KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wuraren 4 Dad yakira Asad dabayanan awaya, bai daukaba akaro na biyune yadauka, Dad yace “kana office ne” cikin muryan nan nashi na baison magana yace “ganinan zan shigo gida” katse wayan yayi yashigo yay parking sanan yafito yana kara kallon yanda ake aikace aikace ana decorating gidan for event sanan yay falonsu, Dad yagani zaune da kowa afalon ga wasu kwalaye sweet, goro tabarma da sauransu akasa duk ana magana, ganinshi yasa akai shiru yaran duk suka gaidashi, karasawa yayi yazauna kusada Sharif ahankali yana yatsine fuska danyagaji, harara Anty Turai ta watsamai, murya chan kasa yace “Dad gani” murmushi Dad yayi yace “My Son the latest ango, anyway family din wife dinka gabaki dayansu sunzo suna around, mahaifinta da kannen mahaifinta maza biyu, da macen, sai matanshi biyu da Maman Du’a da kishiyar, dakuma duka yaransu, da mahaifiyar Babanta Kaka su, inaso dakai da Sharif dawani abokinka ku shirya bayan magrib kaje kai gaisuwan iyaye ka gaidasu sanan kutafi da all this, bayan sallan isha’i mahaifinta da kannensu wai zasu tafi masaukin su, nayi nayi dasu su kwana tunda sunada nasu flat din, amman yace bazai iya kwana agidan suruka ba, so ku shirya karka bata musu lokaci kaji” gyadamai kai yayi, Sharif yace “tashi muje mu shirya, nama riga nakira Jabir” yatsine fuska yayi yatashi, Rahima nawani dan murmushi tana mamakin Asad kaga yanda yakeyi ne kaman ana tursasashi Ammi sai kallonshi take da tsoro karyace yafasa saisa wani sabon lallabashi take kwanan nan Allah sarki Ammi batasan danta yafi kowa son bikin nan ba.

