KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Yau idan kaga bakin Du’a har kunne, har Rahima dake feeling tagirme su bazata iya zama friend din Du’a ba jitayi tanason Du’a sabida yarinyar akwai kyau dudda sun lura duk sun fita wayewa basu wani damuba kafin kice me cika falon Hajiya sukayi da hayaniya, suka tasa Hajiya agaba sai tabama Du’a itama kudin shopping gobe duk suka tafi tare, itama 200k tadauko tabata daman tanason takai yarinyar shopping but bata sami lokaci ba waya ma tace “gobe idan zata dawo zata taho mata da waya” duk suna cikin uban hanayinan Sharif yay sallama, dasauri Rahima tace “kinga Du’a we have two brothers, wicked and harsh, yanzu zakiga weekend one din shike mana murmushi da wasa amman shine ba’acin kwandalan shi” Hajiya dake kallonsu tace “Au haka kikace Sharif shigo kaji yanda kannenka kebata maka suna” turo kofan yayi yashigo hakan yasa Du’a itama tadaga kanta dantaga wanda ake batawa, wani kyakkyawan gayene dogo mai tsayi gashinan fari fat kaman su Rahima, tana ganinshi taga kamanninshi da Rahima da Mariya, baida kiba ko kadan, sai uban kyau ga sajenshi baki sidik dasuke nan akwance, gashin baida tarin gashi irin na Asad amman akwai gashi kadan da lowcut yakeyi ko kadan bata ganeshi ba hakan yasa kawai ta tsaya tana kallonshi daga inda take zaune kusada Hajiya dasu Rahima.

Dauke kai yayi daga kallon Du’a ganin kannenshi da kowa na wajen yace “Hajiya yanzu har gidanki suka tattaro sukazo suna gulmana yaran nan, aiko wlh zan baku kashi” yay maganan yana dunfaro su, ihu sukayi duk suka tashi suka kankame Hajiya Du’a ko sai dariya dasauri Hajiya tace “jama’a na shiga uku, wani yamikomin wayata yaga wlh Ammin ku zan kira tazo ta kwashi yaranta kutafi gida tunda neman kasheni kuke kai kuma wlh bazaka taba yaran nan agidan nan na ko kazo kazauna kokuma kawice katafi idan mugunta kazo yi nagayamaka kukuma ku dagani” Da sauri suka dagata shikuma yazo gefenta yazauna kusa da ita yay folding hannu yace “Hajiya jikanki batada kunya ita batasan yayanta yazo tagaidani ba wlh idan tace zata biyema marasa kunyan yaran nan nida ita bazamu shirya ba” yay maganan yana hararan Du’a, sosai Du’a ke murmushi ganin yanda Sharif keda ban dariya, ahankali cikin yar muryanta tace “Ya Sharif ina yini” hararanta yayi yace “lpy lau” Mariya dake gefenta tace “Ya Sharif kaga harda ita zamuje shopping din gobe tunda Ya Asad yabamu namu kai kabata nata ai itama kanwarka ne yanzu” dasauri Hajiya tace “ohh ni yasu Mari ke Mariya yaushe kika dawo scammer eh, Sharif yaran nan damfaran ka zasuyi ba yanzun nan nabama Du’a nata 200k dinba” dan sosakai Sharif yayi yace “Hajiya ni bansan ko yaran nan basuso nai aure bane, kudin aure fa nake tarawa” saikuma ya kalli Du’a yace “nasan sun riga sunce miki banda kirki I will prove them wrong, kinga ban shigo da kudi ba, but zanbama Mari gobe tabaki okay” gyadamai kai tayi tana kallonshi irin kaman bata yarda ba dinan dan ita Grandma tariga tabata kudin ta, kaman Hajiya ta lurada hakan ne yasa tace “baki cema Yayanki kingode ba” murmushi tayi ahankali tace “nagode Ya Sharif” nan fa dakin ya kachame da hira, shi Sharif baida girman kai yana shiga kannenshi yayi hira dasu sosai iyayensu dasuka rasu yasa yafara haka dan he is all dasuke dashi couple with the fact Asad baida wasa, saisa yake hira dasu yasasu dariya yasasu bakin ciki komi ba, daga karshema zamewa Du’a tayi tai bacci shoulder ta nakan jikin Rahima, sai wuraren 11 Sharif ya tarkatasu sukama Hajiya sallama suka tafi kaman karsu tafi, itakuma ta tada Du’a tawuce taje ta kwanta.

