KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Aneela na shiga falon tai wajen Mami tamika mata wayan tace “Mami Uncle say I should give this phone to Ya Du’a” ahankali Mami tace “to wuce ki kaimata” kwala mata kira Mami taji Kaka tayi. “zokiga barnan da yaron nan yawa yarki Zainabu, taho nan”.

DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

PAY 500 INTO 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461

you can chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461

SANARWA SANARWA SANARWA!!!!!
MATAN AURE WATSAPP CLASS WILL BE BACK THIS FEBRUARY, AND REGISTRATION IS ONGOING, ZAKI SHIGA GROUP DIN WITH JUST 2K. IF YOU ARE AN OLD MEMBER ZAKI BIYA JUST 1K. THANK YOU ❤ come and join ki koyi so many amazing marriage stuff.

6️⃣7️⃣

Ahankali Mami ta tashi tana wani irin kin kunya tai sama tana hawa benen ahankali, dakin datagani abude tayi tashiga ciki ahankali, Du’a datagani kwance idanunta sunyi jajir sun kumbura yasa taji gabanta yawani irin fadi, ganin Maman ta yasa kaman jira Du’a take tamikama Ammi hannunta tana wani irin kuka kwance akan gadon, shiga cikin dakin tai dasauri ahankali Mami tazauna abakin gadon tana kama hannun Du’a dake kuka da kyar tsabagen bakar wahala ga jikinta dayay zafi sosai, dago kanta tayi ahankali takalli Su Nana da Hawwa dasauran yaran gidan yanda suka tsaya sukai charko charko suna kallonta, cire kawaici Mami tayi ahankali tace “Nana kwashe yaran nan kutafi kasa kufara aiki” kaman jira Mom take tace “koran mini yara akeyi nagadai inda ace bata raba Nanan danata mijin ba da yanzu tariga yartaki aure” cikeda masifa Kaka takalli Mom tace “kefa dadina dake kenan wani zubin sai kiyi abu kaman mai hankali wani zubin kuma kaman jaka kike wlh” cikeda bacin rai Mom takalli Kaka, dayake Kakan tafita iya bala’i tace “zoki doken karewanta kenan dan bana gane nufin kallo” takalli Su Nana tace “kukuma bazaku wuce kufita ba kunga abin yara akeyi anan ne” dasauri yaran duk suka wuce suka fita Mom tabisu abaya fuuuu bakin ciki kaman tahadiye zuciya tamutu, bataso Du’a tasami miji irin Asad ba, yama akayi tasamu, inda tasan kara zuga Kaka akori Du’a datayi saiza tasami miji haka da wlh batayiba, gashi yasameta abudurwa zaizo yama kara santa ne, Du’a batai deserving irin jin dadin nan ba da yaranta suka dace, kamata yayi Du’a tamutu da kunci, wani irin lafiyayyen kunci takeji kaman tasama gidan gobara tahuta.

Ganin sun fita yasa Kaka ta tura kofan tarufe tareda saka sakata sanan tajuyo takalli Mami dake rikeda hannun Du’a dahar lokacin kuka take mara sauti tace “Zainab wani irin jarababben yaro kuka dauki yarinyar nan kuka auramawa eh? Uban wayagayamai haka akeyi? Yaran yanzu kwata kwata basusan al’ada ba, zamanin mu sai miji yafi sati biyu yana bareki dudda muna yan kauye, yau yay kadan saiya hakura, gobema yabareki kadan yahakura ahaka haryazo yabareki duka, amman wanan takadirin yaro dakuka dauki yarinya kuka bashi jibi abinda yamata saida ya bare yarinya tass saikace ance za’a rabashi da ita kokuma ana kokarin kwace mai ita, jibi yanda yarinya takoma, wlh idan haka yakeda jaraba saiya tsotse miki y’a tass yakare duk yarinya tabi tarame taki kiba haba dan Allah, dama daga ganinshi yanda yakeda uban kyan nan da tsayi haka yakeda uban jaraba iyye” itadai Mami tana zaune tana jinta takasa cewa uppan, dan masifan Kaka first class ne wlh.

Kallon Aisha dake tareda ita tayi tace “je falo dan nagaji da shegen benen man dakowani gida ake zubawa tunda nazo Abuja ban hutaba kafafuna sun kusan tsinkewa, je jakata kidauko ki kawomin kaman nasan abu haka zai faru nadebo sayuwan” ahankali tace “to Umma” sanan tawuce tabude kofan tafice, Kaka tajuya tana kallon Du’a din yanda take numfashi sama sama akan gadon tace “sannu kinji, Allah miki albarka, wanan wahalan dakikaga kinyi shi zaisa mijinki ya darajaki da daraja iyayenki dan sun baki tarbiya mai kyau kuma ya shaida hakan jiya da daddare, Allah miki albarka…” tsayarda maganan tayi sabida Aisha data shigo, da ledan sayuwan karba Kaka tayi ta duba tace “yauwa itace, ungo to, jeki kicin ki wanke ki tafasa ki juyo ki kawo uwarta tasata aciki kafin anjima da yamma wajen ya warke yadaina mata zafi bacci ma zatayi” wucewa Aisha tayi tafice da sauri dan itama Du’a tabata tausayi ita dama bata tsani Du’a ba kawai ba yanda zatayi da uwar tata ce, Allah yahorema Kaka masifa yaranta ma hakuri suke daita dan ansan tsufa ne.

