KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

ZAKI IYA MAGANA DANI DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK
wa.me/+2347012181461

WLH DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA, MASU KARATU SATA DUK BAN YAFEMUKU BA DUNIYA WA LAHIRA, AND INA BAKU SHAWARAN KIYAYAN HAKKIN MUTUM. THANK YOU

EPISODE 5️⃣2️⃣
Daga Sharif har Asad juyawa sukayi suka kalli gate din dasukaji anbude, hada idanu sukai da Aneesah dawasu yammata guda hudu, ganin Ya Asad da Ya Sharif dabata taba tunanin sune masu motan ba yasa jikin Aneesah yafara wani mahaukacin rawa sosai ganin Ya Asad da Ya Sharif akan Du’a datagani a kwance bata iya bude idanu da kyau ga jini yabata kafanta da hannun, ga jacket akan kirjinta, gawasu maza guda hudu datagani a sussume in various places, ga gorunan coke akasa wanda tasan da babusu, ahankali Sharif cikeda mamaki yace “Aneesah” sunanta da aka kira yasa Du’a tabude idanunta da kyar takalli gate din jin ankira Aneesah. “what are you doing here Aneesah who are this people”? kasa magana tayi sai rawa da bakinta yake tana kallon Ya Asad dako kai bai daga yakallesu tun bayan kallon farko daya musu najin anbude gate yacigaba da dressing din kafar Du’a abinshi, ganin yanda Aneesah tashiga trembling yasa ahankali da muryanta dabaya fita sosai cikin kuka ahankali tace “Ya Sharif nina kirata nace tazo” juyoda kai Sharif yayi yace “Ke kika kirata”? Gyadamai kai tayi ahankali, gama dressing din Asad yayi yakalli Sharif yace “I will go with the car zan kira akawo naka, call the police suzo su kwashi su” gyadamai kai Sharif yayi jikinshi yay sanyi dan no one needs to tell him Aneesah has something to do with all of this, idan Du’a ce takirata tayaya zatai locating this place dakoshi it took him time to track, badai son Asad yasa Aneesa did something as stupid as this ba.

Tashi Asad yayi yadauki Du’a ahankali kankameshi tayi tana kuka ahankali dan ko Yaya aka tabata zafi takeji, ahankali yake tafiyada ita dasauri Aneesah da kawayenta suka matsa gefe takasa kallon Ya Asad, shima ko kallon inda take baiyiba yawuce yafita, sata abayan mota yayi ahankali yana kallonta kwantar da ita yayi sanan yarufe motan yadawo gaba yashiga yaja motan, saida Sharif ya tabbatar da yatafi sanan yakira police kafin yatashi yataho inda Aneesah ke tsaye kanta akasa har lokacin jikinta yakasa daina rawa yace “tell me u have nothing to do with this Aneesah” kasa dagokai takalleshi ma tayi, yanda jikinta kerawa haka na kawayenta ma suka shiga rawa, Billy datafi kowa tsoro barinma dataji ankira police yasa tace “Aneesah Brother wallahi we don’t know this guys” kallonta Sharif yayi strictly yace “just tell me what happened” nan takoromai bayani tundaga kan plan din da sukayi a group na yanda zasuci uban Du’a, sanan takarashe da fizge wayan Zeezee tabude tanunama Sharif video da Zeezee tayi tana ihu tana kara tunzura Aneesah tana kiban Du’a kaman yarta tana kuka tace “wlh ko yatsunmu daya baitaba Du’a ba, Aneesah tai komi mu kawai yan rakiyane dakuma hyping” karban video yayi yana kallo kasama jure kallon video yayi yatura wayan aljihu yashiga dukan ta da kafa da hannu tana kuka sosai polisawan dasuka zone suka rikeshi sanan yabarta tafiya da guys din akayi sanan yasata a motan da Asad ya aikomai dashi suka wuce batare daya bada wayan Zeezee ba.

