KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Hada kayan suka shigayi suna jera jakunkunan anan falon, tashi Aneesa tayi dasauri tana kama cikinta tana yatsine fuska dasauri Du’a tace “menene” hanyar stairs tayi tace “continue ina zuwa lemme use the bayi, cikina na juyawa I guess I am too excited ne” dan dariya Du’a tayi batace komiba tacigaba da abinda takeyi ahankali aka bude kofan falon dawani irin sauri tadago kanta, hada ido tayi da Asad dake sanye dawani dark blue 3quater da farin t-shirt yana wani irin zuba uban kamshi fuskanshi yadan kumbura alamun baidade da tashi daga bacci ba, wani irin faduwa gabanta yayi dawani irin sauri tadauke kanta tana saukar da kanta kasa, gyara zaman kafanta tayi takai hannunta tanajan skirt dinta yarufe mata kafa duka dan yadan tattaro zuwa wajajen gwuiwanta sabida yanayin zaman datayi da jakan datake ijiyewa in between legs dinta tana saka souvenirs din aciki, wani irin ijiyan zuciya tasauke feeling so uncomfortable sabida yanayin kayan datasaka, ahankali taja jakan daga tsakiyan kafanta tadaura kan cinyanta sabida yadan rufe boobs dinta dasukai girma ta farin t-shirt din sanan kana hango shape da komi na bra jikinta sabida very light expensive t-shirt ne, jin shiru bataji sahun tafiyanta ba yasa tadan dago kanta kaman munafuka tana kalle kalle, a dinning din falon taganshi tsaye yadaga flask yana zuba ruwan zafi a mug yana kokarin hada coffee, batasan mesaba amman kasa daina kallonshi tayi shigan dayayi yamata kyau saiyay kaman wani dan gayu, juyowa yayi dawani irin sauri tadauke kanta kirjinta na dukan uku uku, daukan mug din yayi yazo cikin falon kujeran dake facing nata yazauna akai tareda mika hannu yadauki remote yakunna TV yasaka a tashan ball sanan yayi sanan ya ijiye remote din yay crossing legs dinshi yakai mug din bakinshi yayi sipping coffee ahankali yana kallon TV.

Kasa cigaba da abinda takeyi tayi, gabaki daya jitayi she’s so uncomfortable, sai gyara nan da nan da nan take na kayan jikinta, daidai nan Aneesah tasauko kasa ganin Ya Asad yasa ta ware idanunta tace “laaaa Ya Asad daman bakaje office ba” ko kallonta baiyiba haka yasa tawuce kusada Du’a zata zauna yace “make me some omelet ki kawomin part dina” dasauri takalleshi cikin wani irin jin dadi jin yakulata tace “tom Ya Asad” sanan tawuce kitchen, tashi shima yayi rikeda mug din yawuce yafita daga falon, wani irin ijiyan zuciya tasauke tacigaba da aikin har lokacin takasa dainajin kamshin dayakeyi.

Kusan 10min Aneesa tadauka a kitchen tana hadamai lafiyayyen Omelet sanan tafito rikeda hadadden tray data daura plate din Omelet din akai, daidai lokacin aka bude kofan falo wata hadaddiyan faran mata tashigo tana sanyeda Abaya tanama Aneesa murmushi, wani irin tsalle da ihu Aneesa keso tayi tunawa da abincin waye ke hannunta yasa ta ijiye kan hannun kujera dasauri sanan tawani kwasa da gudu tafada jikin matan saikuma kuka. “Oyoyooo Mum, bakincemin gobe zakizo ba” kankameta matan tayi tace “I wanted to suprise my birthday girl” tai maganan tana kallon Du’a dake kallonsu tana murmushi dan taga kamanninsu da matan hakan yasa tagane itace Maman Aneesa, sakin Maman nata tayi tajuyo takalli Du’a tace “Mum kinga best friend dina sunanta Du’a” wani irin kallo Turai tabi Du’a dashi, ahankali Du’a tace “ina yini” lafiya ta amsa sanan takama hannun Aneesa tace “muje sama” juyowa Aneesa tayi takalli Du’a tace “Du’a please tayani kaima Ya Asad Omelet dinshi yanzu karyamin fata, kina fita flat dinsu ne a gefen namu kinji please, baiyi breakfast ba” gyadamata kai Du’a tayi ahankali tana kallon yanda sukebinstairs Mum dinta namata magana, harsunkai karshen stairs Aneesa takara juyowa tace “Du’a hurry karya huce bazaici ba” tashi tayi jikinta har bar bar yake tadauki tray data ijiye kan kujera sanan tawuce tafita hakan yasa Aneesa sukai ciki, flat din datagani kusada nasu tayi, ahankali ta tsaya gaban kofan tama rasa mezatayi she’s so nervous hakanan, door bell datagani ta danna ahankali, daga taciki taji ance come in.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

