KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

            ✍️M SHAKUR 

Free Page
EPISODE 1️⃣5️⃣
Hannu Hajiya tasa cikeda tausayinta tace “stop crying, dena kuka, ya isa” tasata ajikinta tana bubbuga bayanta tana gayamata kalamai masu sa natsuwa hartai shiru, saida ta natsu sanan Hajiya tace “bari nakawo miki abinci kici nasan is being long bakisa abinci acikin nan naki ba” batama tsaya sauraronta ba tawuce tafita, lafiyayyen tuwo takawo mata da miyan kubewa busassa da kifi da man shanu, bude kofa tayi tashigo dakin tana kallonta, maida kofan tayi tarufe takaraso ijiye tray tayi akan carpet tace “wayyo jikin tsufa, sako kici kinga kinsani aiki” murmushi tayi ahankali sanan tasauko tasan halin Hajiya hakan yasa batai gaddama ba tashiga cin tuwon sosai taci tuwon ta koshi sanan taje tawanko hannunta anayi tafito carpet din Hajiya tanuna mata hakan yasa tazo tazauna kusada ita, ahankali Hajiya tace “Walida, ke yanzu ba yarinya bace, inda ace Asad yayi aure da yanzu kinada jikoki dozen ma halan” dan murmushi tayi Hajiya tace “my point is indai rayuwan zaman aure ne you’ve come a long way saidai kibama wasu shawara, kunada yaro dakeda shekaru 33 aduniya aiko littafi aka baki zaki iya rubutawa kan zaman aure, Baban Asad wanan halin nashi bayau ko jiya yafara ba, kinyi kuka kinyi kuka Walida, kukan jini ne kawai yarage bakiyiba, kinsan yanayin lafiyanki, amatasayina na mahaifiya agareki dudda bani na haifeki ba abinda nafadi miki kafin kutafi kano shizan kara gayamiki ki manta da batun mijinki and concentrate akan yaranki, fi fawwalama Allah lamarin Baban Asad kidinga mishi addu’a idan yanada rabon shiriya wlh zai shiryu, kinsan yanda Asad ke sonki sama da rayuwanshi ko ciwon kai yaron nan yaga kinayi lamarin shi saiya tabarbare yaron dayakeda TV show dazai fara nan da kwana biyu, I think, kinason ya susuce ne”? Dasauri Ammi tace “a’a Hajiya” “then dole ki jajirce ki kauda komi, Alhamdulillah baihanaki ci ba baihanaki shaba, ke kodama yahanaki danki Allah ya horemai mezai dameki, ki share batun shi yanda yasa kafafunshi yafita dakanshi zaisasu kuma yadawo gidan kinji” harcikin ranta taji wani sanyi wani zubin takance inama ita yar Hajiya ce, dan Hajiya tayi arayuwa, tadauketa tamkar yar cikinta, haka tadauki yaranta tundaga su Asad da Sharif harzuwa kansu Aneesa kaman jikokinta, babu abinda abinda take iyayi bata sanar da itaba, murmushi tayi ahankali tace “Hajiya nagode, Dadda da Turai sunce na gaisheki” haba Hajiya takama tace “wanan rigimammen tsohon yanzu bai biyoku yadawo nan Abuja yadinga ganin specialist bako” dariya tayi kaman ba itane tasha kuka ba tace “ai yace shi kano yakeso, Turai natare dashi dakuma Nurse dinshi, ya samu lafiya sosai kafin mudawo ma” Hajiya tace “Masha Allah”.

