KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Gidansu yashigo ranshi fess yaja motanshi yatafi office abinshi.

Saida Asad yafita Grandma taji karan bude gate da fitanshi sanan ta daddage ta dakama Du’a dakekan jikinta duka acinya tace “tashi dan gidanku kidubeni nan” tashi zaune tayi ahankali tana turobaki, Grandma tace “ba asama na barki ba da yaushe kika fita danaga kin shigo ta kofa” turo baki tayi tace “ta window” shiru Grandma tayi tana kallonta anyway bama ta tambayan nan takeba wanan ne most important one ahankali tace “Du’a yaushe kika fara son Asad” sosai take kallon Grandma lips dinta harrawa yake tanaso tafadi mata gaskiya but tana tuna uban kashaidin da Asad yamata, tashi tayi takai hannayenta kan fuskanta tace “ni kunya nakeji” tai stairs da sauri tanadan dingishi, tafi Grandma tayi tace “jama’a yau naga yarinya, agaban kowa tagama cewa tanason yaro, yanzu ni dana tasata agaba ina mata tambayan shine take cemin tanajin kunya ai shikenan” tai maganan tana murmushi wlh bazatai karyaba har cikin ranta taji dadi, tun ranan da Hamad yakawo Du’a data daura idanunta akanta aranta taji zataso tahada Asad da Du’a aure, sai gashi Allah yatayata kome zai faru yafaru she will make sure that this marriage work, kwalama Razika da Shemau kira tayi dasauri suka fito, cikeda fara’a Grandma tace “kuzo inaso na aikeku kasuwa direbana na kaiku ku sayomin sweet da goro, an daurama Du’a aure da Asad dan wajen Ammi yanzun nan mahaifinta a masallaci kutayani murna” gani kawai Grandma tayi sunhau tsalle, Razika tace “Ammi ni duk idan yazo gidan nan dama nakanji inama ace Du’a budurwanshi ne wlh naji dadi” dariya Grandma tayi tace “nima haka, ungo kudin nan kuga kuje ku sayomin narabama jama’an Annabi suci su shaida su sama auren jikata albarka insha Allah mutu karaba, wuce kutafi” karban kudin sukayi, Grandma tadau wayanta takira danta tasanar dashi sanan tashiga kiraye kiraye tana sanarda jama’a.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