Flat dinsu ya shiga yana maida kofa yarufe sanan yashigo ciki Asad yagani zaune afalo yana kallon wani horror movie a smart TV dake falonsu, tsaki Sharif yayi danya tsani horror movie zama yayi yace “kafara kallon film din aljannun nan naka ko” dagamai gira daya Asad yayi sanan yadauki drawing book din da Ammi tabashi ya jefama Sharif din, dasauri ya chapke yace “what is this” yay maganan yana budewa, ganin wasu hadaddun zanen takalma yasa yamike tsaye yacigaba da kallon su one by one. “woooooo Asad who drew this??? Wow Wow, waye yay zanen nan eh, we need this talent a company mu wlh, who drew this Asad” dan batarai yayi yace “Ammi takawomin wai I should hire wacce tai zanen a company mu” dasauri Sharif yace “of course Asad you should hire this talent karfi all those competing companies su gano mai zanen su rigaka hiring nashi, but waye mai zanen a ina Ammi tasamo maka” tabe baki yayi yace “tace wai jikan Ammi ce mai zanen, she’s a small girl 21, kuma karatun ta a JSS2 ta tsaya due to some reasons best known to them, how can someone dabaida qualification zaimin aiki eh” dasauri Sharif yace “in this case don’t look at qualification look at the talent, Asad ko bature illustrator dinka baitaba zana takalma masu kalan kyau dinan ba, this is masterpiece wlh, mukai takalman nan trust me all celebrities across the globe will be rocking ur brand, yarinyar nan tun wuri without second thought kadauketa” yatsine fuska yayi yace “Ammi tariga tasa nadauketa gobe zata fara aiki” dasauri Sharif yace “gobe” dan yasan gobe zasuje shopping, gyadamai kai Asad yayi yace “yes, inaso you should handle everything, interview her kasata a office na illustrator din let her get to work, guide her, before nagama this TV program in yaso once am back sai afara work on production” gyadamai kai Sharif yayi yace “okay Asad, bari naje na kwanta, kaine night owl” yay maganan yana stairs yana murmushi da gangan yaki fadamai wacece jikan Ammi yanaso yaga reaction dinshi ranan dazaiga wacce yace to daga rijiya ce jikan Hajiya ita yabama aiki.

Wuraren 5:30 Hajiya tashigo dakinta, tadata tayi ahankali tabude idanunta tashi tayi ahankali tazauna Hajiya dake kallonta tace “guess what” bude idanunta tayi tarr tana kallon Hajiya, murmushi Hajiya tayi tace “kinsami aikin” wani irin murmushi tayi tawashe fararen hakoranta, Hajiya tace “amma ance yau zaki fara aiki, danhaka tashi kiyi salla kiyi wanka ki shirya yarinya na is now a working class young lady, my lucky jika” murmushi sosai tayi ahankali cikin muryan baccinta tace “Grandma shopping dinmu dasu Rahima fa” murmushi tayi tashafa gefen fuskanta tace “don’t worry about that karfe 4 zaki tashi daga office idan kindawo sai kuje, yanzu tashi kije kiyi salla” gyadamata kai tayi ta tashi dasauri tai bayi alwala tayi tafito tai salla saida tai karatun Al Qur’ani tai addu’a Allah ya sanyama aikinta albarka sannan takoma bayi tayo wanka tafito mata shafa ta shirya cikin riga da skirt na atampa sanan tafito falo, tunda take saukowa Hajiya ke kallonta ganin yanda mahaukacin shape dinta yafito akayan yasa taji bata natsu ba, ko aikin ma data bari tayi sabida tasan Ammi da yaranta ne tasan yanda sukeda natsuwa kuma tasan zasu sa ido akan Du’a, saisa ta natsu da bata bartaba, sanan kuma tanason yarinyar takara girma tai wayau tasan ya rayuwa take outside