KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Agaban wani gida mai kama da mansion sukai horn bude musu akayi suka shiga, Sharif na parking yabude mota yafito yana attishawa, daidai wata kyakkyawan mata tana sanye dawani hadadden lace tafito kana ganinta kaga mamanshi sabida kamanninsu tana ganin dan nata ta tsaya turus tana kallonshi ganin yanda yay sharkap daidai nan shima Sharif yafito yana murmushi dasauri takaraso wajen tace “what on earth happen daka jike haka son” ranshi abace yace “lemme shower Ammi” yay wucewan shi, tabishi da kallo saikuma tajuyo takalli Sharif dataga yana murmushi tace “maiya faru yaji ke haka Sharif kaima jibi yanda kai daka daka kaman kai wasa a mud”? Dan dariya yayi yace “aikin Allah mukayi Ammi” aikin Allah? ta maimaita gyadamata kai yayi yace “Ammi we just saved a girl dabadan muba data mutu arijiya wlh, Asad yacirota daga rijiyan nikuma na ciro both Asad and the girl, nima bari naje nai wanka” shima yawuce yabar Ammi awajen baki bude.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

        ✍️M SHAKUR  

free page
EPISODE ????
Gban wani hadadden flat yayi ya bude kofa ahankali yashiga, kaga flat din zaka dauka a turai kake, sama yayi yabude wani daki da komi nacike kenan blue, bathroom yabude yashiga danyay wanka, koda yafito shiryawa yayi cikin 3 quarter da singlet fara, sanan yafito anan falon sama yaga Asad zaune dagashi sai towel daya daura a waist dinshi fari, tulin gashin kanshi ajike da ruwa yana tsiyayar da ruwa, ruwan nabin fuskanshi yana diddiga akan kirjinshi gwanin ban sha’awa, dark skin dinshi nawani irin glowing dankomai bai shafaba yana fitowa daga wanka yatuna da abinda yakeyi dazu a mota yazo yazauna yacigaba, kirjinshi kaman zai fashe acike tsabagen work out gashi da uban hair akirjin dasuka kwanta sukai lub lub har wajen cibiyanshi da maranshi, hakama muscle dinshi amurtuke yadaura MacBook din akan cinya nashi yana danne danne ya mikarda kafafun shi yadaura kan wata cushion. “katashi kasa kaya Asad yanzun nan fa kabar cikin rijiya kayi wanka basaikasa kayaba” kaman ba dashi ake magana ba yamai banza dan haushin shi yakeji sabida abinda yamai dazu, tabe baki Sharif yayi yace “koba komi dai after such a long time nasa kayi taimako u just save a life today wired dude kawai” dago kanshi yayi yawani kalli Sharif din irin kallon nan na dani kake, dagamai gira daya Sharif yayi sanan yawuce yace “am starving idan kagama come down muje ka gaida Dadda, nidai natafi wajen Ammi naci abinci” yawuce yasauka kasa abinshi batare daya karabi tanan Asad dinba tunda yaga fitina yakeji, baitaba ganin fitinannen yaro dan bala’i irin Asad ba.

Yadade yana danne danne sannan yarufe system din yatashi daidai lokacin iPhone 13pro max dinshi tahau ringing kobai kalli screen dinba yasan Ammi ce hakan yasa yadauki wayan yakara a kunne cikin muryanshi dakeda dan sanyi yace “Ammi gani nan zuwa” katse wayan yayi ya jefar kan kujera sanan yashiga wani daki, shi dakin komi off white ne ba kaman na Sharif ba, hoton dake jikin bango nashi zaisa kagane wanan dakinshine, gaban madubi ya tsaya dayacika da kayan shafa sanan yadau cream ya shafe jikinshi kafin yabude wardrobe yadauko wani 3quater maroon da white t-shirt yasaka dasukamai kyau sosai sanan yakoma gaban madubi wani man gashi yabude sanan yalukata yashafa akanshi kafin kaceme gashin su kara wani kanannadewa bakinsu na shinning kaman wani gashin jariri sanan yadau turarukanshi ya feffesa yadau yazura wani crock na maza yafito falon saman, wayanshi yadauka sanan yawuce yafice daga flat din, yana fita wani rana yadaki fuskanshi tsaki yayi yace “I hate this damn country” Babban flat din gidan yayi kofa yabude ahankali yashiga Sharif ne ke zaune afalo sai wasu yan mata guda uku Aneesa, Rahima, da Mariya duk suna zaune kusada Sharif din suna hira, suna ganinshi tsit kakeji wani irin batarai yayi kaman baitaba murmushi tunda yazo duniya yazo zai wuce tagaban su dasauri suka shiga gaidashi. “Ya Asad welcome ya hanya” da kyar ya iya bude baki ya amsa batare daya kallesu ba. “fine” that’s the only thing yafadi sanan yay dinning Sharif nabinshi da kallo saikuma ya kalli Aneesa data bishi da kallo kaman zata hadiyeshi.
Zama yayi kan kujera daidai lokacin Ammi tafito daga kitchen rikeda flask tana kallon fuskanshi tace “sannu da aiki superman mai shiga rijiya, yanzun nan nagama hadamaka tea dinan zokasha koya kori sanyin daya shiga jikinka” dan murmushi yamata daidai tamikomai cup din shayin dayaji kayan kamshi karba yayi itakuma taja kujera kusadashi tace “Ya hanya” ahankali yace “Ammi yaushe zamu koma gidanmu”? “to marason zumunci anan kano zaku cigaba da zama” dasauri yadago kanshi wata hadaddiyar mata ce kyakkyawan gaske tana sanye da bakin jallabiya kesaukowa, ahankali yace “ina yini Anty” hararan shi tayi sosai tace “kai yaron nan ina kanwar mahaifinka kana kirana da Anty, abinda kike koyamai kenan Maryama? Kaf family nan bamuda yaro mara tarbiya irin Asad” sanin halinta yasa Ammi tace “stand up and greet her properly Asad” kallon Ammi yayi yanda ta gyadamai idanu yasa yatashi ahankali yana kallon kasa yace “ina yini M…um” washebaki tayi takaraso inda yake hannunta takai kan fuskanshi tace “ko kaifa Asad, kadawo lpy” kanshi akasa yace “lpy” murmushi tayi tace “ance kadawo kayi aikin nanne na youth start up forum ko da government sukai establishing right?” gyadamata kai yayi batare daya kalleta ba, cikeda gamsuwa tace “awani tasha zakuyi Channels television news” murya chan kasa yace “kowani TV station zasusa har nagama na 7days” gyadamai kai tayi tace “Masha Allah, Allah yataimaka, saikuma batun aure ko” shiru yayi sakinshi tayi tace “anyway nadawo mayi maganan da kyau, let’s go girls” tashi matan sukayi suka bita suka fice.