  ✍️ M SHAKUR 

EPISODE 4️⃣5️⃣
Wuraren Magrib suka shigo gidan, motan Sharif ne agaba na Asad biyedashi, suna parking suka fito agurguje sukai alwala anan pampon tsakar gida sanan suka fita zuwa masallaci salla sukayi suna idarwa Sharif yaga sai musabaha akeyi da Asad ana cemai Allah ya sanya alheri Allah ya sanya albarka, tabe baki yayi yace wanan hala yasayama masallacin wani abune, gaba yayi dan yunwa yakeji, Asad din yabiyoshi daga baya, suka shiga gida Sharif yace “muje muci abinci please I am starving” hararan Sharif din yayi hakan Yasa Sharif yaja hannunshi yace “common d more kana gudunma Anty Turai d more tanamaka iskanci idan ta ganka muje jor” janshi falon yayi kowama zaune a dinning harda Dad ganinsu yasa Dad yace “daman ku muke jira let’s eat” karasowa sukayi ahankali yace “evening everyone” sanan yaja kujera yazauna Anty Turai ta ballamai harara amman ko kallonta baiyiba, ahankali sukecin abincin jikake tsit babu mai magana ma Aneesa sai satan kallon Asad din take dataga yamata kyau, saida aka gamacin abincin sanan Dad yadau tissue yashare bakinshi yace “nobody should leave the table akwai abinda zan gayamuku listen up” duk gyara zama sukayi suna kallon Dad din banda Asad da yaciro wayanshi yana daddannawa, gyaran murya Dad yayi yace “I believe dukan ku nan kunsan Du’a, Du’a yarinya ce that has been through a whole lot………nan yabasu labarin Du’a har zuwa dalilin zuwan ta Abuja everyone was shock barinma Sharif dayaga he’s a bit closer to him and bata taba gayamai rayuwanta ba, sanan Dad yacigaba yace “yau mahaifinta da mahaifiyarta sunzo…….. nan yabasu labarin komi harzuwa inda Du’a tace Asad takeso har aka daura aure har kawowa yanzu” yanda gaban Sharif ke fadi haka na Aneesa kefadi danasu Rahima dan sunsan yanda Sharif keson Du’a, haka kuma sunsan yanda Aneesa keson Asad dudda bata taba fadamusu da bakinta ba, kasa hakura Sharif yayi yajuya yakalli Asad dake daddanna waya abinshi kamanma baisan mesukeyi ba yace “kai kanason ta ne Asad” girgixa mai kai yayi yana tabe baki, cikin yanayin wulakancin nan da halin basarwa irin nashi yace “Ammi made me do it” dukansu juyawa sukayi suna kallon Ammi, dasauri Ammi tabude baki zatai magana Dad yace “yes Ammi ku tasa yay haka but I am in support of hakan datayi inba hakaba tafiya da ita zasuyi maybe ma amaidata kauye, so for now abar maganan aurensu ahaka harzuwa komi yay sanyi ya lafa, auren is not like irin eh aure aure is just to save the girl ass, dazaran komi yalafa Asad zai iya rubuta mata takarda and free the girl idan tasami miji ta auri duk wanda takeso” ahankali da Anty Turai ranta yake a mugun bace tadan saci kallon yarta dake gabda kuka amman daurewa kawai take jitayi ta harzuka sosai tace “maganan banza maganan wopi, wani irin banzan abu kukasa danku yayi eh? Ina ruwanku dawata Du’a ba dangin iya bare na Kaka haduwan Abuja, yar uwanmu ce ko danginmu ne dazakusa yaro ya aureta just to save her, ba kauyeba ko wuta sukakai yarinyar me ruwan mu ba yarsu bace inma sun kasheta ai su suka haifi kayansu, ni dama tun ranan dana fara ganin yarinyar naji bana sonta, nidai wlh inhar da raina banyi accepting auren nan ba so I as much am concern Asad is still very single in my eyes kuma zamu nemamai mata……” tsareta Dad yayi yace “to menene abin tada jijiyoyin wuya anan Turai eh? Kedai wlh baki raina abin fada, shi yaron kinga yanaso ne”? Cikin fushi tace “wani irin tambaya Yaya kakemin haka? Asad fa namiji ne eh? Inhar yarinya nada nono da duwawu mezai hana kar Asad yasota nan gaba? Anfa riga an daura aure yarinya tazama tashi halak malak, namiji anbashi mumnunan yarinya dabayaso amatsayin mata yadurama yarinya ciki balle kuma anbama Asad mai kama da mayun nan dako yan uwan ta tsoronta suke, ai wlh Asad ya shiga kenan, ni wlh ku masifan batamin rai and nagayamuku I will never ever accept that girl, Yaya sabida rashin mutunci da rashin ganin amfani na ma ace ina gidan nan fa babu inda naje, ni kadaice kanwarka yar uwarka aduniyan nan amman kuje kuyi abu dagakai sai munafukar matarka baku sanar dani ba san……” Tashi Sharif yayi fuuuu yawuce yafita, Turai tabishi da kallo, ahankali Asad dake daddanna wayanshi yatashi yabishi yafice shima, tashi Aneesa tai dagudu tai sama su Rahima da Mariya suka bita sama itakuma Anty Turai tashiga surfafama Dad da Ammi bala’in ta inda take shiga batanan take fitaba Abba yay shiru kaman ruwa yacinyeshi dan he’s even confused, ba’a taba trusting namiji da mace shi karan kanshi bazai iya kirga mata munana da bayasonsu yan office dinsu dayaci ba, baya sonsu ko kadan amman saida yacisu balle kuma mai kyau, what if Asad sleep with this girl, what if yama yarinyar nan ciki ga yarinyar da shegen kyau ya zaiyi kenan?…..

Fadawa kan gado Aneesa tayi tafashe dawani irin mugun kuka, shigowa su Rahima sukayi suna maida kofan suka rufe, ahankali Rahima takaraso gaban gadon ta zauna tana shafa kan Aneesah tashi tayi dagudu ta rungume Rahima sosai tana wani irin kuka, ahankali Rahima tace “kiyakuri Aneesah ba” dasauri Mariya tace “kiyakuri Aneesah ni banmaga abin kuka ba kema ai kinsan Asad bayasonta kumama ai temporary aure ne” wani irin hararanta Rahima tayi tace “angayamiji akwai wani abu waishi temporary aure ne aduniyan nan, ni wlh Sharif ma yafi bani tausayi, ita Aneesah babu wanda yasan kina naki ai komu baki fadamana ba, shiko Sharif ya nunama kowa yanason Du’a, kwata kwata Ammi batai planning abin da kyau ba but nasan harda sabida Asad ne agida Sharif bayanan da am sure Ammi Sharif zatasa ya aureta dan yafi kirki dan Ya Asad dakeda bakin halin nan ai gana mata azaba zaiyi” dagakai Aneesah tayi cikin kuka sosai tace “da yardan Allah sai Ya Asad yagana mata azaban da saitai dana sanin cewa tana sonshi, wlh wlh Du’a mayaudariya ce kuma makira ce algunguma maicin amanan friendship, ita kadai nafadama inason Ya Asad” dasauri su Rahima har suna hada baki sukace “dagaske” gyadamusu kai tayi tace “ana gobe birthday dina ranan Thursday wlh saida na gayamata har tana cemin tona gayamishi ai gashi ita tagayamai, wlh Du’a makirace Allah ya isa tsakanina da ita wlh bazan taba yafemata ba duniya walahira wlh wlh ko” tsabagen bakin ciki tama kasa magana sai kuka, ta bala’in bama su Rahima tausayi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button