KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ahankali Abba dake kallonta yace “Du’a” sai alokacin tadago kanta takalleshi, hannu yamika mata, ahankali ta taso hannunta tasaka kan nashi zaunarda ita gefen kafanshi yayi yana kallon fuskanta yace “how are you Du’a? Ya shirye shirye”? Dan murmushi tayi tana kallon Abban nata ganin yau yamata magana faram faram ahankali tace “Alhamdulillah Abba” hannunshi yakai ahankali yadaura asaman kanta yace “Allah yamiki albarka, Allah yakaimu jibi lpy akaiki dakinki, Allah ya sanyama aurenki albarka” ahankali tace “Ameen Abba” wani irin murmushi Grandma tayi sometimrs rashin wayon Du’a pays her alot, kannin Abba dake kusada ita addu’a suka mata sanan babban cikinsu maibin Abba yace “saiki sanar da mijin naki iyayenki sunzo yazo yagaidamu anjima da daddare, yaga yan uwanki muna muganshi musan wanda muka bama yarmu, ayi zumunci” gyadamai kai tayi, sanan Abba yatashi yace “kutashi mutafi masallaci” tashi mazan Saukayi harda Hamad suka fice dan zuwa mosque.

6️⃣0️⃣

MASU FITAR DA NOVEL DINAN WAJE KUNMA KANKU MARASA AMANA.

PAY 500 INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK SAIKI TUROMIN EVIDENCE OF PAYMENT TA WATSAPP NUMBER NA 07012181461 SAINAI ADDING NAKI A GROUP DIN DANAKE POSTING.

CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK
wa.me/+2347012181461

Kaka data kasa daina kallon Du’a ne tace “taho nan naganki yarinyar nan” ahankali Du’a tadago kanta Grandma takalla danko kadan jininta bai hadu dana kakarta ba, gyadamata kai Grandma tayi alamun taje hakan yasa ahankali tamike tsaye taje wajenta ahankali tazauna akasa, hanci Kaka taja agaban kowa jin wani hadadden kamshi da Du’a keyi tace “banda kyau har kamshin fata Allah yabaki ne, lallai nidai Allah ma yasani haryau nakasa yarda ke diyar Muhammadu ce billahillazi” Kaka tai maganan tana kama hannun nata tarike sanan tace “Ya sunan mijin naki” ahankali murya chan kasa tace “Asad” gyadakai Kaka tayi tace “tabbas haka Muhammad Muhammadu ko yafadi mini, dana aiko adaukoki akawomin ke chan Ikara ki zauna dani shine kikace ke aure kikeso, shikuma dayake uban naku wani zubin bakai gareshi ba sai ko ya aurar dake, ai shikenan tunda auren kika zaba, nidai addu’ata Allah yasa karya gano kinada jinin ifiritu ajikinki yasakoki tunda mun samu kin sami miji kin aure” daidai nan Grandma tace “kinga Kaka jikata batada jinin ifiritu jinin danki gareta, kumama bakisan wani abuba, Kakan Babana usulin shi balaraben Egypt ne, yazo naijeriya yay aure, to daganan ne abin yatafi muka duk aka haifomu bakake sabida matayen dasuka aura, Du’a tadauko jinin dangin ne na kakanni” baki Kaka tabude ganin Grandma na taran mata numfashi idan tana magana hakan yasa tahadiye sauran maganan tace “asheee” murmushi Grandma tayi tace “eh wlh, yanzu dai kugamacin abinci ayi salla saimu tafi sama kuga akwati” takalli Mom daketa kallon Du’a dake wasa da yatsunta tace “akwai wani abu dakike bukata akawo miki Maman Hamad” murmushin yake Mom tayi tace “a’a wlh” lafiyayyen abinci aka kawo musu daban daban ga namomi zuku zuku, bawai basacin abinci agidansu bane amman kaga wani abincin sai agidan wane da wane ga gasasshiyar rago, dayan flat din da Grandma tasa aka gyarama su Abba suna dawowa wajen aka kaisu dan su saki sanan aka kaimusu nasu abincin, zuzzuba abincin akayi sanan Grandma takalli Du’a tace “oya tashi kici abinci tareda yan uwanki” tanuna mata su Hawwa dasuka zubo abincin su a plate tare, gyadamata kai tayi tai wajen atsakiyansu tazauna ahankali sanan takalli Nana dake kallonta ahankali tace “Ya Nana” dan murmushi tamata tace “Du’a ya kike”? murmushi tayi tace “lpy lau” sanan takalli Hawwa dake kallonta tace “Ya Hawwa” murmushi taga Hawwa tamata tace “Amarya Du’a” dan murmushi tayi sanan tadau spoon dinta sukahau cin abincin bini bini Mami na satan kallon Du’a da tuni Grandma ta lurada ita kuma tasan bakomi take kallo ba illa girma dakuma kyau da Du’a takara, saida sukaci suka koshi sanan Du’a takallesu tace “kutashi muje dakina kuyi wanka ku shirya” basuyi musu ba suka bita sukai sama duk aka bisu da kallo, akwatinan dasuka gani afalon sama sukabi da kallo kusan set 15, sanan suka shiga dakinta shima kallon dakin suka shiga yi, skirt Hawwa tacire tai bayi dagudu tace “zanyi fitsari wayyo karya zubo” murmushi Du’a tayi sanan takoma kan gadonta tazauna, ahankali taga Nana tazo tazauna kusada ita hakan yasa tadan dago kanta ta kalleta hada idanu sukayi, murmushi Du’a takarayi tasaukar da kanta kasa, ahankali Nana takira sunanta.”Du’a” dasauri tadago kanta takalleta, hannun Du’a Nana takama tace “nadade ina neman hanyan dazan kiraki nabaki hakuri, I am very sorry Du’a akan duk abubuwan danamiki akan Muhsin, Muhsin is nothing but a jerk nima daga baya nagane haka, bake kadai yabi ba, infact namaji dadi abinda yafaru badadan keba da yanzu na aureshi ina cikin bakin ciki, kece sanadin dayasa Nagano wayeshi, ashe duka friends dina na school daya sani duk yana dating nasu, mayen mata ne na karshe kuma dan iska, I was so blind by his love bangane hakan ba, kiyakuri kinji Du’a” Gyadamata kai Du’a tayi ahankali tana murmushi, Nana tace “bayan Ya Hamad yadawo daga kawoki Abuja yafadima Abba komi, saiya yakulle Uwani, Mai gadi dashi Muhsin din a police station, akayi case sosai sanan aka bashi hakuri yasakesu da sharadin ko akofar gidanshi yasake ganin any one of them hukuma zasu raba shi dasu ahaka case din yakare” gyadamata kai Du’a tayi daidai Hawwa tafito, tashi Nana tayi tashiga bathroom din, Hawwa takalli Du’a tace “kin kara kyau yarinyar nan, yaushe rabon damuyi fada” dan murmushi Du’a tayi tana mamakin yanda duk suka chanza toko sun kara hankali ne oho, salla sukayi sukahau bama Du’a labarin kano daga tai murmushi saita gyadamusu kai, kwala musu kira da Mom tayi yasa suka fita banda Du’a datai zamanta, duk afalon saman suka taru ana bude kayan Du’a dababu na Nigeria ko daya, daga akwatin har atampopin dakomi ma, Mom duk yanda taso kasa boye bakin cikinta tayi, harsaida Kaka yar bala’i tace “kekuma kowa na tofa addu’a bazaki tofa ba” murmushin yake Mom tayi dan daga ganin akwatin wani mai kudin Abuja Du’a zata aura, itada ta dauka wani mai gadi ne kokuma lebura haka zata aura, amman wanan akwatuna haka set 15, kowani saiti nada 3 dan designers akwati ne ba irin na Nigeria ba, ahankali tace “Kaka yarinya tai goshi Allah sanya alheri” da karfi Grandma tace “Ameen” sanan tanuna ma kowa dakinshi asaman dan suje suyi wanka su huta, kowa yatafi, su Hawwa suka koma dakin Du’a duk suna mamakin akwatin Du’a dan basu saba ganin irinshi a kano ba.

