KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ahankali yatura kofa yashiga dakinsu tsaye yaga Sharif yakafa goran ruwan sanyi abaki yanasha kaman wanda yaje yaki, dan tabe baki yayi yawuce stairs abinshi, binshida kallo Sharif yayi kawai yacire goran ruwan daga bakinshi ya jefar ruwan yazuba atsakar dakinsu wani irin kifa kanshi yayi a fridge din yana kokarin daidaita heartbeat dinshi yace “Ammi why? Why? Eh” ahankali yazauna a kasan bango yakifa kanshi yana magana shi kadai ahankali. “nasan ni kika fara nema rashin ganina yasa kikai reaching out to Asad for the help, Ammi maisa baki kirani awaya ba? Don’t u know that Asad is bad choice ma Du’a haaa? He will maltreat the poor gurl and make her suffer, Asad baya sonta” wani hawaye mai zafi ne suka zubomai dasauri yashare ahankali yace “but Dad yace ita dakanta tace tanason Asad, Du’a how could u love Asad mutumin da all abinda zaiyi shine ya wulakanta ki and make u cry all the time” ajiyan zuciya yasauke yace “I’ve been so good to you starting from the first day dana fara ganinki aduniya, ta dalilina kike araye yau, I forced Asad to save u a rijiya, I’ve been very generous good and romantic towards u but all this baki ganiba kikaje kinason wanda bai damu dakeba daidai da zarra daya, maisa mata sunfison mazan that makes them cry always mazan dake wahalar dasu eh”? Wani irin fashewa da kuka yayi mara sauti awajen yana taushe bakinshi he is deeply hurt, like deeply, part din da Du’a ne tai proposing komi shiyafi cimai zuciya, ko kadan baya ganin laifin Asad dan yasan tursasashi akayi.

Asanyaye Asad yamaida kofan dakinshi yarufe tareda jingina da kofan yana lumshe ido dan he could hear sautin kukan Sharif dan dakin komi akashe yake ba’a kunna AC ko TV so so zakaji sound na komi very well, ahankali yazauna akasa gaban kofan still idanunshi a lumshe, he really care about his brother yanason Sharif sosai he hates seeing him hurt, ahankali yace “I am so sorry Sharif, I am sorry”.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

       ✍️M SHAKUR 

EPISODE 4️⃣6️⃣
Wani irin lafiyayyen bacci tayi da kyar ta tashi shima sabida Grandma data tadata ne tawuce tafice ahankali ta tashi zaune da kyar tana hamma, sanan tasauko da kafafunta tamike tsaye daga gado jin tsamin da kafafun nata sukayi jiya duksun bace yasa taji wani dadi tawuce ta tafi bayi, brush tashigayi saikuma tadago kanta ahankali ta kalli kanta ta cikin madubi tace “ke matan aure ne yanzu fa Du’a” wani irin kawarda maganan tayida sauri dan daga ita sai Asad sukasan komi tasan wanan ba aure bane besides ma ita ai taroki Ya Asad to save her gashi kuma hakan dayayi really saved her dan bagashi Abba da Mamin ta duk sunzo sunkoma ba’a tafida ita ba, so all this ba aure bane, ina zamata iya auran Ya Asad dinan mugu, zata sami mijinta mai kirki kaman irinsu Ya Hamad dasu Ya Sharif suyi aure abinsu, karasa brush din tayi tana wani irin murmushi dan harga Allah murna sosai take ta tsani kano sosai rashin tafiya da ita ba karamin dadi yamata bata ganin anything sama da hakan, alwala tadauro sanan tafito tai salla tana idarwa ta zauna tana biya karatun da malaminta yamata sanan tazo tai assignment din daya bata duka tamaida books din jaka sanan ta tashi, fitowa tayi tana tafiya ahankali tasauka kasa dan yunwa takeji sosai, Grandma tagani zaune a falo tanajan charbi ganinta yasa dasauri ta tsinke charbin datakeja tace “ke yau zakije aiki ankawo komi naki jiya kinyi bacci, wuce kije kiyi wanka