KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Inda suke dazu suka koma Sharif yajamata kujera ta zauna sanan yazauna kusada ita wani abu namai wato aranshi, daurewa yayi yadanne ya matso kusada ita sosai ahankali yana kallonta yace “Du’a” kallonshi itama tayi tace “uhm” ajiyan zuciya yasauke yasaukar da idanunshi kan fararen hannunta sanan gently yamika hannayenshi biyu yakarbi hannunta yarike dasauri takalleshi, dan murmushi yayi batare daya kalletaba yana kallon hannun yace “sorry nasan na rike hannunki kuma ba kyau I just wanna tell u something ne” yaydan shiru sanan ahankali yace “tun ina dan yaro nakanyi mafarki na auri mace irinki” yaydan shiru sanan ahankali yace “inason mace mai natsuwa da aji, ni namiji ne dako kadan wayan nan wayayyun matan yan gari da sauransu basa burgeni hasalima nafison mace wacce batasan komiba wacce nice zan shayarda ita dadi nakoyamata komi, mai natsuwa mai kyau kamila mai cute smile, ranan dana fara ganinki I saw that kind of lady in you, I love you so m…..” tsayarda maganan yayi jin fuskarta akan hannunshi, dasauri yakalleta bacci tayi.

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

  ✍️ M SHAKUR 

Not edited
sorry banyi editing this page.

EPISODE 4️⃣1️⃣
Zaiyi magana saiga Rahima ta taho wajen tana murmushi tana kallon Sharif irin kallon nan na nasan komi daure fuska yayi tana karasowa gabanshi yace “me” dariya tayi tace “babu naga tayi bacci ne shine zan tadata muje chan dakinmu ta kwanta tunda kasa ce ita” hararanta yayi yace “come amman kibita ahankali please wlh duk kun wahalar da yarinyar nan ita batasaba da gantali irin nakuba” tabe baki Rahima tayi tace “cute Baby alert wlh harna hango d’anda zaku haifa” tai maganan tana tapping fuskar Du’a tana kiran sunanta Du’a, Du’a, bude idanu kadan tayi hakan yasa Rahima tace “tashi muje ciki nima fitsari nakeji” mikewa tsaye tayi dasauri duk cikin bacci tana sosa ido, wayanta Rahima tadauka tace “muje” gaba Rahima tayi hakan yasa Du’a tabiyota abaya ahankali tana tafiya kadan kadan danga bacci gakuma takalmi Sharif yabita da kallo baccin dayagani a idanunta yasa baice mata komi ba, bude kofa sukayi suka shiga falo sama sukayi suna kaiwa dakinsu Rahima kawai fadawa gado tayi ko lafiyayyen 1min batayiba bacci yasakeyin awon gabada ita, itakuma Rahima tawuce bayi fitsari tayi sanan tafito tana kallon yanda Du’a ke bacci ko takalmi ma batacireba tace “Allah sarki Du’a aikam kingaji wanan bacci haka, fitinan Aneesa kadaima yaci kimai baccin nan yau kwana nawa tahana mutanen gidan nan sukuni da shegen birthday dinan” tai maganan tana daura hannu akan switch takashe wutan dakin tawuce tafita sanan tafito ganin Sharif yakoma filin rawa yasa tace “yagama soyewa yakoma rawa kuma” murmushi tayi tawuce wajen itama duk abinda ke faruwa a idanun Abba, ahankali yazame jikinshi yasudade yawuce flat dinsu batare dakowa yalurada shi ba.

