KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Fitowa daga dakin Du’a tayi tana murmushi tana tattaba wayanta dan Aneesa ce kebata dariya tana kawomata karan Mariya waita sace mata zobenta, typing yakuri tayi sanan ta ijiye wayan kan dinning tawuce tana tafiyan nan ahankali takarasa gaban fridge din dake dinning din tabude dan kishi takeji sosai, wani karamin bottle water mai sanyi taciro tana kallon goran, maida kofan fridge din tayi tarufe kafin ahankali tashiga bude marfin goran sanan takafa ahankali abaki tawani lumshe ido tanasha.

“you know cold water is not good for the body” kaman daga sama taji murya kaman na Sharif akanta, dawani irin sauri tabude idanunta tareda juyowa, yana zaune kan dogon kujera shi kadai a falon yana sanye da 3quater na sojoji da farin t-shirt yana rike da system dake kan cinyanshi, dudda taga ba kallonta yakeba amman saida taji wani irin kunya dasauri ta ijiye ruwan sunnar da kanta kasa tayi amugun kunyace tace “Ya Sharif ina yini” batare daya kalleta ba still yana aikin dayakeyi ne yace “hope u good” gyadamai kai tayi ahankali tama rasa mezata ce tace “uhmm kaga Grandma dina? Tana sama bari nakira maka ita” tai maganan tana fitowa daga dinning tai stairs dasaurinta harda dan gudun ta, wani irin turgudewa tayi kafanta ya lankwashe dayasa tasaki wani irin wawan ihu. “wayyo Allah na kafata” tashi Sharif yayi daga kan kujera dasauri yawaigo daidai lokacin Grandma datagama wayan datakeyi tafito kenan taji ihun ta tazo stairs din dagudu tace “subhanallahi maiya faru? Muga kafan” Hajiya tafadi dasauri tana karban kafan da Du’a takasa ijiyewa kasa tsabagen azaba tana dan kuka mara sauti dan yamugun mata zafi, cikeda tausayinta Hajiya tace “sannu ijiye kafan nagani” gyadamata kai tayi tana kokarin ajiye kafan akasa wani irin ihu tayi saikuma tafashe da kuka sosai wanan karan mai kara tace “dazafi Grandma” cikin dan fushi Hajiya tace ” kinsan wajen nan bene ne akan wani dalili zaki dinga gudu akai eh” cikin kuka sosai tana kokarin kama hannun Hajiya dake liliyamata kafan tace “zan kiraki ne naga Yaya Sharif yazo” cikin fada Hajiya tace “Sharif da tuntuni muke tare muna hiranmu har tuwo yaci, sama nazo nayi waya, koma bansan yazo ba gidan nan ba Bakin Sharif bane har sama zai iya zuwa wajena, Sharif zo dan Allah kadubamin kafarta kotasami targade ne, kosu Razika basu kadai ba duk wanda zaizo gidan nan hanashi gudu nake akan bene dan hatsari ne da bene yanzu jibi”, karasowa wajen Sharif yayi dawani irin sauri takai hannunta ta share hawayen daya bata fuskanta, Hajiya data matsa gefe tace “au uban kukan dayagamaji kinayi dan yazo nanne zaki wani goge hawaye” turo baki tayi ta dauke kai, Hajiya tace “kaji Sharif dubamin kafan kagani” ahankali yakai yatsunshi biyu yadaura kan kafar datai ja sabida turgudewan yanabin dogayen feet dinta da kallo yace “does it hurt” yadan dagakai yana kallon fuskanta, hadiye zafin tayi tagirgiza mai kai alamun a’a hakan yasa Hajiya tace “kafan dakika gamawa kuka ne kike cewa baya zafi”? Murmushi yadanyi yace “buguwace kawai tashafa man zafi zai daina mata zafi” yay maganan yana sauka kasa abinshi, hararanta Hajiya tayi tace “wuce kije kishafa robb akai Allah kika karamin gudu agidan nan saina saba miki Du’a, kidena guje guje kinji” gyadamata kai tayi ashagwabe tace “tom” “wuce kitafi dakin ki, wani aiki Sharif ketayani yi” gyadamata kai tayi tawuce ta tafi tana tafiya ahankali Hajiya tabita da kallo saida taga tabude daki tashiga sanan tasauko tace “Allah kyauta” karasowa tayi tazauna kusada Sharif tace “wai shi gogan bazaizo yagaidani bane” dariya Sharif yayi yana abinda yakeyi yace “finally kinyi admitting kinyi kewan Asad” hannu tadaga kaman zata dakeshi ya kyalkyace da dariya yace “wlh aiki sosai ne aikin nan dayakeyi shi kanshi yagaji kinsan Asad ya tsani takura shida yasaba saidai yatakurama mutane shi baiso atakuramai Allah Allah yake gobe tayi yagama, da sassafe fa yake fita kullum” murmushi Hajiya tayi tace “Allah sarki Asad, kana ganinshi haka akwai kwazo da zuciya” murmushi Sharif yayi yace “nidai idan yazo kicemai wlh yafito da mata yay aure inba hakaba dudda ina kanninshi aure abuna ni zanyi na barshi” yay maganan yana batarai, wani irin baki Hajiya tasaki tana kallonshi tace “ohhh jama’a yauni naga takaina, kaiwai mara kunyan inane Sharif, yoo dan kaniyan kama duka duka da wata nawa ya girmeka wata uku ne fa tsakaninku haka Amminku tagayamini, Asad nada wata uku aduniya aka haifoka” dan dariya Sharif yayi yaturo baki cikeda rashin kunya yace “nidai gaskiya nafadi muku aiko Ammi nagayamata ni wlh aure nakeso kuma shi Asad banga alamun ya shirya aure ba Hajiya wlh yaron nan kaman aljani shi yama tsani mata, basa gabanshi the only matan dayakema murmushi yayi hira yay wasa dasu aduka fadin duniyan nan guda biyu ne daga ke sai Ammi, kinsan ko Anty Turai kanwar Abban mu bayama murmushi cewa ma yake he hates her, to ina zan tsaya jiran irin wanan saiyay aure zanyi ai namutu tuzuru hakanan Hajiya wlh a’a” wanan karan hannu Hajiya takai ta dakamai duka abaya dayasa yakusan sakin laptop din yace “aashhh” dauke laptop din tayi tace ” naga alama kwana biyu ban jibgeka ba saisa bakada kunya, mugama aikin dakakemin Allah sa ba shirme kakeba dan naga hankalinka baikai” tai maganan tana saka glasses a idanunta tana kanne idanu danta karanta report din daya rubuta mata, karban system din yayi yace “ni dai tsaya na karanta miki natafi gida nai waya da budurwa ta kuma saina gayamata kece duk kika cinye mata time” dariya tayi tace “kagaya mata hala tamadan soka sabida yanda ba’acin kudinka at least ni Kakar ka ina moreka” dariya yayi sosai sanan ya shiga karantamata…..
wa.me/+2347012181461

