KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

5️⃣6️⃣

Da Sallama tashiga dakin zaune taga Du’a akan gadon, daga ita sai wata yar jan riga data tsayamata acinya, anmata parking kalabanta tai wani irin simple kyau tana daddanna wayanta da babu wani abun kirkin datakeyi dashi, ganin Rahima yasa tai wani kalan murmushi tace “Ya Rahima kinzo good morning” karasowa tayi tazauna abakin gadon tana kallon kafan nata that looks good tace “sannu ya jikinki? Ya kafan yadena zugin” gyadamata kai tayi ahankali batare datai magana ba, kallonta Rahima tayi Du’a is really a definition of innocence, zama tayi kusada ita ta jingina da bangon gado tace “kinsan gobe Ammi zata tafi Dubai za’a je ahado akwatin ki, yaushe zaki fitomana da anko yanzu fa yau bikin ku saura sati uku da kwana shidda” kallonta Du’a tayi gabanta nafaduwa kaman bazata ce komiba saikuma ahankali tace “wai dagaske Ammi take? Ni banson Ya As…..” kaman wacce ta tuna abu saitai shiru tana kallon Rahima dake kallonta gabanta nafaduwa, murmushi Rahima tayi saikuma ta tashi takama hannunta tarike tace “Du’a kinsan ni na yarinya bace ko I am 27 yanzu, inaso nagama school ne this year da tuni mai aure nima, inaso ki gayamin gaskiya because I really want to help u tsakani ga Allah, I told you zan zame miki sister dabaki taba samuba in your life, and duk wata magana da zamuyi it will be tsakanin mu me and u har abada, I want to help u so tell me now how did everything happen har kika auri Ya Asad bayan baki sonshi? I promise bazan fadamai ba or anybody” tunda Rahima ke maganan take kallonta hakanan taji ta yarda da ita itama kuma tanason tagayama wani labarin koya rage nauyi daya mata azuciya, murya chan kasa tace “Ya Rahima ni wlh banason Ya Asad, wlh ko mugun tsoron shi nakeji, ko yanzu ma sabida nasan agidane akwai Grandma da kowa bazai iya min mugunta ba ko yaci zaluna, amman idan akai bikin ba barin gida akeyi ba za’a kaini gidanshi ko”? ta tambayi Rahima, gyadamata kai Rahima tayi hakan yasa tace “wlh ni banaso, Ya Asad baida kirki mugu ne, shi yace ince ina sonshi ni bana sonshi ko kadan……” gabaki daya tabama Rahima labarin yanda akai auren, bakaramin mamaki tayiba, from what she understands a labarin nan Ya Asad na mugun son Du’a amman shegen halinshi na zurfin ciki, da jan aji da mugunta boyewa yake yana nunama mutane kaman ana tursasashi ne aiko yanzu zai gane, gani yanda Rahima ke murmushi yasa Du’a tace “why are you smiling” girgixa mata kai Rahima tayi tace “babu komi, kawai mamakin rashin wayonki nake, all I will tell you is Ya Asad na bala’in sonki and kibari ayi bikinku karkice komi kinji Du’a” gyadamata kai tayi idanunta sun kawo kwalla, dan hararanta Rahima tayi tace “I will teach u yanda zaki handling Ya Asad cikin ruwan sanyi kawo kunnenki kiji” dasauri Du’a takai kunnenta, magana Rahima tashiga mata whispering, dasauri tadago kanta takalleta idanunta awaje gabanta nafaduwa tace “Ya Rahima no bazan iyaba wlh, tsoro nakeji” hararanta Rahima tayi tace “bakiso ki chanza ko kinfison mutane koda yaushe nacin zalinki ana taking advantage of you, wlh bazai miki komiba yana sonki zaki gani kinji” gyadamata kai tayi jikinta yay sanyi, Rahima tai murmushi tacigaba da gayamata maganganu akunne daga wanda Du’a zatai rejecting sai wanda zatayi kaman zata fashe da kuka saida Grandma tazo takadata kan taje tai wanka sutafi kan Ammi takira ana neman ta sanan ta tafi ranta fess takasa daina mamaki bata taba ganin takadirin mutum irin Ya Asad ba, saisa kowa ke cemai mai bakin hali, cikin ruwan sanyi yama Du’a wayau ya aure ita banzan Du’a bama tasani ba batasan yamata wayau ya aureta bane sai uban tsoron shi datakeji kaman wani ma’aikata, kiri kiri yasa yarinya tai rashin kunya tace ita aure takeso shi takeso shiko yana gida yana cincin magani Ammi kullum cikin lallabashi take yanayi kaman forcing nashi akayi ya aureta duk basusan yaron su yay lakur shiya hada komi ba Kai Ya Asad nacire maka hula awanan act din, Rahima tafadi tana murmushi, Ya Asad Ya Asad shegen guy ne wlh, amman yanzu duhun shi yacika, bazai karama yarinya wayau ba wlh, dan wlh saita zuga Du’a tasa yamugun susuce ya rame I will make Du’a beat u in your own game, niko nace to masu karatu kuna ganin Mr Asad Abdullahi Kitse is beatable kuwa???? Let the show begins.