Sama yayi dasauri kirjinshi na beating fast fast, direct dakinsu Rahima yayi yabude kofa ahankali kaman barawo, ganin dakin da duhu yasa ahankali yakai hannunshi kan switch din wutan dakin, kunna wutan dakin yayi dakin yay wani haske bau, ganin Du’a kan gado tana bacci yasa da sauri yawani irin waiga baya yana kallon falon saman su jin shiru babu wanda yakenan acikin gidan yasa yamaida kofan yarufe ahankali sanan yasake waigowa, tundaga kan kafafunta dabata cire silver hill dinta ba yake kallo dasukamai bala’in kyau zuwa kafafunta dasuke abude sabida daman rigan bai kaimata har kasaba gashi yanda ta kwanta yasa yadan kwashe gefe sai faran kafanta ya bayyana harzuwa wajajen bayan gwuiwanta, wani irin lashe miyau bakinshi yayi jikinshi har tsuma yake yace “wanan wace irin danyar yarinya ce haka, yarinya kaman hurun ini, Ya ilahi jibi fata saikace da jinin dawisu take wanka kullum wayyo Allah na gabana” yay maganan yana takawa zuwa gefen gadon yana wani irin kallon fuskanta da gaban riganta dayasa yanayin kwanciyan ta kirjinta yadan fito, wanan karan harwani zazzago harshe waje yayi kaman dan kare yana kallonta baisan lokacin daya mika hannunshi zai tabataba yaji anbude kofan dakin dawani irin sauri yakoma baya gabanshi nafaduwa sosai yakalli kofan Asad yagani da headphone makale akanshi hada ido sukayi da mahaifin nashi, saikuma ahankali yajuya yafice dawani irin sauri yace “shitttt nima maiya kaini, na kwafsa wlh” yay maganan dasauri yajuya yafita, ganin Asad zaune kan kujeran falon sama yana daddanna wayanshi yasa yay wajen yasami gefenshi yazauna yana sauke ijiyan zuciya yace “Asad wacece wanchan yarinyar wai nashiga dakinsu Rahima naduba yama sunanshi gorona dan nemanshi nake naganta kwance tana bacci wacece ita” batare daya kalli Baban nashiba yace “I don’t know her” dan murmushi yay yace “kai daman dababu ruwanka da yan gidan nan wama zaka sani” yay maganan yana murmushi yana kallonshi ganin Asad ba kulashi zaiyi ba yasa yatashi yay dakinshi daidai Mariya nahayowa falon saman da gudunta, hada ido dasukai da Asad dake mata wani mugun kallo yasata rage gudun murya chan kasa tace “sorry Ya Asad I’m about to pee on my panties ya matse ni” dauke kanshi yayi yace “when u go inside wake that girl ta tafi gidansu” gyadamai kai tayi batare data iya magana ba dan fitsarin ya matseta tawuce tashiga dakinsu tana fitowa tashiga tada Du’a da kyar ta iya tabude idanunta takalli Mariya, Mariya tace “sannu da aiki Du’a wanan ne birthday ko to tashi kutafi gida dare yayi, fara zuwa ki wanke fuskanki” ajiyan zuciya ta sauke cikin bacci sanan ta tashi ahankali zaune takai kusan 2nin ahaka Mariya tace “kefw nake jira” tashi tayida kyar tashiga bayinsu fuskanta ta wanka fuska sanan tafito tana hamma, wayanta da Mariya tadauka tabata tace “muje” tana gaba Mariya na biyeda ita abaya tana sosa idanu tabude kofa tafito, hada idanu tayi da Asad dayasa taji ta turgude tai baya zata fadi dawani irin sauri Mariya tariketa tace “subhanallahi ke Du’a wai haka kikeda bacci karki fadi kiji ciwo fa” tai maganan tana dan turata sabida ta tashi tsaye da kyau, tashi tayi tasauke kanta kasa tawuce tai stairs batare datasake bari sun hada idanu ba.

Har gate dinsu Mariya tarakata sanan tadawo ahankali tabude kofa tashiga falonsu tana tafiya babu kowa falo tariga tasan su Razika sunyi bacci stairs tayi tahau tun kafin takai karshen stairs din takejin muryan Grandma nafada, mamaki abin yabata to dasu Razika take fada, but hardly kaga Grandma nama su Razika fada dan bama su cikamata laifi ba, tun tanajin hayaniya fadanta bata jin maganganun datake tana kaiwa falon sama tasomajin maganganun da kyau. “Muhammad nagayamaka ka kira kanwarka ka shaida mata wlh inhar tazabi mijinta kanni mahaifiyarta dana haifota duniya na shirya na yafe Zainab, tasha min laifi I ignore nahakura I always term abubuwa da kuskuren datakeyi amatsayin soyayya ce tarufe mata idanu but nalura abin mata tsabagen iskanci ne, kagaya mata maganan Du’a tadawo karta karamin shi inba hakaba wlh wlh wlh saina masifaffen bata mata rai”…… iyanan taji kawai taji gabanta na mugun faduwa, tana ganin tunda tazo gidan nan bata tabajin Grandma nafada tana masifa ba sai yau, Du’a tadawo! Du’a tadawo! komarda ita kano za’a sakeyi, nooo jitayi kanta yawani irin buga yasara dasauri tajuya takoma kasa, kitchen ta shiga tadau ruwa tashiga sha dasauri sauri, wani irin shakewa tayi hakan yasa tasaki cup din kasa tana tari sosai tana bubbuga kirjinta, Grandma ta fitowanta daga daki kenan ranta abace jin tari yasa tasauko dagudu tayo dinning gani Du’a a kitchen ta dafa fridge tana tari sosai idanunta sunyi ja yasa tace “subhanallahi sannu sannu, daga shigowanki sai tari Du’a, halan kishi ki kije sosai, sannu ko” tai maganan tana bubbuga bayanta, tsayawa tarin yayi Grandma tace “sannu, iyye daman haka akasha kyau yanmata ko a nunamin aka wani tafi, ya akayi kika dawo naji ba’a gamaba” asgaeabe tacd bacci nakeji, fuskanta Grandma tashafa tace “jeki kwanta to kinji, amman ki wanke wanan fentin da aka miki kafin ki kwanta kinji yar albarka, Allah yatashemu lpy” gyadama Grandma kai tayi tana tafiya sama hawaye ya zubo mata Grandma tabi bayanta da kallo cikeda wani irin so dan sosai Du’a tashiga zuciyanta yanda yarinyar nan ta zama happy girl gashi harya making friends bazata taba bari tKoma kangin datake ciki daba wlh.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button