KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Gida yacika fal da matan anguwan ana salati ana sallallami, Bala Maigadi har zufa yake yana zura mata igiya yana ihu yace “Du’a ko yayane kifito da hannunki sama ki chapke igiyan zamu jawoki waje” wata mata dake kiran mijinta awaya tace “wanda yafada ruwa fa bayajin magana nataba fadawa rijiya, ji zakiyi ruwan na shakeki, ayita salati kawai idan tanada kwaran kwana zakuga Allah zai kawo yanda za’a ciro ta, Baban Nana nake kirafa ya iya ruwa kuma shagon shi nabaki titi amman baya dauka”……….

THIS BOOK IS 500 U CAN PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK SAIKI TUROMIN EVIDENCE OF PAYMENT TA WATSAPP NUMBER 07012181461

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

           ✍️ M SHAKUR 

Dan chatting dina ni M Shakur directly click on this link
wa.me/+2347012181461

Free page
EPISODE 9️⃣
Wata latest AMG Benz ne fara ta doso cikin anguwan tana tafiya ahankali sabida tudu da kwarin anguwan yasa motan bazata iya tafiya dagudu ba, mutane biyune acikin motar, wani farin guy ne bala’in kyakkyawa da akalla zaikai 33yrs ko 32 yana sanye da jumper na wani classic USA yard dakenan da bala’in taushi blue, ba’ama dinki aiki ba amman yahadu yana tuki da hannu daya yanashan horse power da dayan hannun, saikuma wani black guy hadadden gaske dakeda kakkauran jiki lebenshi pink sosai yana zaune abaya da akalla zasuyi agemate damai tukin, yana sanye da suit shima mai ruwan toka da necktie awuyanshi yadaura Mac book kan cinyanshi yana dadannawa, yanada wani irin cikan coily gashi akanshi dasuka nannade sosai yayi kama da black somalian guys sosai looking damn sexy and hot, irin definition of classic young rich guy dinnan. “wai dagaske ka maidani drivern ka ko Asad” dan dagokai yayi yakalleshi saikuma yamaida kanshi kan laptop din yacigaba da abinda yakeyi batare daya kulashi ba, dan tsaki mai tukin yayi murya chan kasa yace “mtsww this guy piss me off kodayaushe” batare daya kalleshi ba har lokacin kanshi nakan system din dayake aiki akai yace “and he heard u loud and clear Sharif” dan dariya direban da aka kirada Sharif yayi yadan waigo yakallehshi ganin hankalin hi nakan aikin dayake yasa yajuya yamaida hankalinshi kan hanya daidai lokacin kuma yataka wani irin mahaukacin burki da saida yasa Asad dake baya kanshi yabugu da kujera laptop dinshi yafadi akasa dasauri yadago kanshi danshi yadaukama wani abu suka taka suna neman suyi accident ne Sharif yaci burki kawai dukansu biyu sukaga Uwani gaban motansu takife kanta akan glass din motan tana kuka sosai tahade hannaye, kallonshi Sharif yayi dasauri Asad din yace “is she a kidnapper”? Dasauri Sharif yace “how am I suppose to know eh? Ammi saida tace inzo da security indaukeka kace kai bakason azo daukanka da kowa, yanzu in kidnappers ne Yaya zamuyi”? daidai lokacin tarinmata kusan su shidda suka fito daga gidansu Du’a da gate kenan abude, Babban cikinsu ne