KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR
Kallo daya tamai tasaukar da kanta kasa dasauri, tunda take bata taba ganinshi ba rigaba sai yau, wani irin hadiye miyau tayi gabanta na dukan uku uku, tashiga wasa da yatsunta takasa magana, batare daya kalleta ba hankalinshi nakan aikin dayake yi akan system yace “why are you here”? Yanda kirjinta ke dukan uku uku yasa muryanta yama fara rawa tace “Y…..a As…ad, dama….dama….” saita karayin shiru tadan dagokai ta kalleshi aikinshi yakeyi comfortably a MacBook dinshi kaman baimasan tana wajenba, kirjinshi tabida kallo jitayi jikinta yadau rawa da sauri ta maida kanta kasa tadage tace “Ya Asad I want a new phone Ammi tace zata gayama shine yanzu wai muje musameka da kanmu, ahhmm kuma da shopping da resuming school, I want new school bags, pairs of shoes sai Abaya dakuma and kuma pads dinmu yakare duka” saida takai nan tai shiru kirjinta na bugawa fat fat fat bata taba sanin zata iyama Asad magana ba saiyau, juyoda kanshi yayi yakalleta for the first time tunda tashigo dakin, ahankali kaman baison yay maganan yace “what happen to your phone” dagokanta tayi ta kalleshi yanda yake kallonta yasa takasa mai karya langabar da murya tayi tace “babu abinda yasame shi I just wanted a new one” still kallonta yake babu alamun wasa kowani yanayi akan fuskanshi yace “and the other things nawa zai isheki kisaya” wani irin murmushi tamai cikeda jin dadi tace “150k zai isheni Ya Asad” Su Rahima da tuntuni suke gaban dakin suna jiran suji yanda zata kaya jin yana tambayanta nawa yasa suka turo kofan suka shigo suna sallama, duk atare suka gaidashi muryansu narawa. “Ya Asad good evening” dasauri Aneesa tace “Ya Asad kaga saida nace musu fa suzo muje tare sukaki wai tsoro sukeji sai yanzu dasukaji zaka bani kuma wlh ni bazan raba kudina daku na nawa kadai nafadi” dasauri Rahima tadan kyafta mata ido takalli Asad din tace “Ya Asad sorry” Mari ma ahankali tace “Ya Asad sorry ni wlh tsoro ya hanani ma biyota” duk tsayawa yayi yana kallonsu yanda duk suke trembling, ahankali yasaki dan murmushi, wani kalan dadi ne yakashe su dasauri Rahima tace “Ya Asad nima I want new phone” dasauri Mariya tace “Ya Asad nima” ganin suna neman samai ciwon kai yasa yakalli Aneesa yace “go to my room, check the left sidebed drawer bring all the money that is there” wani irin dadi taji tace “tom Ya Asad” dasauri tawuce stairs tai sama dakinshi tabude ta shiga wani kamshi ne yamata sallama, drawer taje ta kwaso duka kudin wrappers na yan dubu dubu ne guda 10, kwaso su tayi tasauko, Su Rahima na ganinta suka shiga murmushi, gabanshi tazo zata bashi kudin gefenshi ya nuna mata hakan yasa ta ijiye kudaden awajen, hannu yasa yadauki rapa biyu yabata dasauri takarba tawani washemai baki tama kasa godiya, “Rahima” “na’am Ya Asad” dasauri tazo dauka biyu yayi yabata dagudu Mari tazo itama yabata biyu dukansu yabasu 200k each, ahankali yace “u will get the phones tommorow” wani irin ihu sukayi sukahau tsalle awurin suna rungume juna. “Ya Asad thank u, yaaayyyy, Ya Asad u are the best wallahi” ihunsu yatada Sharif dake bacci hakan yasa yasauko ganin kudi a hannunshi suna rawa suna nunamai yasa cikeda wasa yace “yanzu sabida ku yan bakin ciki ne Asad na rabon kudi shine bazaku tasoni nazo na amshi nawaba ” dasauri Rahima tace “bayan kahanamu damuka maka magana” hararanta yayi yaje gaban Asad dake aikinshi yana kallon ragowan 4 raps na kudin yace “Ya Asad nima abani nawa”? Dan hararanshi Asad yayi saikuma kaman bashiba yakalli su Aneesa yace “abashi” atare sukace “nooo Ya Asad” wani irin biyo su dagudu Sharif yayi aiko suka kwasa dagudu suka fita daga dakin yace “shegu yan bakin cikin yara kawai” murmushi Asad yayi sosai yace “kasai musu waya” juyowa yayi yaharari Asad yace ” marasa kunyan yaran nanne zasuci kudina, ashe zasu mutu bawaya, Tara kudin aure nake” tabe baki Asad yayi yace “says wanda baida girlfriend” hararanshi Sharif yayi yace “Malam ya isheka fa kaita daga harkata tunda dai kahanani kudi”.
wa.me/+2347012181461
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
EPISODE 1️⃣8️⃣
Tashi Asad yayi ya rufe system din ya ijiye sanan ya kwashe ragowan kudinshi yawuce wanshi sama, baiwani dade ba yasauko cikin jallabiya sabida sallan magrib da aka kira sai baza kamshi yake bayin falo shima Sharif ya shiga ya dauro alwala sanan yafito suka fice tare zuwa masallaci.
