KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Wani flat suka shiga kayataccen falo ne da kujera ke ciki sai lallausan carpet da aka rufe ko ina na kasan dakin dashi sabida sanyi sai wani tsohon dattijo da akalla zaikai shekara 90 ko fin haka ke zaune kan wata kujera mai ultra taushi wacce kanagani kasan musamman sabida shi akayita yana zaune gashinan tsaf tsaf sai wani bakin glasses a idanunshi hannunshi rikeda ayaba yanaci da aka yayyankamai awani clean bowl, tunda yashigo gidan this is the first time yayi kayataccen murmushi yace “Dadda” da sauri tsohon dake tauna ayaba abaki ya tsaya chak saikuma da sauri yasake gyara zaman glass dinshi a idanunshi yakalli kofa sabida haske kofa yasa baiganesu ba cikin muryanshi ta tsufa da still kuma take fitada kyau yace “amaida kofan arufe” dasauri Sharif dake hadiye dariyan shi yamaida kofan yarufe hakan yabashi daman ganinsu ahankali yanuna Asad da yatsa yace “Sharif Asad nake gani” dawani irin sauri Asad yaje bowl din jikinshi yacire ya ijiye agefe sanan yawani rungume kakanshi tsam tsam yace “Dadda kai kadai nayi missing wlh, kaga Sharif tunda na shigo garin nan yake batamin rai Dadda” washe bakinshi da hakora sun fiffita yayi yace “to wlh su kiyayeni aina gayamusu duk wanda yataba Asad toni yataba kona mutu bazan yafemai ba” dariya sukayi duka Sharif yazo yace “Dadda kai bazakamai fadaba mugun halinshi yay yawa” hannu yamika ya kamo hannun Sharif yace “banace ku hada kanku ba kome yayi kamai hakuri, shi hali zanen dutse ne ko mutum zai rabu dashi saidai da kadan kadan, halin mahaifinshi Abdullahi yagado sak” kankameshi sosai Asad yayi yace “i love you Dadda na”

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

      ✍️ M SHAKUR 

wa.me/+2347012181461

Free page
EPISODE 1️⃣1️⃣
Da taimakon Matan dake compound din aka kwasheta akai falonsu da ita jikinta na mugun barin sanyi daidai lokacin motarsu Abba tai parking akofar gida wani irin azababben gudu sukayi dayake Hamad shiya tukasu da Mami da Abba ne kadai sauran duk sun barsu awajen Kaka achan Ikara, dawani irin gudu Mami tashigo gidan idanunta sunyi jajir, this is the first time data iya cire koma meke sata yima yarta wani kala tanuna tsantsan damuwa da so akan yartata tadubi matan tace “ancirota ancirota daga rijiyan? jama’a kufadamin ina y’ata Du’a, ina take”? Tai maganan tana kama kirjinta dataji yana wani irin bugawa tsabagen fargaba, daki matan gidan suka nunamata sukace “tana daki, yanzun nan aka shiga da ita ciki” dawani irin gudu Mami tai flat dinsu Abba ma dayashigo yabita dasauri Hamad shima dagudu yabisu da shine last na shigowa sabida parking mota dayake, tana shiga falo taga some few mata akan Du’a dahar lokacin take ajike akasa tana wani irin rawan sanyi hakoranta na karkar kar kaman ana hada kacha ana gwarasu, wani irin ihu Mami tayi. “Du’a! Du’a” yanda Mami tayi baya kaman zata sume yasa dasauri Abba yatareta yace “calm down” juyawa Matan dakin sukayi suka fice ganin maigida, daidai Uwani tasauko kasa dawasu kaya da bargo daban daban a hannunta, tashi tayi daga jikin Abba dasauri takarasa wajen Uwani, karban kayan hannunta tayi sanan takoma inda take, dagota tayi dasauri takalli Hamad tace “Hamad bani wuka” dagudu yay kitchen wuka yadauko yafito yaga rigan jikinta Mami tayi Abba da Hamad duk suka juyar dakai chanza mata kayan Mami tayi agurguje sanan tawani irin rungume yarinyar dasauri tarufeta da bargo tana kuka. “I am sorry Du’a sorry” matsowa wajen Abba yayi hannunshi yakai yadaura kan wuyanta jin sanyi yasa yakalli Uwani yace “jeki hado garwashi” sanan yaciro hannun Du’a daya yana murza tafi hannun dasauri Hamad shima yazo yakama dayan hannunta yana murzawa duk tana jikin Mami data kankameta sosai, ba’a wani dauki lokaci ba saiga Uwani da uban rushi a kasko dan makota taje tasamo, ajiye wa sukai agabanta still suna murza hannunta ahaka suka samu kadan kadan tarage rawan sanyin hartazo tada ina gabaki daya kallon fuskanta tayi yanda idanunta ke a lumshe shafa fuskanta Mami tayi ahankali takira sunanta.

