KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ahankali takai fararen hannuwanta tashare fuskanta sanan tamike tsaye ahankali, wani iri mahaukacin cokacola shape Allah yamata gawani irin pointed curvy ass gareta daya fito sosai cikin doguwan rigan material din dake jikinta, itama kaman sauran yaran gidan tanada dan jiki danbazaka taba kiranta da mara kiba ba amman batakai su Nana kibaba, saidai tafisu diri, ga gashin kanta dabaida banbanci dana yan India har waist dinta, juyowa tayi ahankali TSARKI YA TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA’ALA WANDA YA HALLICI SAMAI DA KASSAI DAKUMA HALITTUN DAKE CIKINTA!!!! yarinyar nan koda ace itace tayi kanta banjin zatai kanta tai kyan datake dashi yanzu hakaba dan My Lord!!! dan itace definition of tacika goma cip cip tamakai sha uku, farace Kal fuskanta babu pimple ko daya idanunta sun kumbura sunyi ja sabida kukan datayi wanda haryau takasa sabawa dan by now yakamata ace tasaba duk sanda yan uwan ta zasu makaranta boko ko islamiyya saitai kuka, tanada wani irin long pointed hanci ga pink lips, gashin idanunta dogaye kuma acike sun jikeda ruwa, ga kirjinta awani irin cike kaman wacce taje tai surgery ga flat tummy kaman bata tabacin abinci ba, Allah yamata ass amman waist dinta kona jariri albarka her waist is so tiny, ahankali take tafiya har zuwa gaban madubin dakinsu ribbon dinta dake wajen tadauka sanan ta kulle kanta da kyar sanan tashiga bayinsu wanko fuskanta tayi tafito tadauki dogon hijabin ta maroon tasaka tafito daga dakin ahankali.
Cikin wata irin siririyan cool melodious voice tai sallama gaban dakin Abban su, daga ciki taji yace “shigo” ahankali tabude kofa tashiga kanta akasa, yana zaune kan couch din dake dakin yabita da kallo tazo gabanshi tazauna tareda saukar da kanta kasa ahankali tace “Abba gani” zama ya gyara tareda bude Al Qur’ani dake kan cinyanshi sanan yace “biyomin haddanki” gyara zama tayi sanan tafara rairomai suratul Yusuf shafa’i ukun dayabiya mata last week, shi karan kanshi idan tana biyamai hadda baiso tadena dan muryanta Allah yay mata dadi saida tagama tsaf sanan yakara mata wasu shafa’i ukun kafin yamata tajweed sanan yace “tashi kitafi” tashi tayi ahankali tai hanyar kofa yasake binta da kallo harta daura hannunta kan handle din kofa taji yakirata anatse. “Du’a” dasauri tajuyoda kanta ta kalleshi saikuma tasauke idanunta kasa tace “na’am Abba” ahankali yace “nariga nasaman miki wata sabuwar malama, daga gobe zata fara zuwa In sha Allah, ki shirya” gyadamai kai tayi sanan tajuya zata bude kofan saikuma tajuyo ahankali batare data budeba ta kalleshi hada ido sukayi hakan yasa takasa magana tajuya zata bude kofan tafice cikin muryan nan nashi nabawasa yace “mekikeso ki fada”? Dan juyowa tayi ta kalleshi saikuma tasauke kanta kasa kirjinta na bugawa fat fat tashiga wasa da yatsunta tsabagen how nervous she was tama kasa magana, dan idan Abban su yakureka da ido zamaka iya fitsari ajiki baka saniba, shifa kokadan baida wasa kuma yanada zafi sosai, gashi kaifi daya saisa duka yaranshi ke tsoron shi. Ganin takasa magana yasa yace “I’m listening” rawa sosai muryanta yafara tanama bude baki maganan yakasa fitowa saikuma tasaki hannunta ta shiga chakuda hijabinta da hannu duk yana binta da kallo hijabin tarike gamgam sanan da kyar tasamu maganan yafito ahankali tace “Ab…..ba ni……maisa ake barina agida kahanani fita kowaje, Abba ni nafison naje school kaman su Ya Nana……” saikuma tasake hadiye wani irin dry miyau hawaye yawani zubo daga idanunta suka sauka akan hijabinta cikin wata irin murya na wacce ke gabda fashewa da kuka kuma take a bala’in tsorace tace “Ab….ba ni maisa baka sona kaman yanda kake son su Ya Nana da Hawwa da….d…..” Du’a!! taji anwani irin kirata da kakkausar murya dayasa tadaga kanta da sauri ta kalli inda taji muryan, Mami ce tafito daga bedroom din Abba da alamu tuntuni take ciki maybe gyaramai dakin take dan taga karamin rag na goge goge a hannunta, cikin wani irin tsananin bacin rai tace “Du’a are you questioning your father? eh? mahaifin ki kika tasa agaba kina tuhuma haka?” girgixa mata kai tayi dasauri saikuma tasaki kuka dasauri tajuya tabude kofa tafita daga dakin dagudunta.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️M SHAKUR
UMMI COLLECTION is a whole world of turaruka, both na wuta dana feshi, exquisite burners na electric dana charcoal, and oils, turarukan wanka da sauran su. kunkosan kwanan nan UMMI COLLECTION na promo free delivery, hehehe banso kuyi missing this mad offer just click on this link danyin magana da ita directly.