Ko minti biyar bai dauketa ba ta tafasa tajuye ruwan tafito tazo takawo, Kaka tace “tashi Zainaba kije ki sirka, kekuma wuce kije kisamusu hannu kuyi duka aikace aikacen daya dace” wucewa tayi tafice itakuma Mami tashiga bayi dan hada ruwan, Kaka ma zaune adakin tace “ruwan yay zafi fa Zainab karya salapce” daga ciki Mami tace “to” gamawa tayi sanan tafito tazo gaban gadon, dago Du’a tayi ahankali tace “zomuje” wani irin fashewa tayi da kuka tace “wayyo Mami zan mutu” Kaka dake zaune tace “ke dalla chan raguwa tashi kitaka kafarki” da kyar Mami ta iya sauko da ita daga gadon amman Du’a takasa takawa tana wani irin kuka dayasa Mami taji tausayinta sosai, tasowa Kaka tayi tace “bari kiga natayaki” da taimakon Kaka dabawani karfin kirki ne da ita ba suka jata da kyar take ijiye kafan akasa tana mugun kuka, suna kaiwa gaban kofa saiga amai dasauri Kaka tace “yau na shiga uku, yaro zai kashemin jika eh? Ni wlh tambayata daya dan ubanshi Awdullahi Kitse ko eh ai haka Abban ku yacemin sunan shi, to dan ubanshi cemishi akayi za’a kwacemai itane? Zainab anya yaron nan basuda jinin jaraba adanginsu kuwa jibi yanda yamaida yarinya” itadai Mami batace komi ba saishafama Du’a baya datakeyi saida tagama aman sanan suka shiga da ita bayin, Kaka tafito tana kwalama Mom kira, shigowa dakin Mom tayi tanuna mata aman tace “yi sauri share aman nan ki gyara dakin nan kafin Zainaba tagama mata wanka” wani kallo Mom tama Kaka akufule, Kaka tace “bazaki yi bane nakira wata” akufule tajuya tace “bari na dauko tsintsiya tawuce tafita itakuma Kaka tasami kujera tazauna”.

Saida Mami taida gaske sanan tama Du’a lafiyayyen gashi dake nema ta sume mata, bayan tagama tamata wanka mai kyau sanan tafito da ita tana jikinta tanadan takawa ahankali, Kaka tai murmushi tace “kingani ba maganin nayi sosai yanzun nan jikin zai saketa, yanzu je bata kaya tasa akawo mata abinci taci zakiga sai bacci amman ma tagama yinshi da ikon Allah” wuce Mom dake shara Mami tayi suka shiga closet, shirya Du’a tayi cikin wani simple gown na atampa sabo fil tana kallon gashinta daya haukace, comb ta dauko ta taje mata gashin ahankali daya kara wani extra taushi sabida leman dake cikinshi sanan tasa ribbon tamata parking gashin nan tai dan kyan gani tai fayau kana ganinta kasan ta wahalu sanan tafito da ita Mom harta gama gyaran, Kaka tai murmushi tace “haba yanzu kika fito Amarya dake, oya kawomata abinci Zainab taci, da uban namomi” dan murmushi Mami tayi sanan tazaunar da ita ahankali da kyar ta zauna tanason ta karkace Kaka tace “ke zauna da kyau” zaman tayi da kyau tana nishi, fita Mami tayi ta debo abincin da Grandma ta dafamata da nama dayawa sanan tashigo ta ijiye agabanta kafin ta tsugunna tabude jakanta taciro maganin da Grandma tabada akawo mata, dasauri Kaka tace “me wanan”? “maganine Mama tabani nabata idan nazo” “toto bata tafara sha saita ci abincin” kaimata maganin baki Mami tayi tace “sha” ahankali tasha maganin dadi gadan yaji ya in cinta hakan yama bakinta dababu dadi sabida aman datayi dadi sosai tasha sanan ta ture, ijiye goran Mami tayi sanan tadau plate tana debo friedrice din zatakai bakinta wayan da Asad yabama Aneela takawo mata dakekan side drawer dake gefen Du’a yahau kara, kallon wayan Mami tayi batace komiba takai abincin bakin Du’a datai kaman bamatasan da wayan ba, ahankali tabude baki ta karba tana taunawa, har wayan ya katse aka kira na biyu still bata dauka ba kuma Mami batace mata kalaba akaro na uku ne da wayan ke ringing Kaka tace “waike dan gidanku ba mijinki ke kiranki ba” tai maganan tana kallon Du’a tace “dazun nan Aneela tashigo takawo miki wayan tace yace abaki, bazaki dauki wayan ba yaro duk yanachan yadamu, dauki wayan nan miskilan yarinya kawai” ahankali tasa hannunta tadauki wayan tana kallon screen din, Ammi tagani akai, ahankali tasa hannunta tadauki wayan takai kunnenta tana juyarda kanta gefe sabida Mami da Kaka batare datace komiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button