KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Karfe 7:30 Abba yasauko kasa Mami ce kadai a dinning tana hada kayan breakfast, bamataji tafiyanshi ba dan aiki take amman tayi mugun nisa a tunani, binta yayida kallo saikuma ya ijiye jakan aikinshi kan kujera yataka har zuwa dinning Mami bataji zuwan shi ba, hannunshi yakai yakama nata firgigit tafarka tareda juyowa bin fuskanta yayi da kallo idanunta ja da alamun tasha kuka, murmushi takakalomai sanan ahankali tace “ina kwana harka sauko” bai amsa gaisuwantaba yace “tunanin mekike”? kaman bazatai magana ba but ganin yanda ya tsareta da idanu yasa tace “tunani nake kodai mu aika Du’a wajen Mama nane” tsareta yayida mayun idanunshi ya dayasa kawai taji tacigaba da magana tace “Dadyn Hamad understand me kaga sabida Du’a gabaki daya gidan nan babu lpy, Nana tabani tausayi Allah kadai yasan what she is going through wlh is not easy karasa masoyinka, look at Mamansu ga Hamad, in order for peace to rain ni ina tunanin mukaita wajen Mama tai zamanta achan har Allah yasan yanda zaiyi da ita, daga saukanta kasa jiya jibi kalan trouble datajawo” murmushi yadan mata yace “fitanta so daya yajawo wanan matsalan idan muka kaita wani wajefa da bamanan, kinmanta komi ne tun yanzu”? Ajiyan zuciya tasauke takasa magana, murmushi yayi yace “bani abinci inada meeting by 8” gyadamai kai tayi tashiga serving nashi abinci, abincin yashiga ci wayanshi tafara kara ajiye cokalin abincin yayi sanan yatura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan ganin mai kirannashi saida kirjinshi yadan buga amman yadaure yakai wayan kunne zaiyi magana aka katse shi.

wani sharp muryan tsohuwa ce kemagana ta wayan. “nasan yau litinin ko ubanme kakeyi kowani kalan aiyyukane kakeyi kabarsu Shafi’u ka tattaro iyalinka tatas banda wanan yar Aljanun kutaho Ikara yanzun nan” tana maganan ta katse, ahankali yazame wayan daga kunnenshi yay jimmm yana kallon Mami da ahankali tace “Kaka ce?” gyadamata kai yayi yace ” jeki shirya yara kowa yafasa zuwa school Ikara zamu yanzu” bude kofa akayi Ahmad yashigo yanasanye da kayan sojoji kafinma ya gaida Abba Abba yace “Ahmad get ready we are going to Ikara” shi kanshi Hamad din baikara fadin wani abubu, saukowa sukaga Mum tayi taci gayu itada yaranta da Nana da idanunta sukai ja sosai tace “mudai mun shirya” ahankali Mami tabi ta gefenta tai sama kaman zata shiga dakinta saikuma tabude dakinsu Du’a ta shiga, zaune taga Du’a kan gado, duka kumburin da fuskanta yayi sun sabe dan dama nan da nan ciwo ke warke wa ajikinta sai idanunta dasuka kumbura sosai, ganin Mami tashigo dakin yasa tabude baki zatamai Mami magana dasauri Mami tajuya tafita dakinta tashiga tadauki hijabi sanan ta tattaro kansu Muhammad da Aneela suka fito, a falo suka sami kowa Abba yace “mutafi” juyawa yayi yakalli Uwani data fito daga kitchen yace “ki kulada Du’a ki kaimata abinci sama zamuje kauyen Ikara” gyadamai kai tayi tace “Allah kiyaye hanya agaida Hajiya” fita dukansu sukayi Mami tadan juyo hada Pido tayida Du’a data fito daga dakinsu ta labe asama idanunta sun cikoda kwalla, Sakai tayi tafice dasauri.

???? KYAWUNA JARABTA ????

          ✍️ M SHAKUR 

Free page
EPISODE 7️⃣
Tashi tayi ahankali tawuce cikin dakinsu bathroom tashiga wanka tayi da ruwa mai zafi sosai hakan yasa taji duk wani ciwon jikin datake ya watsake sanan tadauro alwala tafito daureda towel, maita shafa ajikinta sanan tabude wardrobe din, wani dogon riga kawai taciro na atampa ja ta shirya cikinshi sanan tasaka hijabi tai salla, zama tayi wajen kan dadduma hakanan kawai gabanta yake fadi maisa tunda ta taso tafara wayau rayuwanta kecikin kunci eh? Maisa ita kadaice problem din gidan nan, Kakanta bata sonta sabida itama tadaina zuwa gidan danta Abban su, Abba baya sonta kawai ijiyeta yake sabida bazai iya koran y’arda ya haifa ba, Mami ma kaman kunya takeji ace ta haifeta, gabaki dayan mutanen datasani aduniyan nan mutum biyu ne tasan kawai suna sonta Nene Maman Mami wacce ita dinma tun tana yarinya ne Mami ke daukansu suje su gaidata tunda Abba yahanata fita ko’ina bata kara zuwa gidan ba saidai ta aikomata da kayan kwalama idan Mami dasu Aneela sunje kokuma musamman takira Mami taita mata masifa sanan tasaka Mami tabata waya su gaisa da Nene.