ta bubbuga motan dan tinted class ne tagefe dasauri Asad yace “don’t open the door” bude motan Sharif yayi yafita ganin matan aure kamilallu, Matar tace “Malam dan Allah kataimaka mana kakap anguwan nan babu maza yarinya kuma tafada rijiya kusan minti takwas da rabi kenan bamu samu nasaran ciro ta ba kuma iyayenta basa nan sunje kauyen su chan Ikara dan Allah kataimaka mana maganan rai ake anan” shiru Sharif yayi yana kallonsu saikuma yakalli gidan dasuke nunamai yanda aka taru yara da manya gawasu na kuka dan abin abin tausayi yasa yace “Ina zuwa” shiga motan yayi dasauri yakalli Asad dake binshi da kallo yana jiran bayani yace “Asad zomuje muyi taimako” dasauri Asad yace “taimakon mene” dasauri yace “yarinya ce tafada rijiya and parents dinta are not around tayi about 8min a rijiyan kuma kasan ni ban iya ruwaba pls muje kacirota” Wani kalan matsiyacin kallo Asad yamai yace “you must be joking, na iya ruwa yes na iya ruwa kataba ganin na shiga rijiya ne? I don’t think namataba ganin rijiya, common key this car mubace daga anguwan nan” dasauri Sharif yace “common Asad maganan rai akefa anan what if yarinya tamutu right before our eyes when munada chance na saving life dinta mezamu fadama God” maida kanshi yayi jikin kujera yace “sannu superman, tunda kanada relation ne da yarinya ai kaje kai saving nata nidai count me out” dasauri Sharif dake kallonshi cikeda mamaki yace “haka kace” tabe baki yayi yace “saikuma kayi” yay maganan yana lumshe ido danshi bacci ma yakeji fita daga motan Sharif yayi yakalli matan yace “muje ingani” dasauri daga Uwani har sauran matan sukai gidansu Du’a tareda Sharif din dake biyeda su, almost 1min yayi idanunshi a lumshe saikuma yabude idanunshi dasauri yajuya yakalli gate din su Du’a, wani irin banzan tsaki yayi sanan yabude kofan bayan yafito yana maida kofan yarufe yace “you are messing with my mind Sherif” sanan yawuce ahankali yabisu, kafanshi nadama yasa yashiga gidan wani irin sanyi yaji yay wani irin cringing acikin bones nashi dasauri ya tsaya chak yanabin duka gidan da kallo yanda yaga duka matan gidan sun juyo suna kallonshi kaman sunga wani hero ko celebrity na movie, juyawa yayi dasauri zai fice daga Gate din yaji muryan Sharif yace “yauwa gashinan yazo, the well is here Asad” dasauri yajuyo yakalli Sherif din dake gaban rijiyan kusada Bala direba yana nunamai rijiyan, wani kallo yama Sherif irin zamu ganmu dinnan sanan yashigo cikin gidan zuwa gaban rijiyan, necktie dinshi yacire yabama Sharif din yakarba, sanan yacire takalminshi dakuma jacket dinshi, igiyan dayagani hannun Bala ne ya karba wani irin dauri yama igiyan a waist dinshi da sanan ya kallesu yace “zan shiga ciki idan Nagano ta zan muku sign ku jawota” duka gyadamai kai akayi, juyawa yayi yakalli rijiyan baitaba shiga rijiya ba, kallon Sharif yayi dake kallonshi irin kallon nan na u caused all this sanan yay wani irin tsalle yafada rijiyan jikake tsundum.!!!

