KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Tunda suka shiga hotel din gabanta ke faduwa sosai parking yayi hakan yasa suka bude suka fito suna kallon kofan dazai sadasu to asalin cikin hotel din da wani security guard dake sanye da uniform ke tsaye yana kallonsu, kallon Du’a dataga ta tsaya sakakau Razika tayi yanda take kalle kalle tace “a ina akeyin abun” dan zaro idanu Du’a tayi irin na asalin wanda doesn’t have any idea akan abu tayi tace “nima bansani ba” ganin haka yasa Razika tadan matso kusada ita murya chan ciki tace “to ki tambayi wanan security daman gashinan yanata kallonki” dan zaro idanu tayi saikuma tajuya takalli mutumin dake kallonsu har lokacin kafin Du’a tai magana yace “are you here for the program”? Gyadamai kai Du’a tayi batare datai magana ba, yace “to ku shiga hall din ma 8th floor” gyadamai kai tasakeyi sanan tawuce tafara tafiya tana kama hannun Razika suka shiga ciki tare, tunda taji 8th floor yasa tasan akwai elevator hakan yasa sukai hanyar stairs suka farabin bene, da sauri sauri gudu gudu take hawa stairs din, sosai sukai nisa dafa bango Razika tayi tana nishi sosai tace “wayyo Allah na kafana, Du’a nagaji wlh” kaman zata fashe da kuka tace “nima wlh nagaji kinga ankusan gamawa dan Allah muje” tashi Razika tayi tana nishi suka cigaba dabin stairs din ita karan kanta Du’a daurewa tayi kaman kaman kafafunta zasu tsinke, ahaka suka kai floor din tundaga tsayin corridor wajen sukaga mutane sunyi layi hadaddun yammata da maza anyi layi har zuwa hall din da cikin hall din da ake asalin abun, ganin anbisu da kallo yasa Du’a tabi Razika da kallo saikuma takoma tabayan Razika tana sussunar dakai kaman mara gaskiya dan wani iri takeji idan ana kallonta, murya chan kasa kaman mai whispering tace “Razika tambaya mana inane hall din me akeyi anan” dan Jim Razika tayi saikuma ta kalli wata mata dake tsaye alayi tana sanye da hijabi tace “dan Allah inane hall din” hall din dake gabansu matan ta nuna mata tace “ga hall dinan” ahankali Razika cikeda tausasa murya sabida karta gaji da ita tace “angama ne me kukeyi alayi dayawa haka”? File din dake hannunta matan ta nunama Razika tace “anriga angama liyafan, layin nan kuma na masu son irin su email dinshi ne sanan muna using opportunity din muna submitting CV dinmu akwai possibility na zaiyi recruitment koma baiyiba tunda gwamnati sunsan da zamanshi zaya iya sama mana aiki kingane, long layi ne about 100 people naciki duk sunata bashi kuma ya karba” gyadamata kai Razika tayi tace ” nagode sosai, sanan tadan matsa baya still Du’a na labe abayanta tace “kinji ko, ina zamu iya jiran this plenty mutane dasunkai 200, Hajiya tasan kinzo nan” girgixa mata kai tayi alamun a’a, hakan yasa Razika tace “to gaskiya ki wuce mutane tunda anriga angama bazamu kafin akawo kanmu goman dare tayi” gyadamata kai Du’a tayi asanyaye Razika tace “muje” juyawa tayi ahankali suka fara tafiya saikuma ta tsaya Razika takalleta tace “menene?” ahankali tace “I want to say thank u” bata jira amsan Razika ba tawuce wajen da saurinta tai gaban hall din tana sussunnar dakai batai wata wataba kawai ta danna kanta ta kutsa tacikin mutanen dake layi tashiga hall din, tana shiga yan waje sukahau ihu chaaa barinma matan wasu suka biyota ciki ganin haka yasa tawani irin kwasa da gudu dan hall din nada makeken girma sunachan kan stage, dagudu itama Razika tashigo tana kwala mata kira. “Du’a, Du’a, Du’a ina zaki”…..