kiga” turo baki tayi dan bataso tajeba takoma sama, wanka tashiga, koda tafito saitaga anfito mata da kayan dazata saka, wani baki da golden abaya ne mai mahaukacin kyau tagani akan gadonta, dasauri tai wajen abayan tana dagawa tace “wow yaushe Grandma tasaimin wanan” ijiye rigan tayi sanan takoma gaban mirror tadauki mai ta shafa sanan ta fesa bodyspray sanan tadauki rigan ta shirya tsaf cikinshi tana kallon kalaban kanta da duk suka soma warwarewa da kansu dan haka gashinta yake yatsine fuska tayi tadauki ribbon takullesu sanan tawuce tafito kasa zuwa dinning zama tayi Razika tafito daga dakinsu tana mata murmushi tace “mezan zuba miki?” Irish tafadi tana kallon soyayyan Irish din, zuba mata Razika tayi sanan tamiko maka karba Du’a tayi tace “thanks” sanan tadau fork tafaraci, dagakai Razika tayi takalli Grandma ganin lazimi take abinta yasa Razika tazagayo taja kujeran kusada Du’a tazauna tana kallonta tana murmushi tace “sannu Amarya ke kodan kunyan nan da kawaici na amare bakiyi” kallonta Du’a tayi kaman wacce batagane me ake fadiba tace “wacece amarya”? hararanta Razika tayi tace “kece mana jiya duk munje mun gama raba cingum da sweet, Allah Du’a namiki murna sosai Asad dinan yahadu wlh gashi baya wasa da mutane baya murmushi, u are very lucky dakika aureshi” kallonta Du’a take da ace tasan wanan ba aure bane daduk batai maganganu hakaba, gyadakai kawai tayi tadauki cokali tacigaba da cin Irish dinta sanan tadau tea kurba daya tayi kawai ta tashi zata wuce Dasauri Razika tace “wai har kinci abinci kenan Du’a “? gyadamata kai Du’a tayi alamun eh, dasauri Razika tace “Irish din dakikaci banjin su kai guda 10 bafa wai mesa bakison abinci ne Ulcer sai kamaki fa” cunno mata baki Du’a tayi tawani juya tai sama Razika tabude baki ganin wani tsiwa ma takeji da safen nan, shafa lazimin da Grandma takeyi tayi takalli Razika tace “ai Du’a sai dai Allah yatarota karki biye mata sami kula mai kyau ki zuba mata abinci tatafi office din dashi danni ban yarda Ulcer yakamata ba ba gaira ba dalili atoh” murmushi Razika tayi taje kitchen tadauko wani karamin kula mai kyau ta zubamata chips din da plantain tasan yanda takeson nama hakan yasa tazuba mata soyayyen naman kasa ciki, daidai nan tasauko tana duba jakanta taga kotasaka komi Tao rolling gyale dudda babu komi akan fuskanta amman tai bala’in kyau, ganinta yasa Grandma tabita da kallo murmushi tayi tace “kawo kulan nan kiga Razika” karasowa tayi rikeda kulan tana kallon Du’a data tsaya atsakiyan falo tana kallonsu, karba Grandma tayi tamikama Du’a hannu tace “bani jakan nan” turobaki tayi tace “akwai wajen cin abinci fa a office so kike acemin yarinya zan wani tafi da abinci” hararanta Grandma tayi tanasa kulan ajaka tace “dabakison kijeda abincin da kinci da kyau, zo ga national ID card dinki yafito gakuma account number ki nan rubuce akan paper nan ga ATM card dinki” zama tayi kusada Grandma tana duba komi tana murmushi sanan takalli ATM CARD din daga sunanta ajiki tai wani irin murmushi tace “nima yanzu inada katin cire kudi” tabe baki Grandma tayi tana kallon agogo takwas saura tace “wlh Du’a kikai latti mijinki Asad daidai yake dake” dasauri takalli Grandma jinta kirashi da mijinta wani bambaran abin yamata tashi tayi tana zuba komi ajaka sanan tarataya jakan tace “natafi Grandma, Razika bye” tama Razika dake kallonta waving hannu dan Du’a tamata mugun kyau kodan andaura mata aure jiya ne oho amman yau taiwani irin special kyau kaman wata Amarya.

