KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

       ✍️ M SHAKUR 

EPISODE 2️⃣6️⃣
daurewa yayi iya daurewa danko kadan baiso tagane yanayin dayake ciki but maganan datayi kiris yarage bai koro amai acikin motan ba, hakan yasa yakasa magana dawuri kafin ahankali yace “it seems u are not interested in my offer, keep the paper and get out of my car” ganin yanda babu wasa tattare dashi yasa tadanyi murmushi tace “wow yanda Abban ka keda raha bansan cewa zai iya haifan murdadden mutum haka ba, anyway naji tunda u don’t wanna fuck me u have to add 2min akan kudin idan kayarda then we have a deal idan baka yarda ba we don’t have” yana kallon waje har lokacin yace “deal zan baki 12M” signing paper tayi sanan ta mikamai hannu yasa yakarba yace “zan aiko miki da kudinki and everything dana fadi gobe with a copy of this document dakikai signing excuse me” wani irin murmushi tayi tacigaba da taunan cingam dinta tace “I am curious so I have to ask this question kana tunanin ayanda Babanka yake sabida nabace na barshi bazai nemi wataba ne?” batare daya kalletaba yace “at least idan baki zai dawo gidanshi to his family” wani kalan dariya tasaki tana tafa hannu saikuma tanuna shi da yatsanta dayasha uban nails tace “I am sorry Asad but bari nagayamaka this kaga mahaifinka neman mata nacikin jinin shi ne, kaga dudda yana taredani nasan cewa nice best dinshi da nikadai wacce ya ijiye akarkashin shi but still bai hanashi cheating on me ba yanabin wasu up and down, agabana baya kunyan kallon mace kaman zai cinye ranan nan harwata yar kyakkyawan yarinya yadinga kallo a saloon daya kaini, kawai zama nakeda shi sabida banda wanda yake kashemin kudi irinshi but baban ka is a certified cheat” batare daya kalletaba yace “can you get out of this car please” dan dariya tayi tana kokarin bude kofa tace “sure mana ganinan ma fita nake, but know this, bin matan Baban ka kana basu kudi dan surabu dashi is not a problem dan karuwai irinmu are just after money zamu karba muwuce, the problem is kudinka gabaki daya saiya kare akan babanka ne, that Man bayason mahaifiyarka yace batada komi kaman bamace ba haka take gar……..” wani irin ihu daya dakamata yasa batasan lokacin datai wani irin tsalle tafadi waje akasa daga motan ba bura’uban wlh ta bala’in firgicewa, kunna motar yayi baima tsaye rufe kofan side dinta yake abudeba yawani irin yi reverse da mugun gudu tai flat akasan wajen danda sai marfin motan side dinta ya kwaye mata fuska yawani wanke ta da kura yabar wajen.

Yadade yana tuki sanan ya tsaya awani masallaci akan hanya yay salla sanan yafito yashiga mota yana tuki yana lumshe ido yana budewa, he just needs some time alone, he needs fresh air, kaman yatafi airport yashiga jirgi yabar garin yakeji amman bazai iyaba, he just wants to get away daga gidansu this night baimasan kowa ya ganshi na gidansu, yana tunane tunanen yakai anguwan su kasa karasawa yayi gidansu kawai saiya sami kanshi da tsayawa gaban gidan Hajiya horn ya danna hakan yasa Maigadi yafito ganinshi yasa yakoma yabude gate jan motan yayi ciki, yadade zaune a motan sanan yabude yafito yay ciki, ahankali kaman mara gaskiya yay sallama chan kasa yabude kofan falon yashiga, Grandma na zaune kan kujera ita kadai a falo tana kallon gidan Badamasi a Arewa24 ga bowl dake cike da sliced fruits ajikinta tajuyo da kanta, kallo daya tall tamai takarance shi tsaf, maida kofan yayi yarufe ahankali yakaraso cikin falon har zuwa gabanta ya tsaya, cikin wani kalan yanayi na bala’in sanyin jiki yace “har yanzu dakina na nan Grandma”? Duk gidansu Ammi shi kadai kecema Hajiya Grandma dan sauran gabaki dayansu Hajiya suke cemata, tunda yaga yanda Ammin shi tamaida Hajiya Mahaifiyar da Batada shi dan Ammi batada Mama, Maman Dadsuka raineta, tunda yaga yanda Ammin shi kesonta itama takeson Ammi yamaida Hajiya kakanshi saisa yake cemata Grandma, yawanci idan yana cikin kunci ko wani abu na damunshi wajen ta yake zuwa yakwana dan musamman tamai dakinshi agidan, saisa dazaran yazo wajen ta Ammi bamata nemanshi sai hankalin ta ya kwanta.

Ahankali tace “Asad are you okay”? Gyadamata kai yayi batare dayay magana ba, dan Jim tayi tana kallonshi sanan tace “jeka kwanta dakinka na nan, nakawo maka wani abu ne”? Girgixamata kai yayi yace “a’a I will eat in the morning” yay maganan yana hawa stairs, falon saman yawuce da dakunan dake wajen yay wani dan corridor da aka jera flowers awajen wanda bazaka taba sani da flower awajen bama, ahankali yabude kofan dake wajen yashiga dakin dakenan fess fess gahotonshi da aka makala a bango lokacin yay graduating a school a UK dashi da Grandma ne ajikin hoton suna murmushi duka.
wa.me/+2347012181461