Chak ya tsayar da rubutun dayake ma wata a littafin data bashi, yau yana sanye cikin wani gray suit dayafi na kullum mai kyau, yana zaune yadaura kafa daya kan daya agaban wani hadadden table, both sides dinshi bodyguards ne tsaye rike da gun, sai wasu manyan mutane dake kan stage din suma a zazzaune da suit, tsayar da rubutun chak yayi batare daya dago kanshi ba jin ana ihu da hayaniya a hall din amman suna daya kunnenshi ya iya karba Du’a!

Dawani irin gudu Du’a takaraso gaban hall din daidai inda mutum zai fara hawa yan kirgaggun stairs din dazai sadaka to stage din wanda anan line din yafara duk wanda yazo kanshi xaihau stage ne yaje yasauko, wani irin tsayawa Du’a tayi tana nishi sama sama kaman kirjinta zai fashe sabida gudun datayi tana kallonshi ganin yes yes tabbas shine, daidai lokacin matan dasuka biyota suka karaso cikeda fada sukace. “ke waye dazaki baromu alayi ki gudo ki shigo ciki” juyawa tayi tasake kallonshi cikin muryanta mai shegen zagin nan da dadi dake rawa kuma sabida tsabagen tsoro dakuma gudun datayi tana kallonshi still tace “thank u” duk binta akai da kallo ganin yanda take kallonshi tacemai thank you, wani mutum dakebinta da kallo ne dakekan stage din yace “Pretty lady ki koma kibi layi idan akazo kanki then you now tell him thank u, as it is so many people sun cemai thank you yours is not first kinga he is busy” yanuna mata Asad dayama cigaba da attending to mutane kaman ma baisan something is going on ba, gyadama mutumin kaitayi hawaye na neman zubomata amman ta daure tana kallonshi ahankali tace “thank you for saving my life” daya daga cikin matayen dasuka biyota ne tawani finciketa tace “dalla malama kizo kifita” dasauri Razika takama hannun matan tace “kisaketa dalla kema ai tafiya zamuyi, muje Du’a” kasa daga kafa daga wajen Du’a tayi tana tsaye kaman an dasata tana kallonshi, muryanta wanan karan narawa sosai hawaye yacika idanunta sosai tace “thank you for saving my life” fincikanta matan tasakeyi hakan yasa Razika tace “malama dalla kisaketa, Du’a let’s go” kin motsi Du’a tayi kaman ba ita akeja ba, nan hall din yadau hayaniya, ahankali ya sallami guy din dake gabanshi sanan yajuyo da kanshi ahankali yadaura fararen idanunshi akan na Du’a da akeja taki tafiya tana kallonshi, faduwa gabanta yayi yanda yanda ya kalleta, wani irin yatsine fuska yayi sanan yadauke kanshi daga kanta yajuya yakalli security dake gefen damanshi batare daya kalleta ba yana jiran next person dake kan line yanuna Du’a da yatsanshi a wulakanci yace “fitarmin da yarinyar nan daga hall dinan please and throw her outside this premises”.