Leka rijiyan dukansu sukayi Bala yace “kace ya iya ruwa sosai ko” gyadamai kai Sharif da kirjinshi ke dukan uku uku yayi yace “eh ya iya amman baitaba shiga rijiya ba” wani irin salati duka gidan aka dauka, wata mata cikinsu takalli Bala tace “incedai ka kira mahaifinta ka sanarda su inma barin ikaran nan subaro sutaho fa dan wanan yarinyar inhar ta rayu to Allah yace kawai kwanan ta nagaba ne” ahankali Bala yace “nariga na sanar dashi” “jama’a Qulhuwallahu kafa bakwai” nan aka fara karatu fa, ganin yayi kusan 2min a ruwan ruwan ma yadena motsi yasa dasauri Sharif ya tsugunna yana leka rijiyan. “Asad Asad can u hear me are you okay? Asad” kana ganinshi kasan hankalinshi atashe yake, kusan 20sec dagama kiranshi saigashi yawani bullo da kanshi daga ruwan yay ihu yace “I got her!” dasauri daga Sharif har duka yan gidan sukahau hamdala, dasauri Sharif yace “what about u are you okay Asad” yana kokarin janyo Du’a kanta yafito daga ruwan gabaki daya yace “we will talk about that when am up there” cirokanta yayi daga ruwan sanan yadaura kanta akirjinshi ya rungumeta ahaka, igiyan dake waist dinshi ya shiga warwarewa sanan yadaura shi kan waist dinta duk acikin ruwan dan kansu ne kawai ke sama sanan yace “Sharif I don’t know if she’s still alive but she is unconscious, na daura igiya a waist dinta, ni zan dingabin matattakala while am holding her kukuma kunajan igiyan waje am I clear” dasauri Sharif yace “yes Asad sanan yatashi dasauri yarike igiyan tagaban Bala yakama ta bayanshi sanan yacilla matan ragowan igiyan yace kuyi layi ku kama igiyan mujawosu waje, duka rike wa sukayi Sharif yace “give us go ahead we are read Asad” hawa matakala daya Asad yayi yana rungume da ita har lokacin sanan yadago kanshi yakalli sama yace “pull us Sharif” jawo igiyan suka shiga yi yana rikeda ita yanabin matattakala har sukakai sama Tsugunnawa Sharif yayi yamikamai hannu da taimakonsu yafito rikeda Du’a akan kafadan shi sanan ahankali yacirota daga kafadarshi ya shinfidar da ita akasa sai alokacin yamaga fuskarta yanda yake kallonta haka kowadake compound dinan ke kallonta, Uwani ce ta rarrafo tana kuka sosai tace “mun shiga uku mun lalace Bala ta mutu jibi yanda takara haske, Innalillahi wa innailaihi raji’un” ahankali Sharif dake gefen Asad yace “Asad tamutu ne”? “I dont know” Asad yabashi amsa atakaice yana dauke idanunshi daga kanta, yace “let’s go” dasauri Sharif yace “check ko she’s alive common Asad, are you this heartless” wani mugun kallo yama Sharif zaiyi magana wata yar tsohuwan dake cikinsu tace “bawan Allah matsamata ciki in ruwa tafito tanada rai idan baifi
to ba ba rai” kaman bazaiyi ba saikuma ya matsa inda take kwance dasauri Uwani ta matsa hannunta ya kalla saikuma yakai hannunshi yakama hannunta yana duba pulse dinta bai sami pulse a hannun ba sai uban sanyi da hannunta yayi kaman kan kara, hakan yasa ya ijiye hannun yakai yatsunshi biyu kan jijiyan dake gefen wuya anan yasami wani very very weak pulse dasauri yazare hannunshi yace “she’s alive” “Alhamdulillahi Rabbil Alameen” yan gidan suka fadi hannayenshi biyu yasa akan cikinta yashiga matse mata cikin da karfi yana kallon fuskanta sai chan ya tsaya yakalli Uwani dake gefensu tana kukan murna ganin tana raye yace “bude bakinta kihura mata iska aciki” dasauri Uwani tazo bude bakinta tayi tahura iska ciki yace “ya isa” daina wa tayi shikuma yacigaba da matsa mata cikin, ruwan gashinshi nabin fuskanshi har zuwa hanci, amman shiru saida yasa Uwani tahura mata iska harsau uku amman shiru hakan yasa Sharif yace “common kai kasan komk nakan harkan ruwa, ka asalin this thing ba kahura mata iskan dakanka mana, let’s help the poor girl” ko kallon Sharif baiyiba yakalli Uwani yace “sake huramata” dasauri tsohuwan tace “bawan Allah kayakuri dan Allah kataimaka mata tafarfado hankalinmu duk ya kwanta inda mahaifiyar ta na nan datakusan mutuwa dan Allah kataimakama marainiyan yarinyar nan da iyayenta basu anan” kaman ya kurma ihu yakeji amman yadai daure da kyar dan matsowa wajen kanta yayi yana kallon pink lips da dan karamin bakinta dazai daura nashi akai, kaman wanda ke tsoro yakai bakinshi gently yana kallon fuskanta yadaura kan nata ko mugun sanyin da jikinta yayine yake shiga nashi oho jiyayi jikinshi yadauki wani mugun sanyi daurewa yayi ahankali yahuramata iskan bakinshi zuwa cikin nata kaman wani magic tarrrr yaga tabude idanunta dasukai wani masifan haske sai cikin nashi suna kallon juna saikuma wani uban tari datayi white tana kallonshi duka ruwan daya taho daga bakinta sai nashi dawani irin mugun sauri yacire bakinshi daga nata yaciro kanshi yajuya yana wani irin kakarin amai babuma wanda ya lurada shi sai wani irin ihu da hamdala da duka mutane keyi na ta farfado tana uban aman ruwa aka zagayeta, ganin yakasa aman yasa ya yunkura zai tashi jiyayi an kama hannunshi gam dasauri yajuyo yakalli hannunshi gani yayi Du’a dake amai sosai tarike hannunshi gam tana kallonshi har lokacin da idanun nan nata da kaman bata hayyacinta, dasauri yajanye idanunshi dagakan hannun yakalli fuskanta idanunta kadan suka budu amman shi take kallo saikuma jikinta yafara bari tana kakkarwa, fizge hannunshi yayi daga nata dasauri yana yarfewa danjjn hannun yayi kaman ya sandare yakalli Uwani dake kanta yace “ku chanza mata kaya ku rufeta shes cold a kaita asibiti” sanan yawuce wanshi batare daya kalli Sharif ba yace “wlh nakai mota baka zona saidai kadawo gida da kafa” dawani irin gudu Sharif yatashi yabishi abaya yana kara waigen Du’a da aka zagaye, mota suka shiga Sharif yaja motan da gudu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button