KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

8️⃣0️⃣

Murmushi Grandma tasakeyi tace “amman Asad idan banci kaniyan kaba bazanji dadi ba, jikata kama wayau ka aure cikin sauki haka” sanan takalli Du’a dake kallonta kaman TV tace “ke mace ce Du’a lokaci yayi dazaki fara daukan kanki da some daraja and mahimmanci, show Asad he treated u wrongly, show him ke mace ce, and make him bow before you, beg u, and tell u how much u mean to him kinajina” gyadama Grandma kai tayi, Grandma tace “karki sake kiji tsoro Asad na sonki kaman ranshi bazai taba iya miki komi ba, babu abinda zai iya miki koda yataso ki tsaye ki kalleshi a idanu kibashi words dazaiji a kwanyan shi zai San yes hannun agogo fa yajuya dayan kwanan” gyadama Grandma kai tayi ahankali cikin tone na kuka tace “Grandma to banson abin nan da zafi yadenamin” dan dariya Grandma tayi tace “okay I will makesure yau kin kwana anan na kulle kofan falo sabida karyazo sabida kihuta yau jikinki ya warke kafin yakara zuwan miki, but after today Du’a dole u just have to learn how to carry and withstand burden na mijinki, like I said this is ur life now, reality dinki, Asad shine mijinki, ki daure kibiyamai bukatunshi kibashi hakkin shi Du’a karki jefashi wani hali, Asad is very young kibarshi yana karban hakkinshi sabida ke Amarya ce amman zakizo kisaba kawai ki daure kizama mai juriya kinji, yanzu anjima dazaran ankira laasar yana masallaci saiki wuf kije gidan ki gaida baban mijinki da miji da Ammi ki taho kidawo nan kafin ya turkeki kinji, karki damu akwai wasu magunguna yanzu haka ma direba na yaje karbowa wlh wlh Asad saiya miki kuka, wayeshi? Zamu tattakashi zaisa yanzu ya auri mace, yanda kikeda kyan nan sanan kika kaimai budurcin ki yabare ai wlh saikin takashi kinyi tafiya akanshi, ihu ko saikin taushemai baki, share hawayen ki kingama kuka, kuka kuma yanzu table have turn, Asad zaki barwa kuka kinji, idan magungunan suka iso karki sake kiyi wasa dasu kinji” gyadama Grandma kai tayi dasauri tana murmushi, Grandma tace “sanan koda wasa sirrin gidanki karna ji awaje, nine komi naki Du’a, ur mother uur sister ur Anty ur friend, ur Grandma ur baba and Mama, komeke damunki tell me kinji” gyadamata kai tayi Grandma tace “don’t worry Asad yagama shigo hannu”.

Fita Grandma tayi daga dakin, itakuma takoma ta kwanta akan gado abinta ahankali tana murmushi, duk duniyan nan ayanzu babu wanda takeso yakuma yarda dashi irin Grandma, tadade tana tunani so yanzu Ya Asad na sonta daman da gaske? ita lokacin da Rahima tace haka bata yarda ba saida Grandma tafadi mata yau dinan sanan ta yarda, dan murmushi tayi ahankali tana tuna yanda yake kula da ita at the same time tana tuna yanda yake mata mugunta, wani kalan murmushi tayi ahankali tace “wlh saina rama” sanan takarayin murmushi tawani kwankwale madaran sanan ta kwanta abinta ahankali, tana kwance awajen saida taji ana gyaran mike din masallaci za’a kira sallan la’asar dasauri tamike tsaye, bakin hijab dinta dake kan dadduma tadauka tasaka sanan tasaka slippers tafito ahankali ta sauko kasa Grandma dake cin abinci tace “zakije” gyadama Grandma kai tayi, ahankali Grandma tace “to gyara tafiyan daurewa zakiyi duk zafin ohkay” gyadamata kai tayi tana gyara tafiyan zuwa normal tafiyanta amman ahankali bata iya sauri, murmushi kawai Grandma tayi tadauke kanta tace “ja’irin yaro zakaci gidanku ne Asad” tana fitowa daga Gate dinta takarasa gaban gate dinsu hannu tasa zata bude gate din aka rigata budewa Sharif ne tareda Asad zasu masallaci, ganin Sharif yasa ahankali tasaukar da kanta tace “Ya Sharif ina yini” murmushi yamata yace “Mrs Asad welcome” sanan yabi ta gefenta yawuce yay mosque batare daya kara waigowa ba, dago idanunta tayi ahankali tazubasu cikin na Asad dake tsaye batare daya fitowa yana kallonta, Sharif tadan juya takalla sanan takalleshi cikin wani irin classic voice takalleshi tace “kai bazaka masallacin bane why are u still standing” tamai maganan tana nunashi da hannu, wani irin binta da kallo yake this is the first ta tabamai magana ko tambaya haka without fear ko shakkan shi akan fuskanta, dan ijiyan zuciya yasauke jin antada salla sanan yataho ahankali yafito daga gidan daidai saitin ta ya tsaya faduwa gabanta yayi amman bata nunaba ta dake tana kallonshi, murya chan kasa yace “wait for me a flat dina” kallonshi tayi batare datace to ba, juyawa yayi yawuce saida ta bari yay kaman taku biyu sanan ahankali tace “Asad” juyowa yayi dasauri, ahankali da hannunta da bakin lallen yasoma goge wa tamai alamu dayazo, like kasa boye mamakin shi yayi hakan ma yasa baisan lokacin dayakai gabanta ba, dan yatsine fuska tayi tace “kabani wayanka please nagaji da rashin waya I am bored, I don’t even know why kawai fasamin wayana, mutum sai fitinannen kishi” wanan karan saida Asad yadan zaro idanunshi like is she Du’a daya sanni ko junnu sun shigeta ba, sometimes idan abu yay hitting naka unexpectedly bama kasanin what exactly zakayi, situation din da Asad yasami kanshi kenan, kawai yay mutuwan tsaye yana kallonta, hannunta tamika mai murya chan kasa tace “bani wayan, idan kasaimin nawa saina maidama back Husband”! wlh ji kawai yayi yasa hannu a aljihun wandonshi zai ciro wayan tsabagen rudewa yama manta wayan na aljihun gaban riganshi da hannunta ta nunamai aljihun gaban riganshi tace “ga wayanka nan ina gani” zaro hannun yayi daga aljihu yasa agaban rigan yaciro yamika mata karba tayi batare datamace thank u ba tajuya kaman ta amshi nata tashiga gidan tamaida gate din tarufe da karfi, karan dayayi yasa yay firgigit daga dena kallon gate din yawuce mosque dasauri.