home, kujeran dinning Hajiya taja mata hakan yasa ta zauna tace “grandma cikina namin wani iri idan natuna zani aiki” dan dariya Hajiya tayi tana zuba mata tea da Irish tace “kina feeling butterflies a ciki, it’s normal, yanzu ci abinci karki latti fa, 8 ake zuwa aiki” dasauri tashiga cin bata wani ci sosai ba dan bata iyacin abinci sanan ta tashi, Hajiya tace “anya bazan sayo miki Vitamin B complex ba kuwa Du’a baki iyacin abinci, oya tashi muje sama kiga” tashi tayi sukai sama, dakinta suka shiga Hajiya tabude wardrobe dinta, wani sabon abaya taciro mata black mai mahaukacin kyau ta ijiye kan gado tace “inaso ki zama very wise girl, kinga kalan jikin da Allah yabaki dan haka bazaki dinga saka atampa haka kina zuwa aiki ba, zan karo miki hadaddun abaya masu kyau su zaki dinga sawa kina zuwa office okay, inaso idan kikaje ki natsu ba ruwanki da gulma ko surutun office respect ur senior idan kikai laifi aka miki fada take ur correction, karkiga sabida kinga Sharif ko Asad sabida kin sansu suna kaman matsayin yarana ne kidinga musu magana anyhow ko rashin kunya no, a office is strictly work and formal communication okay, ki natsu kafin ki zauna akan kujeran aikin ki da za’a baki kiyi addu’a, kullum idan kika shiga office dinki kafin kifara aiki kiyi addu’a hakan zaisa kidinga samin cigaba Allah na Buda miki, ki zama mace mai kamunkai, abinda yasa nama barki kiyi aiki sabida inaso ki sami experience ne kisan menene rayuwa dan bakisan komi kan rayuwa ba Du’a, be very smart okay, karki damu yau zan sau miki wata” gyadama Hajiya kai tayi tace “thank u Grandma” ajiye mata kayan tayi tace “oya shirya nima bari naje na shirya zan shiga office yau saina saukeki a company ku” wucewa tayi tafice, shiryawa tayi cikin doguwan rigan ita kanta saida ta kallo kanta saboda yanda tai wani kalan kyau, parking kalabanta tayi sanan tazauna kan kujeran tadau gyalen abayan tana kokarin rolling bata iyaba aka turo dakin aka shigo, Hajiya ce ta shirya cikin ubansun gown din lace rikeda waya tamikama Du’a tace “ga Mamin Ki” karba tayi takai kunnenta ahankali tace “ina kwana Mami” ajiyan zuciya taji Mamin ta tasauke tace “Du’a ya kike” murya chan kasa tace “lpy lau” murmushi Mami tayi tace “ance kinsami aiki Allah ya sanya alheri ki kulada kanki kinji” murya chan kasa tace “to” “OK bye” bye tace Mami ta katse wayan karban wayan Hajiya tayi tace “bani gyalen kiga namiki rolling” rolling Hajiya tamata tsaf, saita juya tana kallon gaban mirror hannu tasa tadauko wani pink janbaki da kwallin saka mata kwallin tayi sanan ta shafa mata Jan bakin kadan daya saje da lips dinta, kafin tadau turaruka ta fesa mata sanan tadauko wata jaka tace “idan mace zata fita most especially office haka makesure kinada pad kwata daya aciki incase of period yazo miki, sai wipes, sai lip balm, sai dan karamin turare haka dayar hoda ko madubi, pen da dankaramin jotter haka” tai maganan tana daukan komi tana samata ajakan sanan tabata jakan, karba tayi tana murmushi Hajiya tawuce tafita tace “sa takalmi ki sako” takalmi tasaka sanan tajuya takalli kanta a mirror wlh kaganta bazaka iya tantanceta da balarabiyaba tai wani irin kyau akayan, hakanan saitaga tama kanta girma tadawo wata babba kaman yar mai kudi jin Grandma ta kwalama ta kira yasa tajuya da gudu tafice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button