wanna talk to me no problem just click on this link wa.me/+2347012181461

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

Chat me up directly by clicking on this link wa.me/+2347012181461
✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 2️⃣5️⃣
Ko karasa maganan baiyiba katon bodyguard dinshi yataho hakan yasa Razika tawani ja hannun Du’a da duka karfinta, fashewa da kuka sosai Du’a tayi Guard din nabinsu Razika najanta da sauri tana kuka mutanen wajen namata dariya suka fita daga wajen sukai hanyar staircase suka farabi, sai alokacin bodyguard din ya tsaya ata gaban stairs din yace “idan kuka dawo cikin wajen nan saina bindigeku” dasauri Razika kejanta suna sauka sai alokacin tasan ashe kafafunta sun gaji, sosai take kuka Razika tace “waike bakida wayaune Du’a saikace wata karaman yarinya, jibi yanda kikasa akai embarrassing namu” da kyar ta iya karasa sauka daga stairs din kaman kafafunta zasu cire daga cinyanta suka fito waje, wani Alhaji ne suka gani tsaye awajen yana gyara zaman malum malum dinshi yana kallonsu, hannu Du’a tasa tai wiping hawayen dake kan fuskanta tass, wani irin murmushi mutumin yasakin mata yace “common pretty girls basa kuka, daina kuka” dasauri Razika tacigaba da janta da sauri dan magrib yayi, da dan gudinshi ko kunyan mutanen dake wuce su baiyiba yasha gabansu yakalli Razika yace “I guess ke kawarta ce ko dan Allah sakin mata hannu kibani minti daya nai magana da ita” yakalli Du’a data dauke kai yace “Pretty dance mata tasakin mata hannu” cigaba da tafita sukayi yana binsu har sukakai mota, bude motan Razika tayi Du’a tafara sawa aciki sanan tashiga itama taja kofa mutumin na bubbuga kofa takalli driver Hajiya tace “muje wanan mutumin na binmu” kunna motar yayi yaja shikuma mutumin yadaga hannunshi sama kaman mai kiran mutane saiga wata hadaddiyar jeep yazo baya yabude yashiga yace “mubi wanchan motan Auwallu amman ahankali zamubi motan sabida karsu sani suboye inaso nasan mahaifin yarinyar nan” yana biyedasu har suka shigo estate dinsu, nesa dasu yasa aka kashe motan ya gyara zama yana kallonsu, gate aka bude musu suka shiga ciki sanan aka maida gate din aka rufe, dasauri yace “tada motan kaga Auwallu” tasa motar driver shi yayi zuwa gidan da Du’a ta shiga, parking yayi akofar gidan sanan yabude bayan motan yafito yana gyara zaman malum malum yana leken gefen gate din kaman wanda yasami matsalan tabin hankali, ahankali yakai hannunshi zaiyi knocking gate din aka bude gate din aka fito, Sharif ne yafito daure da alwala dan masallaci zaije sallan isha’i, tsayawa yayi yabi mutumin da kallo, dasauri mutumin ya shiga leka gidan kaman zaiga Du’a ta gefen Sharif, ganin haka yasa Sharif yarufo gate din ahankali yace “lpy” wani irin murmushi Alhaji yayi tareda shafa kanshi saikuma yace “wai mugaisa wlh duk na rude ne naga abinda raina ke matukar so” yamikama Sharif hannu, kin bashi hannu Sharif yayi yana kallonshi still yace “lpy maikazo nema? Kokuma nace wakake nema?” sake sosa meya Alhajin yayi yace “wlh naje ba wata yarinya yar fara haka nabiyo naga tashiga gidan nan, inataso namata magana tun achan amman dayan datake tareda ita taja hannunta tahanata magana dani wlh, dan Allah ko zan iya ganinta kokuma zaka hadani da mahaifinku dan naga kaman kai yayanta ne naganka fari kaman ita dudda tafika fari da kyau” yay maganan yana lashe baki yace “Allah yayi mace awurin nan wlh” wani irin daure fuska Sharif yayi ganin tsohon banza ne, hakan yasa yace “sunana Sharif, kuma yarinyar dakake magana matata ce, ka kama girmanka ka tattara inaka inaka kabarmin kofar gida kafin nahadaka da hukuma” wani irin kwalalo idanu yayi saikuma yadaura hannu akan saman bakinshi yace “assha ai bansan matarka bace, bansan matan aure bace wlh nagayamaka bata kulani ba inda ace takulani tagayamin tanada aure daban biyota ba wlh, amin afuwa nabarka lafiya” yajuya yashiga mota dasauri sukabar wajen wani irin tsaki Sharif yaja yabi motan da kallo yace “tsohon banza kawai” saida yaga su fita daga estate din sanan yawuce yatafi masallaci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button