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

       ✍️M SHAKUR 

Free page
chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461
EPISODE 2️⃣7️⃣
Fadawa kan gadon yayi batare dayacire daidai da takalmin kafanshi ba balle kuma ayi maganan kaya, sosai kanshi kewani irin sarawa, he’s so tired and everything and anything, he’s working damn hard to keep his whole family happy, shi baida matsala idan da Dad zai natsu yace aure zai kara yasan Ammin shi she won’t object to that dan tasan yafi mata alkhairi, but wanan wulakanta Ammi dayake yi yafi komai bakantamai rai, shi bawai yasaketa ba kotamai wani laifi ba amman saiya kauracemata dasu yaranshi for months kuma bawai yaje anywhere bane yana nan Abuja tareda matan banzan shi, yasan once Zinariya takarbi komi dazai bata gobe ta tafi zai dawo gida he hopes from there shi And Ammi can work something together, wani zubin he understands his Dad in the sense that auren hadi aka mai da Ammi but that doesn’t zama excuse nashi dazaije yana Zina up and down, Ammi is very very sick low BP takeda shi ita ba high BP ba, and low BP yafi dangerous da high BP mutum can yanke jiki yafadi at any time yamutu, akanme Dad zai dinga wulakanta Ammi eh yamaida ita kaman trash his mother is very sick dudda bata nunawa, but yaga tanashan drugs aboye, gashi sai ramewa takeyi, she’s depress dan yasan Ammin shi nason Dad sosai kodaga yanda take luradashi ma zakasan hakan he just wish yanada power to change things arayuwanshi, he wish ana iya chanza mahaifi, hannunshi yakai ahankali ya share wani dan gajeren hawayen daya zubomai ta gefen ido sanan ahankali ya fuzar da iska waje mai zafi, ko minti biyu baikaraba bacci yay awon gaba dashi mai nauyi gaske yana sauke ijiyan zuciya daman ance behind every thought face akwai thousands of weakness aciki.

Wuraren 5:30 nasafe Grandma tabude kofan dakinta tafito, hanyar dakin da Asad keciki tayi, ahankali tasa hannu tabude kofar tashiga yana bacci har lokacin baitashi ba ga takalmi nan baicireba kayama haka, maida kofan tayi tarufe sanan takaraso tazauna abakin gadon, ahankali takai hannunta taciremai takalman ta ijiye sanan tajuyo da kanta takalli fuskanshi tana kallonshi, harga Allah tana bala’in son Asad samada kowani d’a agidan nan, why because Asad might look harsh kana ganinshi zakaga bakin halinshi but he’s weaker than any other person agidan nan dan abu yafi damunshi kan kowa, gashi da zuciyan nema dudda Asad baitaba nunawa ba ita tariga tasan yasan komi gameda halin Baban shi saisa yana gama school yanemi jari daga CBN batare daya karbi kudin Babanshi ba yabude kampanin kanshi cikin ikon Allah kuma kampanin sai albarka yake, yay wayon nanne sabida duk ranan da mahaifinsu zai juyamusu baya he will be able to take care of his family, bambamcin shi da Sharif kenan, Sharif is very nice but Asad yafishi hankali da hangen nesa dudda idan angansu kowa will go for Sharif dan physically yafi kirki and more welcoming, Asad is just a small boy daya Goya responsibility alot abayanshi saisa yake bata tausayi, she just wish zai natsu ya nemi mata ya aura koyasami natsuwa amman tsoron yanemi mace ma yake sabida baiso yagaji irin halin mahaifinshi beside ance blood is thinker than water, saisa gashinan ne kawai bakowa ke ganeshi ba. Hannunta takai ahankali tashafa tattausan sajenshi tace “kai tashi kayi salla” da kyar yabude ido, ahankali yace “okay Grandma ” tashi tayi tawuce tafita daga dakin, dakin Du’a ta shiga tabitada kallo yanda take baccin ta hankali kwance, karasawa tayi gaban gadon zama tayi tashafa fuskanta ahankali tace “yammatana atashi daga bacci, Du’a Du’a” da kyar Du’a tabude idanunta takalli Grandma cikeda bacci a ido batare datai magana ba, kumatunta Grandma taja tace “da ace yanda kikeson bacci haka kikeson cin abinci danaji dadi saisa kullum cikinki kaman ana diba ayi biyan bashi dashi tsabagen yanda yake ashafe kaman cikin jinjiri” dan murmushi tayi saikuma ta jinkirto tadaura kanta akan cinyan ta takama hannun Grandma dake kan fuskanta ta rungume ajikinta sosai ahankali tace “Grandma agidan ki kadai nasami farin ciki haka tunda aka haifeni, Grandma please karki bari Abba yakomar dani gidanshi I am so happy anan da I don’t wanna leave, da kullum sainai kuka Ya Hamad kadai ke lallaahina da Aneela” fadada murmushin dake kan fuskanta Grandma tayi tana kallonta tace “bazaki komaba ai nagayamiki sai inda karfina yakare babu wanda zai kara wahalar min dake, yanzu addu’a na shine Allah yakawo miki miji nagari” murmushi tayi sosai saikuma ta tashi tazauna takalli Grandma tace “Grandma nina isa aure ne? Ya Nana da Ya Hawwa fa duk basuyi aure ba, kumama ai sai mutum ya iya girki akemai aure ko nikuma ban gama iyawaba tayaya zanyi aure to”? sosai Grandma ke kallonta yanda take maganan saida tagama maganan sanan taja hancinta tace “har wayauma baki gamayiba dan Aneela zata iya sayarda ke agaban idanunki baki saniba, tashi kiyi salla ki shirya yau akwai office” gyadama Grandma kai tayi tana tashi ta sauka daga kan gadontai hanyar bayi kananun kalaban da aka mata sun zubo har waist dinta suna lilo kaman wata balarabiya tabude kofa tashiga bayi, ajiyan zuciya Grandma databita da kallo ta sauke sanan ta tashi ahankali tafice daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button