Ana Magrib suka shigo gidan, dinning direct sukayi, zama sukayi Ammi na fitowa, Sharif yace “Ammi ina yaran nan wai nisukema dariya” dan hararanshi Ammi tayi tace “toba dole suyimaka ba nan nan yaran nan suka rokeka kudi kahanasu, anyway suntafi wajen Hajiya, kasan jikan Hajiya tazo shine ita sukaje gani nace musu nai musu kawa age mate dinsu ce wai zasu cemata ta shirya suje shopping tareda ita gobe” tsaki Sharif yayi yace “Ammi bani abinci na naci nima naje naga jikan Hajiyan muga ko za’ayi ta gida ne, Ammi tanada kyau”? Hararanshi Ammi tayi tace “inkaje ka gano da idanunka” tai maganan tana bashi plate na biryani rice, karba yayi yafara ci sanan ta zubama Asad dake daddanna wayanshi kaman bashi awurin. Biryani ta zubamai sanan ta turamai gabanshi tace “ina kaje dazu Asad” dagokai yayi yakalleta spoon yadauka zai faracin abincin yace “naje nasha iska ne kawai Ammi” ture abincin Sharif yayi yamike yace “Ammi natafi” wanan karan dariya Ammi tayi tabishi da kallo fita yayi abinshi, tashi itama Ammi tayi tai sama bata wani dade ba tafito rikeda drawing book din Du’a samin shi tayi zaune inda tabarshi yanacin abinci, kujeran kusada shi taja tazauna sanan ta ijiyemai drawing book din agabanshi, Ammi yabi da kallo saikuma ya ijiye spoon din dayakecin abinci dashi yadauki drawing book din yabude yana dubawa, ahankali yakalli Ammi yace “Ammi who drew this”? murmushi Ammi tayi tace “zanen yayi kyau” dasauri yana kallon drawing din yace “this is classic, I mean the hands behind this drawings is a genius, Ammi wow, idan yanzu nabada wayan nan zanen akai bringing this shoe to life my company zai zama number show brand company in the whole Africa” murmushi sosai Ammi tayi tace “zaka bama mai zanen aiki kenan”? sai alokacin ya kalli Ammi yace “who drew it Ammi” ahankali Ammi tace “zan gayamaka, but my zanen is very dear to me nai alkawari zaka bama mai zanen aiki dudda batai makaranta ba” dasauri yace “Ammi u mean mace ce tai zanen!” gyadamai kai tayi tace “yes mace ce, but batai school ba sabida some matsaloli irin na rayuwa, but she’s talented, inason kabata aiki sanan kabiyata tsakani ga Allah yanda kake biyan illustrators dinka” yatsine fuska yayi yace “Ammi kinsan qualifications din illustrators dina kuwa, how can I pay wacce bada da credentials haka is not possible ma” fizge drawing book din Ammi tayi tace “then forget it” dasauri yace “okay naji Ammi kawo” ya karbi drawing book din yana kara dubawa, Ammi tace “yanzu yaushe zata fara aiki” ahankali yace “gobe Monday, for now Sharif will handle everything dan sai next week zan koma”
wa.me/+2347012181461
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 1️⃣ 9️⃣
Gyadamai kai Ammi tayi cikeda jin dadi tace “Allah maka albarka Asad dina” murmushi yayi yace “Ameen Ammi, but who is the girl”? kaman bazata fadamai ba tace “jikan Hajiya ce, she’s 21” yatsine fuska yayi yace “Ammi ni all those children banson raini fa” hararanshi Ammi tayi tace “to Uncle Asad, ya za’ayi ma tamaka raini, jikan Hajiya ai she’s just like ur sister su Mariya idan tayi badaidai ba ka gyaramata, kuma batada raini ko kadan that I know” yatsine fuska yayi irin baimasan maganan nan ahankali yace “Ammi I want coffee” tashi Ammi tayi tace “bari nahado ma tunda yaran nan duka sun gudu gidan Hajiya sun barni nikadai” kitchen tawuce tashiga….