“Du’a” bude idanunta kadan tayi saikuma tabudesu gabaki daya tana kallon fuskan Mami, dasauri Hamad yataso kansu yana kallonta yace “Du’a taya kika fada rijiya”?zubamishi idanu tayi shima tana kallonshi saikuma ahankali tamaida idanun kan Mami tana kallonta asanyaye, Mami hakanan taji jikinta yay sanyi sabida yanda yarinyar ke kallonta, hawaye taga sun zulalo ta gefen idanunta kafin ahankali tabude bakinta cikin muryanta dabata fita sosai tace “maisa aka cironi daga rijiyan eh? Mami inaso namutu kowa yahuta saisa kodana fada saidai nadinga lumawa cikin ruwan ko tsoro daya banji ba saima kwanciyan hankali danaji domin ajalina yazo, Mami naso namutu sabida kihuta hankalinki ya kwanta kince tundaga randa kika haifeni baki karasamin kwanciyan hankali ba, yau dana fada rijiya all I could thought of was yanzu zaki fara samin kwanciyan hankali, bazan kara jawo matsala agidan nanba, bazan kara saki ko Abba a matsalan Kaka ba, Ya Nana zata auri Muhsin dinta, bazan kara zamema kowa matsala ba, Abba bazai kara wahalan boyeni ba dan nariga namutu” yanda take maganan tana kuka mara sauti sai hawaye kobakada imani sai zuciyanka ta sosu, ahankali tace “Mami akwai wata tambaya dana dade inaso namuku keda Abba” taidan shiru saikuma ahankali tace “bayan kun haifeni maisa tun a asibiti dakuka ganni daban bakusan yanda kukai dani ba maybe ko kuce baku sona a kaini gidan marayu kokuma kuce a chanza muku yarinya bani kuka haifa ba, maisa kuka daukeni still kuka raineni maisa kukamin haka, wanan kalan rayuwan dakukasa inayi kullum zaban mutuwa nakeyi akanta dan tafimin alkhairi I just want to die nahuta, dan Allah kubarni na mutu” tafashe da kuka sosai dayasa daga Abba Mami da Hamad were damn speechless itako Uwani dake gefe kuka tadingayi, tadade tana kuka ajikin Mami babu wanda yay attempting hanata ahaka bacci yay awon gaba da ita, ahankali suka kwantar da ita akan kujera suka lullubeta sanan Mami tazauna gaban kujeran tana kallon fuskanta, Tashi Hamad yayi yakalli Abba da Mami yace “Abba I want to see you both” yay sama tashi Mami tayo takalli Uwani da jajayen idanunta tace “ki zauna da ita” gyadamata kai Uwani tayi Mami tawuce sama itama, Abba yadade tsaye awajen sanan yawuce yay sama, dakinshi Hamad yabude ya shiga Mami tashigo Abba dashine na karshe shima yashigo yasami waje yazauna, kallon Abba Hamad yayi yace “Abba what are you going to do? Yaya zakayi da maganan Kaka?” kallon Hamad yayi yama kasa magana saikuma chan yace “all I know is bazan taba iya koran y’ata daga gidan nan ba” dasauri Hamad yace “Abba yazakayi da bakin Kaka, tace inhar yarinyar nan batabar gidan nan ba bata yafemaka ba, itaba mahaifiyarka bace kaza kaza kaza, Abba Kaka ta tsufa and we all know yanda tsofaffi sukai believing akan all this superstition, Du’a tazaman ma gidan nan da family mu gabaki daya matsala, jibi duka su Baffa dazu sunce duk akoreta ni I think inhar hakane zan dauki Du’a natafi da ita chan Jaji tai zamanta a apartment dina” dasauri Mami tace “Hamad duk randa mahaifiyar ka tasan kaika tafi da Du’a abin bazai muku kyau ba, kuma Du’a mace ce bazaiyi kyau tayi rayuwa dakai kai kadaiba dama kanada mata ne, ni kaina ayanzu all I want is peace, tunda Du’a ce matsalan afitarda ita daga gidan saisa na yanke shawaran kaita wajen Mama na achan Abuja” kallon Abba tayi ahankali tace “Dadyn Hamad” kallonta yayi yay shiru batare dayace komiba, ahankali tazo kusadashi zama tayi sanan takama hannunshi tarike tace “I know tunanin dakake da abinda ke ranka, mu dinan bamuke kula da Du’a ba wlh Allah ne, so it’s high time we free this girl mu mikama Allah komi and I assure u idan tana hannun Mama she’s safe nasan Mama na, I don’t want u to be stubborn, u are a family man, ba Du’a ce kadai yarka ba, sauran ma dole ka kalli yanda rayuwan su zata cigaba da gudana, sabida Du’a kar peace da family ka ya wargaje just look at what Nana is going through now itama ai yarka ce, the way u look out for Du’a itama haka kake looking out for her, kayakuri kaduba lamarin kaji” tunda take maganan yake kallonta harta gama, ajiyan zuciya yasauke sanan yace “I will think about it, kubani waje yanzu” gyadamai kai kawai Mami tayi ta tashi tawuce tafice, yakalli Hamad yace “ka kira Dr na yazo yadubata tashi katafi” tashi yayi ahankali yafice shikuma Abba ya kishin gida da kujera ya lumshe idanu Allah kadai yasan meke going azuciyanshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button