Dakin Grandma Mami ta shiga, waje tasamu kusada Grandma tace “Mama Yaya Muhammad yace jibi zasu shigo ko ranan jumma’a” murmushi Grandma tamata tace “ashe kunyi waya haka yagayamin” shiru Mami tayi tana kallon mahaifiyar nata tasan har yanzu fushi takeda ita, ahankali tace “Mama dan Allah kiyakuri kiyafemin komi dan Allah” juyowa Grandma tayi takalleta kaman tai shiru saikuma tace “naso namiki yanda kikama Du’a yarki ne, nima na nuna miki baki da amfani kaman yanda kika nunama yarki, but I guess bazan iyaba Zainab” sauka Mami tayi daga kan gadon, guiwanta tasauke akasa tana kallon mahaifiyar tata, ahankali tace “dan Allah kiyakuri kiyafeni” hannu Grandma tasa tadagata dan tanason yarta bakadan ba, zaubarda ita kusada ita tayi tace “Na yafemiki komi ya riga yawuce Du’a tariga tai aurenta, ranan lahadi war haka ai tanama gidan mijinta so bakomi, yanzu dai akwai magungunan ta wajen Jummai, kinsan zan shiga hayaniya ba lallai nasa idoba kisamata ido makesure tashanye komi sanan taci abinci dan bata iyacin abinci har yanzu, akwai turaruka ma anan zaku dinga mata” gyadama Grandma kai tayi tace “to Mama” ahankali Grandma tace “kinga yaron daya wahala shi Allah yake kyautatamawa akarshen sabida ya wahala yay hakuri, Allah yabama Du’a miji, idan kinga yanda yaron kesonta dudda yana kokarin boyewa sai kinyi mamaki, ko bani duniya ayau Zainab na yarda da Asad zai kulada Du’a kaman kanwarshi wanan shaidar nimishi ita” murmushi Mami tayi hankalinta nakara kwanciya tace “Alhamdulillah”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button