Motan Grandma tashiga bayan tagaida direban dake tsaye gaban mota, shiga yayi yajasu bini bini yana kallonta ta glass din motar dan arayuwa baya gajiya da kallo jikan Hajiya nan mai kama da balarabiya, shigowa kampanin sukayi yay parking a parking space ya kashe motan fitowa daga motan tayi ahankali sanan tasa hannu tadauki jakanta dakekan kujera sanan takalleshi tace “thank you Uncle” sanan tamaida kofan tarufe tajuya tana tafiya ahankali tana kalle kalle, sanan takai gaban entrance tashiga, tana shiga receptionist din wajen dake kokarin kwasan wasu files jikinta narawa takalli Du’a tace “why are u late Miss Du’a? Anyway there’s no time for that kiyi sauri sauri kije hall a 2nd floor, Mr Asad is having a meeting with all staff duk ana wajen hurry” yanda tai maganan jikinta narawa tana parking wasu files yasa dasauri itama Du’a tajuya tai bene Receptionist din tabita da kallo, second floor din takai babuko kowa awajen alamun duk ana meeting ganin wani babban kofa guda biyu haka da aka rubuta hall ajiki yasa tai wajen, ahankali ta tura kofan ganin ko gezau baiyiba yasa tasa duka karfinta tawani irin tura kofan kofan yawani irin budu doors din sukai slamp din bango jikake bam ba dayasa kowa naciki yajuyo yana kallon kofan harda Asad dake magana agaba tashiga ciki tana sauke ijiyan zuciya, Babban Hall ne sosai kaman irin na school dinan kowa na wajen harda security, na gate kawaine basa wajen, ga Asad dake sanye dawani dark blue suit yay azababben kyau ya gyara gashin shi tsaye agaban hall din gaban wani speaker haka dake kan mumbarin yana bada speach sai Sharif dake sanye da suit mai ruwan toka zaune kan wani hadadden chair agaban hall dinma da MacBook akan table dinshi da byro alamun ana aiki ne shima, shigowanta da yanda ta bude kofan yasa yadago yana kallonta, wani kalan rawa jikinta yayi hakan yasa bakinta nadan rawa sosai tabude baki cikin yar zazzakan muryanta tace “Sor…..ry” tai maganan tana saukarda kanta kasa first kujeran dake right side dinta taja tazauna hakan yasa kowa yamaida kanshi yajuya, ahankali Asad yadaga hannunshi fuskanshi babu alamun wasa ko kadan, agogon hannunshi yakalla tara saura kwata hakan yasa yasauke hannunshi bakinshi na saitin speaker yace “Miss Du’a” dawani irin sauri Du’a tadago kanta jin sunanta a speaker da hall din ya amsa tashi tayi dasauri kirjinta na dukan uku uku takalli Asad din dake kallonta fuskarnan ba rahama yace “u are late and in my meeting I don’t welcome late comers, excuse us” yay maganan strictly, gyadamai kai tayi tasan menene excuse but batagane kalan excuse din dayake nufi ba anan, ahankali takoma tazauna tana tunani kaman daga sama taji tsawanshi. “I said leave this hall or are u deaf” wani irin firgita tayi batasan lokacin data zabura taja jakanta jikinta na rawaba kanta akasa sabida yanda ake kallon ko kadan bata lurada receptionist data shigo da lots of files da Asad requested for ba, wani irin karo taji taci da mutum tai baya kan kaceme receptionist da dama files din sun mata yawa a hannu hill din kafanta ya turgude tayo gaba kafin tafado files din suka fara zubowa kan Du’a da already tazube akasa, ihunta ma kasa fitowa yayi sabida files din dake kan fuskanta saiga receptionist da itama tafado kanta, dawani irin sauri receptionist din ta tashi jikinta narawa tace “oh my God, oh my God I am so sorry” tai maganan tana kwashe files din dake kan jikin Du’a, ahankali tadaga hannunta tasa hannun ta ture files din idanunta har sunyi ja ga hawaye, ijiye files din reception din tayi takai hannunta kan fuskar Du’a tace “oh my God I am so sorry, are u hurt? Stop crying” ahankali Du’a ta lallaba ta tashi tana share fuskanta da duk kiran files din kekai, sanan tawuce tafita batare data juyoba, 5th floor dinsu tawuce taje bathroom dinsu wanke fuskanta tayi tass sanan ta wanke hannunta ta kakkabe jikinta tana turo baki, kaman tawuce ta tafi gida amman tunawa da maganan Grandma da inyacee get out bawai koranki yayi ba kuma karta sake irin abu da tayi last time yasa ahankali tabude kofan bayin tafito sanan tawuce office dinta, ahankali tabude