Daure fuska yayi sosai yanajan cup din tea dinshi zaikai baki yace “saisa banason zuwa gidan nan I don’t like her Ammi, this Anty Turai” shareshi Ammi tayi tajuya takalli Sharif dakecin abincin shi tace “you want more Sharif” “Ammi am full” kallon Asad din tayi tace “mezakaci”? kallon abincin data bubbudemai yayi sanan idanunshi suka sauka kan spaghetti da meat balls da hannu yanuna mata zubamai tayi ya karba yashiga ci ahankali bin dan nata take da kallo take, anytime taganshi mahaifinshi kawai take gani halinshi sak dana ubanshi, juyowa tayi takalli Sharif tace “baku bani labarin ciro yarinyar dakukayi daga rijiya ba” kaman jira Sharif yake yace ” Ammi I was driving fa kawai wata mata tasha gabanmu tana kuka wai mutaimaketa yarinya tafada rijiya, Ammi I was begging Asad fa yaje mucirota wai bazaiyiba gashi ba maza sai tulin uban mata kaman gidan biki duk suna kuka, shine nace musu mujeni nacirota dan nasan that’s the only thing dazai fitoda Asad daga cikin motan nan danni kadai nasan irin mugun halinshi, aiko ina shiga saigashi yataho ashedai yana sona yasan ban iya ruwaba fear of my death yasa yazo bawaidan he meant to save the girl ba, shine yashiga fa yacirota, Ammi kinsan menene” yay maganan yanajan kujera da sauri yana zama sanan yakalli Ammi dake kallonshi yace “Ammi nifa dasuketa yarinya I thought small girl ce fa tafada rijiyan saigashi Asad yafito da zankadediyan budurwa innalillahi Ammi kinga kyanta kuwa” Ammi dake sauraronshi tace “haba” dasauri yakalli Asad dake cin abincin anatse yana danna waya yace “Asad isn’t the girl beautiful” batare daya kallesu ba yace “I don’t know bankalleta ba” wani mugun tsaki yaja yace “Ammi wlh Asad dan rainin wayau ne” dan dariya Ammi tayi ganin yanda Sharif ya tunzura sosai tace “don’t mind him kaji cigaba da bani labarin” murmushi yama Ammi yace “wlh Ammi tunda nake Allah Ammi harna gama yawona across the globe ni bantaba ganin kyakkyawa irin yarinyar nanba Ammi she don’t even look Nigerian, hala half cast ce, Ammi she’s so pretty gashinta har waist, she’s so pretty I wish I can even see her again” ture plate din abincin dayagama ci Asad yayi yamike Ammi dasauri ta kalleshi tace “harka koshi? Baka cinye ba ai” gyadamata kai yayi yace “ya isheni, natafi wajen Dadda” dasauri Sharif yatashi yace “wait for me Asad” ko kallonshi baiyiba yawuce Ammi tabisu da kallo tana murmushi, Sharif is such a gentle man with a very very forgiven spirit, shikuma Asad is opposite na hakan, churarren mutum ne baka gane gabanshi da bayanshi ko itama sabida ita tahaifeshi ne saisa take iya fahimtan halinshi tass,.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button