Maisa iyayenta da yanuwanta basa sonta? duk sabida wanan kamannin nata to ita tayi kanta ita tayi kanta eh? share hawayenta tayida sauri jin anbude kofan dakinsu, Uwani ce tashigo tace “kin idar kyakkyawan gidan nan, zokiyi karin safe” tashi tayi ahankali tazo inda Uwani ke nunamata, zama tayi Uwani ta ijiye tray abincin agabanta tace “oya ci abincin ki, Allah zai sakamiki, Nana takamaki tadinga jibga danma baki iya rashin kunya bane dakin biyemata kunyi damben da kyau, yi breakfast kyakkyawa” all maganan nan da Uwani keyi bata kalleta ba saida tai maganan karshe sanan tadagokai ta kalleta lumshe ido tayi tabude cikin yar muryanta tace “dan Allah dagaske ni kyakkyawace” zama Uwani tayi akasa kusada ita tana kara kallonta opportunity kaman daman abinda take jira kenan tace “ai wlh Du’a kinada bala’in kyau da duk yan nan gidan babu mai kyanki, kina kama da masuyin film din kasan waje, ai saisa yan uwanki kejin haushin ki sabida kin fisu kyau ga wanda Nana zata aura nan jiya daga ganinki yardage keyakeso, jiya ina kitchen ina jinsu wlh harda kukanshi wiwi sabida ke, ki godema Allah kawai” murya chan kasa tace “ni banson kyau nafison nazama kaman kowa sabida yan uwana da kowa su soni, banson yanda nake rayuwa ni kadai ban iya komiba” dasauri Uwani tace “ko yanzu ma suna sonki ingayamiki kawai bakin ciki ke hanasu nunawa” shiru tayi tana kallon abincin batareda ta tababa, Uwani dabata gaji da kallonta ba tace “yanzu dasuke kulleki adaki haka basuso ki sami naki saurayin kiyi soyayya kiyi aure ne” dagokai tayi takafe Uwani da idanu batare datace komiba, dan murmushi Uwani tayi tace “tashi muje falo abinmu yau mu kadai agida mu sakata mu wala”.

“Salamu Alaykum” sukaji an kwada sallama dasauri daga itahar Uwani suka ware ido, Uwani tace “tashi muje falo muji mene mai gadi kenema wajenmu” tai maganan tana daukan tray abincin ta, tashi tayi ahankali sanan tabi bayan Uwani suka sauka falo, abincin ta ijiye mata akan table sanan takalleta yanda take tsaye kusada Uwanin tace “oya zauna kifaracin abincin bari na sauka naji maisa Bala mai gadi kemana sallama ina zuwa” gyadamata kai tayi tazauna ahankali sanan tadauki plate din nama tadaura akan jikinta tafaraci, bude kofa Uwani tayi mai gadin su tagani tareda Muhsin dake sanye da wasu hadaddun kananun kaya masu bala’in kyau yasaka glass a ido baki, ware ido tayi zatai magana dasauri mai gadi yasa hannunshi akan lips dinta alamun tayi shiru kartace wani abu, sanan ya matsa ta gefenta yajawo kofan falon yarufe batare da Du’a ta ganshi ba danta gefe ya tsaya yajuyo yakalli Muhsin yace “minti daya yallabai bari nai magana da ita” gyadamai kai Muhsin yayi tareda tabe baki shikuma ya yafito Uwani alamun tazo, binshi tayida saurin zuwa gefen daya tsaya tanason taji me wanan Muhsin din dataji anyi baran baran dasu jiya kenema kuma agidan nan, tace “me wanan keyi agidan nan Bala”? dasauri Bala Maigadi yace “yanda kika ganshi haka nima naganshi, ashe tun asuba yana anguwan nan akan idanunshi su Alhaji suka tafi Ikara dazu” dasauri tazaro idanu tace “yoni nabani, daga ganin sarkin fawa waisai miya tayi zaki, dagaske yakewai Du’a yakeso, tome yazo yi yanzu”? dasauri Bala Maigadi yace “soyake mudan bashi dama yaga Du’a ta hanyar barin gidan nan na minti talatin kadai” zaro idanu Uwani tayi tace “kai Bala hauka kake eh, ba amananta aka barmana ba, me zamu barshi dagashi sai ita yarinyar dakasan babu abinda ta i…….” kasa karasa maganan tayi sabida wata bakar jakan Viva bag dataga ya tsugunna yadauka sanan yazo gabanta bude mata ledan yayi wani irin zaro idanunta datayi zaka dauka idanun zasu fadi kasa ne sabida uban kudin datagani cikin ledan, dasauri yace “miliyan biyar ne anan inhar mukamai abinda yakeso tamuce halak malak, zandauki miliyan uku nabaki biyu, aikin shekara nawa zakiyi agidan nan baki sami miliyan biyu ba duka duka albashin naki da dubu goma sha biyar ne, arziki na kiranmu jibi uban kudi haka namune kawai idan muka bama mutum minti talatin kachal, kina ciki ko baki ciki?” dawani irin sauri ta hadiye yawu harsaida yay gut tace “ina ciki wlh Bala” murmushi yayi yace “bari nakai kudin na boye adakin saimu tafi” gyadamai kai tayi yawuce itakuma tadawo inda Muhsin yake tsaye tace “yallabai ko awa dayanema kayi bakada matsala damu, jiyama ingayamaka saida Nana tamata dan banzan duka su basusan shi so Allah kesawa ba, ga yarinyar danya jagab nunan inuwa bamatasan Yaya ake dambe ba, bafata fita bamatasan Yaya zafin rana yakeba” daidai lokacin Maigadi ya iso yakalleta yace “mutafi” gyadamai kai tayi sanan ta kalli Muhsin tace “tana zaune a falo tanacin abinci, Allah baka sa’a” yatsine fuska yayi dan matan disgust him sosai sanan yajuya yana kallonsu suka wuce suka fita, Bala Maigadi yasa key tawaje suka wuce abinsu suka zauna kan wani benci dake facing gidan ta dayan bangaren hanya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button