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

         ✍️ M SHAKUR 

Free Page
EPISODE 2️⃣4️⃣
yauma kaman kullum suka tashi suna breakfast malamin su yazo ta tafi wajen nata su Razika ma haka, as usual by 1 yatafi, daki takoma ta kunna TV tunani kala kala aranta, wanan sanarwan nan na iya tasake saurara rasa abinda zatayi yasa tabude kofa tafice daga dakin, dakin Hajiya tabude tashiga dake meeting a zoom na retired lawyers, ita kebada report din ga glasses akan idanunta, kallon Du’a dake kallonta tayi hakan yasa Du’a tashigo wani book dake kusada ita tadauka rubutu tamata sanan tabata kallon rubutun Hajiya tayi ta gyadamata kai tareda daukan purse dinta ta zaro 10k tabata, karba tayi cikeda jin dadi tafito daga dakin sanan tasauko kasa da sauri tana murna tai wajen Razika dake dakinsu tace “Grandma tace kirakani saloon jeki shirya nima bari na shirya” gyadamai kai Razika tayi tace “kinbar wayan ki a dinning tun jiya” murmushi tayi tace “zan dauka nasan Su Aneesa ne bari naje na shirya” sama tayi, shiryawa tayi cikin wani black abaya mai kyan gaske, sanan tazauna tai rolling veils dinta dayay kyau shima ta feffesa turare tafito rikeda handbag, a falo tasami Razika tace “yauwa kin shirya muje to” gyadamata kai Razika tayi suka fice, driver Hajiya ya kwashe su zuwa wani saloon daba na ranan nan ba dantace dagaske bazata wanan ba, tsife mata kalaban akayi sanan aka wanke mata kan sai murmushi take ta kosa agama, gamawa akayi aka mata blowing hair din yabushe tass sanan matan tace “Hajiya wani style za’a miki” dasauri Razika tace “asake mata kalba amman yan kanana kanana this time” dasauri Du’a tace “a’a ayi manya manya” dasauri Razika tace “please amiki kanana Du’a ai tanada sauri” dagakai Du’a tayi takalli matan tace “idan kikai kanana zaki gama kafin 4” kasa magana da kyau matan tayi sabida idanun da Du’a ta zubamata yarinya kaman ita tai kanta. “eh bakice komiba zaki gamamin kafin 4” kasa magana matan tayi sai kawai gyadamata kai datayi murmushi sosai Razika tayi tace “kingani na gayamiki za’a gama, afara to amata mai kyau mai style” fara mata kalaban matan tayi tana mamakin yawan gashin Du’a dakeda tsayi, tsayin shikecin lokaci ma ba asalin kitson ba, wajajen 3 Du’a takalli uban tulin gashinta da ba’ayi ba tace “3 yayi sai yanzu mukai rabi” kallon fuskanta matan tayi ganin Du’a tayi kaman zatai kuka yasa dasauri tace “yakuri gashinki nada tsayi sosai ne gashi robber hair, I am going as fast as I can, zan gama dawuri” gyadamata kai kawai Du’a tayi matan tacigaba da kitson da saurinta, tanaji tana gani 4 yayi ana kan kalaban ba’a gama gamaba sosai taji hawaye yazo mata amman ta daure tahana kanta wuraren 5 matan tagama, tashi tayi tsaye da sauri tana parking kitson da ribbon dinta tadau gyalen ta ta tafa wanan karan batama tsaya rolling ba duka kudin da Hajiya tabata tabama matar sanan takalli Razika tace “muje” tashi Razika tayi suka fito tace “wai ina kike sauri zakije ba gida zamuba” girgixa mata kai tayi suka shiga mota, tace “dan Allah transcorp hotel zaka kaimu” sanan tajuya takalli Razika tace “program liyafa akeyi na matasa kan fara sana’a tun karfe hudu aka fara” gyadamata kai kawai Razika tayi dan batasan wani program bane ba akeyi ba but yanda taga Du’a tasan it must be something very important to her.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button