Tana shiga gidan wani irin tsalle tayi tana tana bubbuga kirjinta dake neman fitowa sanan tahau rawa so Grandma was right Asad na sonta, sabida ya ganta batada wayau shine yake mata abinda yaga dama gashinan yanzu bai mata komi ba, wani irin murmushi tayi tana kallon wayanshi dake hannunta sanan tajuya tana tafiya ahankali ta tafi gidan, sallama tayi tashiga falon, Aneesah da Mariya ne kadai afalon suna jera kula a dinning, Mariya na ganinta ta taho da gudu ta rungume ta tace “oyoyo Du’a” murmushi tayi, itakuma Aneesah tana inda take ahankali tace “ina yini Anty Du’a” daga Mariya har Du’a kallonta suke saikuma sukai murmushi, Du’a tace “sannu da aiki Aneesah” sanan takalli Mariya tace “bari naje na gaida Dad da Ammi” tawuce sama ahankali takebin stairs din tana runtse idanu sanan tawuce sama, dakin Ammi tafara shiga bata ciki hakan yasa tai dakin Dad, sallama tafara yi dasauri Ammi ta taso bude kofa tayi tana murmushi kafin Du’a tai magana ma Ammi ta rungumeta anatse tace “maraba da my daughter” sanan tasaketa ahankali tai cupping face dinta ta manna mata kiss agoshi sanan tasaketa tana kallonta, duka duka yaune rana na hudu da aurensu amman tai wani unbelievable kyau, ahankali Du’a tace “Mum ina yini ya jiki” murmushi Ammi tayi tace “ni naji sauki ga mara lafiya nan baban ku muje ki gaidashi” shigowa sukayi ciki har gaban gadon Dad sanan ahankali tadago kai takalki Dad dake kallonta kaman zai hadiye ko kadan baiso tasako hijab ba tace “Dad ina yini ya jiki” ahankali yace “dasauki Du’a, ya naki jikin” ahankali tace “dasauki” Ammi tace “ga fuskan kinaan bai gama sabewa ba, koma gida ki kwanta please, ke ciwo babanku ciwo ina zansa kaina, at least ke kihuta naji da wanan” dan murmushi Dad yayi yace “kinga Asad ne yanzun nan suka tafi masallaci” Girgizamai kai tayi, murmushi yayi dadi har ranshi yace “to to shikenan wuce kitafi abinki ki huta agida kafin mu rikeki muhanaki komawa wajen Grandma dinki” murmushi tayi tajuya ahankali ahankali tace “Mum bye bye” Ammi kaman ta cinye ta kallon yar karaman baby takema Du’a ahankali tace “bye bye baby na” fita Du’a tayi daga dakin ta sauka dasauri, bye tama Mariya dakeson riketa sanan tafice daga gidan, dasauri sauri harda dan gudu ta shiga gidansu dan batason anything dazaisa yafito ya ganta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button