KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

7️⃣9️⃣
DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA MATA BA DUNIYA WA LAHIRA

Saida yay sallan asuba sanan yafito daga masallaci yana kallon gidansu Grandma kaman yashiga yadubota danshi kanshi yasan yabata wahala jiya amman dai yadaure yawuce yashiga gidansu, direct flat dinshi yawuce wanka yakara yowa sanan ya shirya cikin wani milk 3quater da maroon t-shirt yafito, yay flat dinsu, su Rahima yagani suna gyara dinning da Aneesah da duk ta tame hannunta yadan warke, gaisheshi duk sukayi amman kallo basu isheshi ba yawuce sama, baima karasa kaiwa ba saiga Dr Dad yashigo hakan yasa Asad yajuyo yana kallonshi yana sanye cikin riga da wando yarike labcoat dawani jaka hannunshi wuyanshi rataye da stethoscope, murmushi yayi yace “Asad ina gajiya” ahankali yace “good morning” sanan yawuce Dr na biyedashi sukai dakin Dad atare suka shiga Sharif da Ammi ne adakin suna kusada Dad daya farka idanunshi biyu Ammi nabashi Kamun dayasa ta dafamai, Dr na ganin Ammi yace “Madam banace kihuta ba, ga maza anan kibasu su bashi u need rest” dan murmushi tayi tana daukan handky tana gogema Dad baki, ahankali Dad yakama hannunta yadaura kan kirjinshi sanan yakalli Dr yace “my wife is my entire life ko” gyadamai kai Ammi tayi Sharif yayi murmushi, Asad shi ai yana tsaye, Dr yace “kagama dan inaso nadubaka and make decision as soon as possible” ahankali Dad yakalli Ammi Yace ” bari Dr yadubani” tashi Ammi tayi ahankali ta matsa hakan yasa Dr yazo wajen yana duba kafan Dad dayay paralyze din karya, ya minsili kafan ya jijjiga amman Dad yaki motsi da ita sanan ya auna BP shi, kafin yajuyo yakalli Asad da idanunshi kur akan Dr yace “BP shi yasauka sosai but har yanzu kafan baya responding, kuma zazzabi yasauka sosai inaga….” da sauri Dad yace “Dr please nida yarana will leave the country, I have office to run, kafata is my everything, nida next year nakeson nai contesting for senate president my leg have to be well” ajiyan zuciya Dr yace “okay in that case zan turaka hospital din danai aiki a NYC, asibitin are specialize in stroke da mutuwa jiki haka” ahankali Dad yace “okay contact them zan daukeka zaka bini, sai yarana Asad da Sharif, Asad is newly married dan haka kadauki matarka, saikuma my wife ko sweetheart” gyadamai kai Ammi tayi ahankali, Dad yadubi Sharif yace “kaje office dina zanma senator Tahir magana, zai baka details private jet xamubi, Asad kaika zauna dani anan, Dr go and get ready dole narikeka kana kaina I won’t risk my health for anything” Kallon Asad Sharif yayi yaga wayanshi yake dannawa, Dad dayaga Sharif din yace “lafiya kake kallon Asad, ahankali Sharif yace “Dad Du’a doesn’t have any papers” ahankali kaman mara lafiya Dad yace “ambassador su abokina ne Kaj…..” wani kalan tarin karya yafara dasauri Asad ya kalleshi Dr yay kanshi yace “kadena magana dayawa calm down” gyadamai kai Dad yayi yana kama hannun Ammi dahar tazo kusada shi, Sharif kuma yawuce, sallaman Grandma dasukaji yasa duk suka dagokai shigowa dakin tayi tana kallon Dad tace “Allah sarki, sannu babban Asad, ya karfin jikin” ahankali Asad ke kallon kofan hardan lekawa yake kallo daya Ammi tamai sanan tai murmushi tace “ina kwana Hajiya” zama kan kujera Grandma tayi tace “lafiya lau wlh yamai jiki” ahankali tace “yaji sauki, where is my daughter”? baki Grandma ta tabe tace “hmmm wlh nabarota agida tana bacci ta tashi jikinta zafi gashi nan tayi very weak, shine nace ta kwanta anjima saita shigo” ahankali Dad yace “tayi wani abun da daddare ne datai weak”? dasauri Grandma tace “a’a wlh, to meme zatayi itada ba yar gidana ba, barinmin gida ni zamatayi yau inba hakaba mutum zaifara biyan kudin haya wlh” tai maganan tana hararan Asad, dan murmushi yayi yace “Grandma good morning ” dan dariya Ammi tayi tace “dayake ma kunfi kusa” tashi tayi takalli Asad tace “stay with ur Dad Dr bari muje chan” to Dr yace sanan suka fice itada Grandma, Grandma na mamakin Asad jibeshi kaman bashine yashigo mata gida tsakar dare ba, batada nauyin bacci daga buga gate din dayayi na gidan ta farka, ta tashi tadaga labule taga meke faruwa agabanta security ya tambaya waye Asad ya shigo yashiga dakin Du’a, daganan murmushi abinta tayi tai bacci dan bata bukatan tasan me sauran hasalima farin ciki tayi yanda yakeaon jikanta saisa itakuma tai alkawari saita zuba last kobo dinta a gyara Du’a dan gyarane mace, wanan halin nashi na miskilan ci saiyahau kanta yay kuka tsabagen dadin da zaiji, yanzu haka yau dinan wasu magunguna data biya kusan miliyan uku zasu sauka daga Sudan, wanan na amarci kadai yaje yake biyota da daddare bari tasha na Sudan halan agaban mutane saiya dinga lalubarta, murmushi takarayi tace dole ki zage dantse Du’a kinriga kin shigo gidan nan ajininsu yake wlh dukansu kakap.