“Grandmaaa” Du’a data shigo falon takira Hajiya ganin bata falo, shigowa Razika dake biyeda ita tayi tace “tana sama, muje kinuna mata kalban da aka miki” dasauri Du’a tai stairs tana murmushi sosai dan kitson da aka mata yamata kyau dan ba’a taba yimata kalanshi ba, tana kaiwa falon sama takara kiranta. “Grandma” dasauri Hajiya take tareda Ammi tace “jikata tazo bangayamiki ba, Du’a gani nan adaki shigo” bude kofan dakin Grandma ahankali tayi tashigo Razika biyeda ita, ganin wata babbar mace baka tareda Grandma yasa ta tsaya batare data karaso ba, saukar da kanta tayi kasa ahankali ta gaida matar tace “ina yini” murmushi Hajiya tayi takalli Ammi tace “ana gaidake” wani kayataccen murmushi Ammi tayi tace “Masha Allah, sabida kin ganni kikaki karasowa ciki wajen Grandma dinki” dan murmushi Du’a tayi cikeda kunya ta girgixa kai saikuma tajuya dasauri tace “bye Grandma” sanan tabi ta gefen Razika tafice dasauri, dan dariya Hajiya tayi tace “kinganta haka take akwai kunya” takalli Razika tace “anmata kitson” gyadamata kai tayi tace “anyi kalba akayi, yayi kyau sosai” “haka nakeso, jeki bata abinci taci” ficewa Razika tayi, Ammi tace “Hajiya yar Muktar din UK ne” dariyan manya Hajiya tayi tace “yar Zainab din kano ce, Du’a, wacce nake baki labarinta” murmushi Ammi tayi tace “Allah sarki Yarinyar ga kyau ga natsuwa”

Saida tai wanka sanan ta chanza kaya zuwa wani gown data dauka daga wardrobe red iya guiwa ya tsaya mata yamata kyau, bata daura dankwali ba tasaki kalaban dayake nan har waist dinta kaman ansaka mata attachment tabude kofa tafito da saurinta ta sauko dan itada Razika sun biya wani super market tadauki drawing book babba da HB Pencils da eraser da colors, dakin kasa wanda shine dakin Razika da Amina ta shiga suna zaune sunacin abinci duk suka bitada kallo ganinta adakinsu, Razika ta kalla tace “ina drawing book dina”? Dan ware ido Razika tayi sanan tace “inama nasa ohh natuna suna dinning” dasaurinta harda dan gudunta tawuce tafita a dinning ta tsaya ganin komi yasa tasaki wani murmushi she’s so happy and excited bayan reading novels wanda technically Ya Hamad ne yakoya mata the only thing datasan ta iya shine zane, babu abinda bata iya zanawa ba saida yawanci abinda tafi zanawa yanzu shine takalma tana bala’in son zama takalma sabida batada takalma agida dayawa dan bata fita saisa hakanan idan tazauna saita dinga zama dream shoes dinta.

fitowa tayi tazauna akan falon, bude komi tayi, tai sharpening pencil dinta sanan tabude hadadden drawing book din da Razika tasiya mata ta shiga zane, yanda take zanen kadai saika tsaya kana kallon hannunta sabida wani kalan burgewa datake yi kafin good 3min tagama zama wani tsantsararren takalmi hill na mata, murmushi tayi tadauki drawing book din tana kallon takalmin saikuma chan ta hura iska sabida all particles na eraser dakekai yafita sanan tace “to yanzu wani suna zansa maka kai takalmin nan kaga nadade banyi drawing ba tunda drawing book dina na gida yacika Ya Hamad baikara sayomin ba” shiru tayi tana tunani kawai saita sauke drawing book din akano saitama zanen tittle Du’aXAbuja, kallon rubutun tayi dayay kyau, kawai saita bude wani page tashiga zana wani daban.