Awani private Asibiti ya tsaya yana parking yafito daga mota yashiga ciki ma’aikatan asibitin sai gaidashi suke, direct pharmacy dinsu yaje yan phamarcy na gaidashi abubuwa yadinga kwasa batare daya amsasu ba yacika wani babban leda sanan yafito mota yashiga yaja motan da mugun gudu, yana zuwa anguwan su direct gidan Hajiya yawuce ana budemai gate yaja motan ciki, sanan yafito tabude baya, Du’a da idanunta a kulle yakai hannunshi yataba jin jikinta yay sanyi yasa yay sauri yadauketa yakalli security yace “bring one big leather from the car” sanan yay cikin gidan da ita, sallama yayi yabude kofan, Grandma na zaune kan kujera ganin Du’a a hannun Asad da fuska yay subu subu ga kayanta yay datti jacket din Asad ne akan kirjinta kafanta jini kasan riganta dukya baci da jini yasa tawani mike tsaye arude tace “innalillahi wa innailaihi raji’un, maiya sami Du’a” sama yayi Grandma tabishi da sauri dakinta yabude yashiga kwantar da ita akan gado yayi, sallama sukaji daga kasa na Dad da Ammi dasauri Grandma data rude tafito ganin su Dad ne da Ammi, da Rahima, Mariya da Anty Turai yasa abin yabata mamaki, Dad da jikinshi yafi kowana rawa yace “what happen maiya sami Du’a Hajiya yanzun nan Sharif yakiramu yace dukanmu muzo gidanki something happen to Du’a shima yakusan karasowa tareda Aneesa” ahankali Hajiya tace “nima bansani ba yanzu Asad ya shigo da ita asume” dasauri sukai dakinta da Asad ke kokarin fixing mata drip, zaro idanu Mariya tayi tana salati aranta me Aneesah tama Du’a haka, cemata tayi magana fa kawai zata mata tabata tsoro what happened to her like this, tsayawa duk sukayi kowama yakasa magana ganin yanda Asad ke komi dasauri sauri, yana saka allurai a drip din, saida yagama tass sanan yadawo kafanta dasuka a yasha bandeji budewa yayi yana dressing duk suka tsaya suna kallonshi sanan yakama hannunta yamata alluran tetanus kafin yasa stethoscope yana kokarin dubata Sharif yay sallama yashigo yana rikeda hannun Aneesah da idanunta sukai jajir, ganin yanda suka cika dakin yasa Dad yace “duk kumu fito falo, Asad muna jiranka” fita duk sukayi harda Grandma suna kallon Asad zare stethoscope din yayi jin heartbeat nata yay stabilizing sanan yafito ahankali ya tsaya bakin kofan dakin yay folding hannunshi a kirji yana kallon Aneesah dake kuka idanunta akasa, ahankali Dad yace “Asad Sharif maiya sami Du’a? kuke tareda ita a office” ahankali Asad yace “she never came to the office yau, katambayeta what happen” yay maganan yana kallon Aneesah dakowa yajuya yana kallo, Anty Turai tace “ke what happen ake cewa atambayeki” hawaye tashare ahankali kanta nakasa tace “Mum inason Ya Asad ne” shiru kakeji adakin sanan ahankali tace “and Du’a is my best friend ita kadai nafadamawa shine ta auri Ya Asad, shine……” tashiga koro bayani tundaga kan yanda suka cireta a group harzuwa yau tace “Dad, Ammi, Mum wlh wlh bansan guys dinba bani nasasu ba, the plan was kawai muje muyi dambe taji tsoro tarabu da Ya Asad” ahankali Sharif yaciro wayan kawarta Zeezee yamikama Dad yace “Dad look” karba Dad yayi ranshi yay masifan baci, Du’a dayake so Aneesa ke jibga haka shida baya dukan yaranshi koda wasa baisan lokacin daya yarda wayan yawani jawo Aneesah yakifa mata mari ba yace “is this the way I train you Aneesah to be this wicked? All what our family knows is love not hatred Aneesah kinsan mekikayi kuwa eh inda kin kashe yarinyar nan dame zaki fadima iyayenta” Dad yakara kaimata mari zuciyanshi na tafarfasa dan abin yamai ciwo ainun, ganin zai sake kaimata mari yasa Grandma taja Aneesah taboye abayanta tace “agabana saikaita dukan yarinya bakada kunya ne, Aneesah yarinyace children now a days do crazy things for love eh, besides her intention was even childish all abinda take dashi aranta shine suyi fada kawai ayi dambe which is very very normal and okay, batayi agida bane sabida za’a raba fadan dawuri saisa takaita where she feels zasuyi fadan and settle everthing yisu yisu, please nobody should touch this girl again, Sharif Asad, no one should lay a finger akan Aneesah, haba jibi idanun yarinya” kankameta sosai Aneesha tayi tana kuka sosai tace “Hajiya I am so sorry wlh bazan karaba, wlh bazan karaba dan Allah kuyakuri” ganin yanda yarinyar ke kuka harwani ijiyan zuciya take yasa Anty Turai taji takai wuya dan marin da Dad yamata yamata ciwo matuka, hannun Aneesah taja tace “ke wuce muje tattara yinamu yinamu mubar musu gidan nan, sabida yana kula dake yana biya miki school fees a private university shine zai wulakanta ki haka” cikin wani azababben fushi dakowa yadade bakiga Dad dashi ba yace “wlh wlh Turai kikaja yarinyar nan kikabar wajen nan saina mugun saba miki karyan rashin kunya kike, fitsararra saisa babu namijin dake iya zaman aure dake” cikin fushi sosai jin cin fuskan da Dad yamata Turai tajuyo takalli yayan nata tanunamai dakin da Du’a take ciki tace “nikake gayama magana Yaya? Eh? condition din da yarinyar chan keciki yanzu y’ata ce tasata aciki? Ba ita bace and we all no that, abinda Aneesa tayi was silly abu da yara mata duka sun sabayi, duk maganan Du’a kuke no one is talking about Aneesah, bayan dukkunsan soyayyan danku wanan ja’irin yaro yasa taje tana fada da Du’a, ita maisa bazaka aura mata Asad dinba eh kabar gida kaje waje kana aurawa danka yarinyar dabatada gata agidan ubanta, wanan shi ake kira da bishiyan giginya yahana na gida inuwa yabama nawaje, sonkai kawai sanan dannai magana kake gayamin irin halin yasa nakasa zaman gidan miji” cikin fushi Dad yadaga hannu zai kwasama Turai mari dasauri Ammi tarike mai hannu tace “Alhaji calm down dan Allah children are here” cikin fushi Turai tace “barshi ya maren mana, I no blame him daman ance yarinyar mayya ce, so anything can happen gashinan daga aurama Asad ita gidanmu ya haukace, gidanmu that has been peaceful for years yarinya rana tsaka tashigo tana neman daburta komi, wlh bakuga komiba baku dai Allah yazuba muku kwashe kwashe ba kucigaba, yarinyar da agidansu neman kai akeda ita amman kuka jida” ahankali Ammi takama hannun Anty Turai ganin maganganunta are hurtful kuma ga Hajiya awajen tace “Anty Turai dan Allah kiyi shiru this whole thing baikai ga haka ba” tura Ammi tayi baya cikin bakar masifa tace “dalla munafuka kyaleni” baya Ammi tayi zata fadi dasauri Dad da Sharif suka tareta aiko Dad nadagowa baiyi wata wataba yadauketa da lafiyayyen mari zaikai mata na biyu sukaji muryan Du’a kaman daga sama cikin yar siririyan muryan nan nata tace “Baba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button