Tadade awajen Ammi tana bata shawara tarage damuwa dan tasan yanda Ammi keson Dad, Ammi tabata labarin zasuje New York city cikin kwanan nan anfitar da Dad harda Du’a sosai Grandma taji dadi sai wajajen 1 tabar gidan takoma gidansu, sama tawuce ahankali tabude kofar dakin.

Du’a tagani zaune akan gadonta dataga an chanza bedsheet gabaki daya tai lagwa lagwa tai wani irin kyau da idan ka kalleta saika kara kallonta tana sanye cikin wata atampa doguwan riga data kamata sosai kana ganin sama saman white perky boobs dinta tanashan wani yogurt din magani da Grandma tasa Razika tabata kanta babu dankwali uban gashinta duk sun tattare sabida ruwan dasuke sha kullum, ganin Grandma yasa tai murmushi ahankali, Grandma tace “ashe kin tashi ya jikin”? Ahankali tace “da sauki Grandma” murmushi Grandma tamata sanan tazo kusada ita tazauna ganin yanda duk fuskan yarinyar yayi kaman jira Du’a take fadawa jikin Grandma tayi tafashe da kuka sosai tace “Grandma wlh ni banason Ya Asad shine yasa na aureshi, Grandma wlh tsoronshi nakeji, kinga ko kasheni zaiyi Grandma ko jiy……” bugemata baki Grandma tai da hannu hakan yasa tai shiru tasake fashewa da kuka tama kasa magana, ahankali Grandma ta kankameta ajikinta murya chan kasa tace “Du’a saurara kiji, har yanzu kallon kanki kike kaman wata yar yarinya but the truth is u are not anymore so dole yanzu u need to wake up to reality and face life, nariga na aurar dake ban isa nacema Asad ga lokacin dazai nemi matarshi koga lokacin dabazai nemi matarshi ba, tashi kigani” ahankali Du’a ta tashi daga jikinta tazauna tana kallon Grandma, Grandma tace “now stop crying” hannu tasa tagoge hawayenta tass, sanan Grandma tace “dazu kince wani abu Asad yasa kika aureshi “? Gyadama Grandma tayi, Grandma tace “how”? Ahankali tabama Grandma labarin komi from A to Z, Grandma felt proud of Asad over, murmushi tayi tace “Du’a tunda nasan Asad banma taba ganin ya kula mace ba balle yama mace kalan son dayake miki, but yanzu is time da u will deal with him codedly, but inaso kidena maganan zaki rabu dashi baki sonshi, shi aure da soyayya ginashi ake, look at ur husband Asad, look at him bada fuskan tsoro ba, look him as a human that he is and love anything u found about him lovable, today and now should be the last day dazaki ji tsoron Asad kinji” gyadamata kai Du’a keyi dasauri tanajin wani karfi da da kewan zuciya aranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button