Bai kara dawowa gidan ba saida daddare wuraren karfe tara na dare, koda yashigo gidan babu kowa a falo hakan yasa yay sama, ahankali yay knocking dakinta tareda budewa yashiga ciki tana zaune kan gado waya akunnenta tana murmushi, kallo daya tamai tadauke kai tana murmushi wanda da alamu awaya ne take murmushin, ahankali cikin yar muryanta tace “ai yama dena zafi yanzu ciwon dakace haka” hakanan yaji kirjinshi yabada dumm! Dakace haka! yamaimaita aranshi saikuma yakalleta, hannunta daya yaga tadaura akan fuskanta tana murmushi tace “ni ba baby bane kadena cemin baby I am 22 fa” tawani turo baki sosai, hakanan yaji kafarshi yasoma rawa yana shaking zuciyanshi nawani irin tafarfasa yama kasa tafiya tsabagen yanda zuciyanshi ke tafarfasa yana kallonta, dariya yaga tahauyi sosai taja fito ta kankame ashagwabe tace “ohh’ohh ni sainakai 25yrs ko 27yrs zanyi aure” kulewa yaji idanunshi sunyi rufff yawani tako zuwa gabanta kawai mutum taji ya kanta yawani irin fizge wayan dake kunnenta yawani chill wayan bango wayan ya tarwatse da hannunshi biyu yasa yawani jawo gaban riganta ya mikarda ita tsaye shaketa yayi da rigan idanunshi sunyi jajir yace “da ubanwa kike waya kina matasayin my wife ha” rawa sosai jikinta yafara kafanta yashiga rawa tana zaro idanu tana kallonshi yanda taga yayi yasa taji zuciyanta kaman zai fashe sabida tsoro tama kasa magana, cikin wani irin murya kaman wanda aljanu yashiga yace “so u are calling a man kina gayamai kinji ciwo lallashinki ma yake kinamai shagwaba eh, kinsan akwai aurena akanki u want me to kill you” bubbuga hannunshi take alamun yasaketa amman ina yakasa sakinta, tuna abinda Rahima ta gayamata tayi da kyar tadaure ganin tana nema tamutu tace “to ai ba aure mukayiba nika sakenmin wuya, I am nobody’s wife” wani irin rawa hannunshi suka shigayi yana kallonta kungane irin maganan nan dazakajita daga bakin wanda baka taba expecting ba hakan yasa kaji duk wani energy na jikinka yay draining yakare that’s the same situation da Asad yashiga baisan lokacin daya saketa ba hannunshi narawa sosai, tari tashigayi tana kuka idanunta sunyi jajir ta duka tana Tari, Asad yadade yana kallonta jikinshi still rawa yake sanan cikin wata irin kakkausar murya yace “what did u just say”? daurewa tayi ta tashi ahankali tana shafa wuyanta takalleshi tsayarda kukan datakeyi tayi tace “nace niba matanka bane, I am not your wife, wanan auren dazuwa masallacin dakukayi aka daura everything is fake ai taimakona kayi sabida karsu Abba su tafi dani, kuma sukazo basu tafi dani ba ba shikenan ba, ni bazan taba aurenka ba, bazan zauna dakai ba, ni bana sonka kaima baka sona Dad yace rokonka Ammi tayi ka yarda, ni wlh baran aureka ba” Asad is someone dazata iya cewa bata taba iya tantance yanayin fuskanshi ba but yau zata iya fassara abinda tagani a idanunshi da fear, sosai jikinshi yahau bari yana kallonta yanda take kuka tsaye agabanshi tana bubbuga lafiyayyen kafanta akasa cikeda rigima, gyadakai yayi ahankali yay wajen wayanta daya jefa da bango dagata yayi ganin ta runtse abaya da gaba amman screen din na haske still yasa ya tattaka wayan kaman ba kudi yasa yasayeta ba saida yaga screen din yadena haske sanan yadago yajuyo yakalleta har lokacin kuka take tana kallonshi kaman ba Du’a dake tsoronshi ba yawuce yabude kofa yafice, cigaba da kukan tayi tana shafa wuyanta sanan ahankali tahau kan gado tana share fuskanta tana mamaki daman zata iya dama zata iya? Abin ya bala’in bata mamaki, saikuma ahankali takalli wayan tana cikin waya daya Hamad, dazun nan fa Grandma ta shigo takarbi number shi daga hannun Grandma ta kirashi kuma ganin Asad yasa duk tai abubuwan nan, wani kalan murmushi tasaki sanan ahankali ta lumshe ido tana jiran gobe tayi tabama Rahima labari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button