wa.me/+2348186968736
free page
EPISODE 2️⃣
Azuciye Mami ta jefar da rag din dake hannunta tace “nikema yarinyar nan magana tafice tabarni sabida batada kunya Dadyn Hamad” tataho cikeda bacin rai zatai wajen kofa tabita Abba dake kallonta tunda tafara masifan yace “ina zaki”? Turus ta tsaya tana kallonshi takasa koda motsi, anatse yanuna mata bedroom dinshi yace “koma kicigaba da abinda kikeyi” dasauri tace “but……” “no buts ki koma kicigaba da abinda kikeyi nace” yay maganan babu alamun wasa akan fuskanshi hakan yasa bata karacewa komiba tawuce takoma ciki ranta abace, jaridanshi yabude ahankali yacigaba da karantawa bazaka gane takamaimen wani yanayi yake cikiba dan fuskanshi bata nunawa.
Dakinsu tabude dagudu tashiga tafada kan gado tana kuka sosai, tayi kuka nakusan awa daya sanan bacci yay awon gabada ita akan gadon.
Hayaniya yatadata daga baccin datakeyi, bude idanunta tayi ahankali saikuma ta yunkura ta tashi zaune tana kallon dakin nasu, Nana da Hawwa ne kecire kayan jikinsu sundawo daga hadda duk sunyi zufa, ahankali tace “Ya Nana kundawo daga makaranta” danjuyowa Nana tayi takalleta tana kokarin daukan zanin dazata daura tashiga wanka tace “eh yanzu muka shigo””sannu da zuwa” tafadi ahankali sanan tajuyo da kanta Hawwa ta kalla taga Hawwa tadauke kai dasauri tana batarai, daidai lokacin aka bude kofan dakinsu, Aneela ce tashigo wacce take kanwarta, dan Du’a ce yar Mami tafarko, sai Aneela, sai Muhammad da Mudasir su Hudu Mami ta haifa, itakuma Mum itace mahaifiyar su Hammad, Nana, Hawwa, Amal, da Asiya yaranta biyar.
Ko kadan Aneel bata kama da Du’a inba ma angayamaka ba bazaka zaci uwarsu dayaba dan tafi kamadasu Nana black beauty ce itama, kyakkyawan yarinya bakutu da ita, zama tayi kan gadon takalli yayartata tace “yauma saida kika kara kuka sabida muntafi makaranta banda keko” Hawwa data zauna kan gadonta tana ciro wayanta daga jaka tana kunnawa tace “asheko xakita kuka har karshen rayuwanki dan Abba yace konan da gate bazaki taba fitaba” turo baki Aneela tayi cikeda rashin kunya ta kalli yayartata saikuma takai hannunta tadaura kan kumatunta tace “karki kara kuka kinji Duudo, kinga ko yau Malam yafassara mana wata aya yace duk wanda yadogara ga Allah to hakika Allah ya isar masa, ki dogara ga Allah and I promise you Allah will be there for you, kiyita addu’a zakiga Abba zai chanza zaice kema kifara zuwa school kaman mu kinji” gyadama kanwar tata kai tayi ahankali, Aneela tawani washe baki tai murmushi hakan yasa itama tai murmushi, Subhanallah idan tai murmushi numfashinka zai iya tsayawa sabida kyan datake karayi.
“In dauko mana abinci muci tare?” Aneela ta tambaye ta, Gyadamata kai tayi hakan yasa tasauka daga gadon tawuce tafita, itakuma ta sauka daga gadon ahankali sanan tawuce bathroom dinsu dan dauro alwala Hawwa tabita da harara wanda inda sabo tasaba tun suna yara basa shiri sabida sako da sako nesu dan daga Hawwa sai ita aka haifa agidan, itakuma Nana babu ruwanta bata shiga harkanta as per babban yaya in the house.