Flat dinsu suka shiga fadawa kan kujera Asad yayi ya kwanta yana lumshe ido, baki Sharif yabude yace “kasan karfe nawa kuwa katashi muje mu shirya” hararanshi Asad yayi yace “ko sarakai ne suka zo wlh sainai bacci na natashi I am tired” yay maganan yana lumshe idanu, girgiza kai Sharif yayi kawai yawuce dakinshi, kayansu da ya dinko dan shine Ammi tabama ragamar dinka all kayan Asad na biki yaciro wai hadadden ash din gizna da akamai riga da wando rigan har guiwanshi dawata bugaggiyar hula tambari daya shiga da shaddan, da sabon takalmi na Tom Ford da agogo dawasu sababbin turaruka yabufe dakinshi yabijiyemai komi akan gado sanan yawuce yakoma dakinshi yana kara kiran Jabir daya cemai gashinan a estate dinsu, shigowa gidan Jabir yayi sanye da kayan asibiti ajikinshi parking yayi yafito yawuce side din su Asad, ganin Asad kwance yana bacci yasa baiyi wata wataba yadaka mai duka abaya, tashi zaune Asad yayi dasauri yana shafa bayanshi hararanshi Jabir yayi yace “mune angwayen dazamu rigaka shiryawa, dalla Malam wuce muje kai wanka” dan gajeren tsaki Asad yaja cikeda kulewa yatashi ahankali yana gaba Jabir na biyedashi sukai sama yanaji yana gani suka sashi yay wanka, shegen wankan nashi ma saida yasa sukai missing magrib a mosque yana fitowa sukai jam’i anan falon sama sanan suka shiga saka kaya, Asad kadaine yasa ash shadda da Jabir da Sharif wasu fararen hadaddun yadi sukasa, fitowa Asad yayi ya shirya tsaf, koshi Sharif daya kalleshi saida yakara kallonshi rabon dayaga Asad da hula akai harya manta, guda yafara yace “wooo ango saura 2days da kacal” tafi sukayi shida Jabir suna dariya, Asad yace “wlh zance nafasa zuwa” yakuri kumuje inji Jabir, saukowa sukayi saida suka fara shiga wajen su Ammi, kasa daina murmushi Ammi tayi dataga danta saiya mata kaman ba Asad dinta ba, yanda suke kallonshi yasa yawani juya cikeda bori yace “kokuzo muje kona fasa zuwa” dasauri Dad yace “kunga kuwa ce kutafi Dr, za’a biyoku da kayan yanzu kafin dan borin nan yafara” dasauri suka bishi su Rahima sai dariya suke dannewa.
A compound suka sameshi tsaye yana daddanna waya, hannunshi Sharif yakama yace “stop being anxious jor let’s go” ko kulashi baiyiba ba suka fice, dayake anriga ansan da zuwan su an gyara gidan tsaf tsaf, Hamad ne yafito ya taresu yana kallon Asad da kallo daya yamai yagane shine mijin sabida yanda yafi dukansu haduwa, hannu yabasu sukai musabaha sanan yace “bismillah” yay gaba suna biyedashi abaya, gidan Grandma gidane daya saba zuwa amman yau sai gidan yamai daban, suna shiga falon Kaka ta kece dawani lafiyayyen guda kaman ba tsohuwaba, kowa na falon kallonsu suke barinma Mom dasu Nana dan basu taba tunanin mijin yahadu hakaba, awani sabon ruug da aka shimfida afalon suka zauna cikeda girmamawa, cikeda natsuwa sukai gaisuwa, amsasu Abba da kannenshi sukayi kafin anatsu dakin yay shiru, sanan ahankali Abba yace “Asad” dago kanshi ahankali Asad yayi, Abba yace “nasan banda ni da mahaifiyar Du’a babu wanda kasani anan, gabaki dayan wajen nan dakake gani yan uwan matan ka ne bari nafara da kainena Baffofin ta” sanan yanuna gefenshi yace “wanan shine Mustapha mai bina kenan da Auwallu, dagashi sai Aisha damuke kira da lami gatachan” yanunamai matar dake kusada Kaka tana murmushi tana kallon su Asad din taga hadaddun yan gayu, sanan yanuna Kaka yace “wanan itace mahaifiyata, Hajiya Kaka” washe baki Kaka tayi tanacin goro, sanan yanuna Mom yace “itace mata ta tafarko, mahaifiyar Hamad, Nana, Hawwa, Amra, da Amira duk gasunan” yanuna su gabaki daya, sanan yanuna Aneela dake kallon Asad din yace “ga kanwar Du’a dake binta, Du’a ce tafarko awajen mahaifiyar ta sai Aneela, sai mazan nan Mudasir da Muhammad” dukansu kallonsu Asad dake to some extent baiyi blaming illiterate tsohuwan chan dake kiran Du’a da mayya ne ko whatever like idan kaga this whole family zaka rantse ka kara rantsewa sanan ka kara rantsewa ba daga gidan Du’a tafito ba, babu tawani abu da Du’a tai using tai kama dasu, da ita dasu kaman gabas ne da kudu, gabaki dayan family bakake ne, black beauties suna kyau masha Allah, ga yaran bakutaye kaman Du’a dan itama ba wata siririya bace, amman dai sun fita kiba but still ko kadan Du’a batai kama dasu ba”. Sosai Hawwa ke kallon Jabir daya mata kyau sosai har saida suka hada ido dasauri tadauke kai, fada aka musu kannin Abba suka bashi shawarwari na rayuwan aure, bayan sungama Kaka tace “sanan karike zikiri sosai, wanan da bamusan tsatson taba karkayi bakin dare” wani mugun kallo Abba yamata dayasa taharareshi ta fito da goronta ta balla tai shiru, saida aka kira isha’i sanan suka tashi kudi suka ciro mai yawa suka ijiye akasa Abba zaiyi Magana Kaka tawani zabura tamike hartana take kafan Mom takwashi kudin tana shimusu albarka, girgixa kai kawai Abba yayi yama kasa magana suka wuce suka fita har gate tarakasu Kaka na godiya sanan aka shiga shigoda tabarmai da kwallayen sweet dinda suka kawo.
Mom kaman zata mutu wanan hadadden mijin da Du’a tasamu bashine wanda tagani kwanakin baya a TV ba ana hira dashi, wanan yaci uwar Muhsin a kudi da kyau dakomima, wayyo Allah na tafadi zuciyanta namata zafi.

6️⃣1️⃣
DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461

????????????????????????????????????????????????????

GYARA SHINE MACE

ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK’I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI
????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button