office din tashiga zama tayi ahankali tana kuyi akan kujeranta saikuma tai murmushi tanason dan office dinan, wayanta taciro tana kallo rabonda tashiga watsapp kotama kunna data harta manta tun kafin birthday din Aneesa dan ita wayan da chatting dinma bawai ya dadata da kasa bane dan bamata sababa daman Grandma ce ma ke kiranta wani zubin yan gidansu babu mai kiranta ko Mami bata kiranta saikuma su Aneesah wanda su yawanci chatting ne, ahankali ta kunna data, ajiye wayan tayi tadauki kukan da Razika tasamata abinci budewa tayi ganin nama asama zako zako yasa tai wani irin murmushi tadau guda daya takai baki sanan tadau wayanta da dayan hannun ta shiga watsapp ganin messages dinta na shigowa, tana shiga taga messages din duka daga groups dinsu na yammata ne wanda su Aneesah suka sata, daman shi kadaine group din datake ciki, dasaurinta ta danna ta shiga group din the first abu datagani shine Aneesah removed you, dan zaro ido tayi tace mistake ne, sanan idanunta suka sauka kan message din Mariya tasa announcement group Du’a is no longer our friend in fact she’s even an enemy, dan dariya Du’a tayi dan she always known Mariya to be a bit wild and Crazy, Rahima da Aneesah sunfi sweet da kirki da iyamagana, tacigaba da karanta messages din tanacin namanta, wata daga cikin kawayen su tace “Du’a Du’a wanan kyakkyawan yarinyar damuka gani a birthday dinku dako kallonmu batayiba, metayi muku?” taga yan group din nata fitowa suna tambayan meta musu, Mariya ce tasake fitowa tai reply da “she’s a snitch, a hypocrite, and very cruel, kunsan yanda mukeson yarinyar nan kuwa? We share all our things da ita, har saka yayyanmu muke yabata kudi muje shopping da ita shine zataci amanan mu” wanan karan dan fadi gaban Du’a yayi dan she understood this is not more a joke, yan group din sai tambaya suke metayi metayi, saiga Aneesah tafito tace “she stole my boyfriend tama aureshi dazu aka daura musu aure, bayan tasan ina sonshi he mean the world to me this girl knows everything about me shine zataje tabi tabayana ta yaudaran, wlh wlh bazan taba yafemata ba duniya walahira, Allah saiya sakamin yar iskan yarinya Aljanna kawai mayya, barima nabaku labari daga ubanta har uwarta duka nadaman haihuwanta suke basa sonta anma kawota nan Abuja wajen kaman just to save her ass ne, yarinyar that has been bad luck and wahala to her parents uban waye bazata tababama, shegiya mai bakin jini, asararra aljanna kawai” dawani irin gudu tafito daga group din takasa karanta sauran messages din kuka tafara ahankali zaginda Mariya tamata baima bata haushiba na Aneesah ne yamata ciwo harda kawo maganan gidansu, ahankali tasake daukan wayan tana share hawayen da hannun riganta ganin not just group tanada individual messages from different numbers da duk batadasu yasa ahankali tabude na first one wanda shi dasafen nan yashigo. “This is Vee Aneesah’s friend, you this bastard girl how dare you kikamata snatching boyfriend eh, wayeke ke yar gidan waye keda ubanki of all people HOD ne, kinsan waye uban Aneesah kinga gidan masu kudi shine kike neman space, bakisan ba’a ma yammatan Nile snatching boyfriend ba, wlh wlh kin shiga uku watch out for your self, mayya kawai mai kamada aljanu duk maitanki kanki kawai zaki iyaci munfi karfinki munbaki 2days kirabu da Asad inba hakaba wlh saimun kasheki” wanan karan sakin wayanta tai akan table ta tashi dagakan kujeran takoma gefe tana kuka ahankali, bude kofanta da akayi yasa tadago kanta dasauri, hada ido tayi da Asad dake kallonta dawani irin sauri tasa bayan hannunta tana share fuskanta lips dinta har rawa suke tace “good morning Sir” dauke idanunshi yayi daga kanta yabi office din da kallo kafin idanunshi yasauka kan table dinta da jaka kekai ga kula abude na abinci, ga naman da aka faraci akan table ga wayanta da screen din ke haske sosai karan messages na shigowa nata shigowa wayan, ganin ya tsare wayanta da kallo yasa dagudu tai table din tasa hannu ta dauki wayan taboye abayanta tanajan hanci trying to stop the kuka kanta akasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button