      ✍️ M SHAKUR 

EPISODE 3️⃣7️⃣
Takai kusan 1min tsaye takasa tura kofan tashiga dakin kuma ba’a kara cewa komiba daga ciki ba, kaman ta ijiye abincin anan gaban dakin takeji amman kuma bai daceba dan Aneesa bamata rufe plate na Omelet dinba, daurewa tayi ta mugun daure sanan ta tura kofan ahankali tasakanta ciki, wani irin sanyi da kamshi ne yamata sallama danya Kure AC dakin yana zaune kan kujera ga mug din coffee dinshi agefe saikuma MacBook kan jikinshi yana danne danne, ganin ko dago kanshi baiyiba balle ya kalli kofan yasa tashigo cikin dakin gabaki daya tamaida kofan tarufe takaraso ciki kafanta na harhardewa kaman zata fadi gawani kalan kunya datakeji sabida yanda babu dogon riga ko hijab ajikinta, dan karamin table din dake gabanshi da mug din tea kekai ta kalla dan dagakai tayi takalleshi batare data kara so wajen ba, lips dinta tadan lasa jin yawani irin bushe kafin ahankali cikin yar muryan nan nata tace “unnnn, Aneesa tace nakawo maka unnn….wanan” tadaga tray tana nunamai kaman yana kallonta, dan table din gabanshi yanuna mata batare daya kalleta ba yana aiki akan system dinshi, dan ajiyan zuciya tasauke sanan tashiga takawo ahankali takaraso gabanshi ahankali tadaura tray akan table din ta tashi dasauri zata wuce batare daya kalleta ba kawai yasamata kafa jikake tipppp tai wani irin mugun faduwa danma Allah yataimaketa akan rug ne inda a tiles ne da halan saita karye amman dudda haka ta bugu barinma kirjinta dan akife tafadi, wani irin malalacin kara tasaki na wahala. “wayyooo Allah na Mamiii na mutu” sai kuka ahankali tasakeshi tana kokarin tashi, ahankali yadauke system dinshi daga kan jikinshi ya ijiye agefe sanan yajuyo da kanshi ya kalleta daidai ta tashi zaune da kyar tana goge hawayen kan fuskanta hulan kanta shima yacire yay chan gaba, hada ido sukayi wani mugun kallo yamata yace “that’s for not greeting me, duk randa kika kara ganina kina bina da wayanan idanun naki batare dakin gashiniba saina miki wanda yafi wanan” gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawayen dasuka kasa daina zubomata, da kyar saida ta dafa kujera sanan ta iya samu ta mike tsaye hakan yasa kalban kanta suka wani zubo har waist dinta, hawaye tasake sharewa sanan ta tsugunna tadauki hulanta sakawa tayi tagoge fuskanta tass sanan tawuce tai kofa harta bude kaman daga sama taji yace “feel free kigayama Ammi ko Hajiya, zakiga abinda zan miki stupid girl” dasauri tafita daga dakin tamaida kofan tarufe, anan bakin kofansu ta tsugunna saida tasha kuka sanan ta share fuskanta tass tarasa maisa ya tsaneta haka, all she ever did was trying to tell him thank you kan abinda yamata, saida tagama tass sanan ta tashi ahankali tasauko tana tafiya akasa, hango pampon wajen flowers din gidan datayi yasa taje wajen, ahankali ta tsugunna tabude pampon ta tara ruwa ahannunta tana wanke fuskanta sanan tazare hulanta tasa akan kafanta ta tattare gashinta ta tufke dan batason sakin gashi sanan tamaida hulan tamike tsaye tajuyo, hada ido sukayi dashi yafito yana tsaye gaban dakinsu rikeda waya a kunne yanayi dawani irin sauri tadauke kanta kaman tada dodo sanan tawuce main flat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button