV show dakayi angama lpy”? yatsine fuska yayi yakurbi shayin kadan yacire daga baki yace “it was stressful but Alhamdulillah nagama” dan dariya tayi tace “kai Asad, yanzu dai mezan dafamaka yau kaci ka koshi” ahankali yace “rice and beans nakeso Grandma” “kaida shinkafa da wake Asad shikenan zan dafamaka” murmushi yamata yace “Grandma bakiyi fushi dani ba tunda nadawo banzo ba” hararanshi tayi tace “ja’iri ashe kasan kayi laifi” dariya kadan yayi yana kurban tea, tace “ai nayi fushi dakai but Sharif nata gayamin how busy u were saisa andena fushin, yanzu daka gama bagaka kazo ba, ai ba’a raba jika da kakanshi” hira suka cigaba day haryana bata labarin aikinshi sosai taji dadi yanda yasake dudda batamai maganan abinda yasameshi jiya ba, saida yagama tass sanan ya ijiye cup din yace “Grandma bari naje na shirya natafi office, I have huge work awajen ma” tashi tayi tace “tafi Asad, Allah yataimaka kaji, nidai kadingayi kana neman mata inaso naga jikana kafin namutu” yatsine fuska yayi irin ewww dinan bayamason maganan sanan yawuce yafita daga falon yatafi itakuma Grandma takoma tai zamanta dan akwai shirin dazata kalla.
**

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button