Ahankali Ammi datai sallama da Hajiya ke tafiya kan stairs Hajiya bata rakota ba sabida wani office related call da aka mata, tundaga stairs take kallon Du’a, dudda batasan metake zanawa ba but ganin drawing book yasan tasan zane take, kitson kan yarinyar tabi da kallo da yanda take zane ita kadai saita daga ta kalla tai murmushi tasauke tacigaba, hakanan Allah mai daurama mutum so da ki kawai taji Du’a na burgeta tanason yarinyar, karasa saukowa tayi Du’a ma bataji saukowanta ba sabida yanda hankalinta yay nisa, karasawa cikin falon Ammi tayi ta tsaya tana kallon takalmin da Du’a ke zanawa batasan lokacin datace. “Masha Allah, you are gifted Du’a” dasauri Du’a tadago kanta ta kalli Ammi, murmushi tayi sosai tace “Mum yayi kyau”? Hakanan Ammi batasan mesa ba but kiranta da yarinyar tayida Mum yasa son datake mata ma yay double da sauri tazauna kan kujeran dake gefen Du’a tamika mata hannu tace “bani drawing book din naga” da sauri Du’a tadauki drawing book din tamika mata sanan ta matso kusada kafan Ammi ta daura hannayenta kan cinyan Ammi batare datama sani ba tana kara leka drawing din itama, gyara zama Ammi tayi jin yanda yarinyar ta dagata tafara duba drawing din daga farko tace “wow, haka kika iya zane Du’a, this is talent wlh” murmushi tayi sosai dan batasaba ayabeta ba agidansu Ya Hamad ne kawai yake cewa zanen ta yay kyau, murmushi takara yi tace “Ya Hamad ne kadai yataba cewa inada talent sai ke Mum” takarashe maganan looking damn happy dayasa Ammi taji suka matsalolinta ma sukau, hannunta takai tashafa kan Du’a tace “you are very very talented Du’a, kinsan nawa ake biyan wayanda suka iya zama abu haka” girgixa mata kai Du’a tayi tana kallon Ammi saikuma tace “Mum ni ai baza’a biyani ba, kinga banyi school ba a JSS2 na tsaya, wanda yay karatu ne ai ake bashi aiki ko”? tunda take maganan Ammi ke kallon yarinyar, idan tana magana sosai zakaga rashin wayau da yarinta aciki wanda yarinyar dakeda shekarunta bai kamata ace hakan yasameta ba, murmushi Ammi tayi tace “ko ina talent yake yanada kyau ayi acknowledge nashi, and it doesn’t matter sabida kin tsaya da karatu a JSS2, with this” Ammi tanuna mata drawing book din tace “with this zaki iya samin aiki a companies da dama that are into shoes kuma abiyaki” wani irin kyalkyacewa da dariya Du’a tayi tawani kife kanta akan kafan Ammi tanajin dadi sosai data kasa boyewa dayasa Ammi takarajin tashiga ranta, Hajiya data dade a stairs tana jinsu takaraso tazauna kan kujera tace “ke karki karya ma mata cinya inba so kike Asad yashigo yay yaki dani ba kirufamin asiri yaron nan son maman shi yake kaman me” dariya sosai Ammi tayi tace “kundai fi kusa kedashi Hajiya” tashi Du’a tayi tana murmushi itama, Ammi tace “how about natafi da wanan drawing book din sabida nasaman miki aiki dashi” dawani irin sauri ta gyadamata kai tace “eh Mum kutafi dashi” tawani washe baki tajuya tana kallon Hajiya dake kallonsu itama tana murmushi tace “iyye Du’an baaa, tobazakima Mum din naki godiya ba za’a neman miki aiki kinata washe baki” cikeda farin ciki takalli Ammi tace “Mum nagode Allah amfana” tashi Ammi tayi rikeda drawing book din tace “bari nashiga gida” Takalli Du’a tace “yaushe to zakizo ki gaidani agida inada yammata nima kinga saikiyi sababbin kawaye ko” juyawa tayi takalli Hajiya dake kallonta tace “yo jama’a kome aka tambayi yarinya sai tajuyo takalleni, Razika da Shemau sa rakota suzo gobe” “shikenan, Hajiya sai munyi waya” “tom Walida ki gaidamin da Sharif dasu Aneesa, shikuma gogan kice nace Allah yataroshi” dariya Ammi tayi tana bude kofa tace “yau dai munjiku arana kuda ba’a shiga tsakanin ku” Jan kofan tayi tarufe tafice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button