KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR
Zaunar daita Razika tayi akan gado sanan takoma tarufo kofa dagudu tanadan zaro idanu tace “naga mutumin jiya a falo Du’a biyomu yayi ne” cikin tsoro muryanta dabai gama washewaba sabida yanda tai kuka tace “nima shina gani bansan lokacin da kofi yafadi daga hannuna ba yanzu idan yafadi ma Grandma Yaya zanyi? Wai waye shi? Ya akayi yasan Grandma sosai har yafito daga lungun flawas din falon saman nan eh” hannu Razika tabude itama alamun oho cikeda damuwa tace “oho amman kaman Shemau tasanshi naga ta gaidashi da sauri tana ganinshi kinsan ita tadade tana aiki agidan nan ni ba’a dade da kawoni ba” shiru Du’a tayi har lokacin gabanta faduwa yake, zama kusada ita Razika tayi murmushi tayi takalli Du’a tace “sonshi kike ko Du’a”? wani irin kwalalo idanu waje tayi tace “so kuma” gyadamata kai Razika tayi tace “eh naga yanda kike ta kallonshi jiya ana koranki kinki tafiya kinata cemai thank you for saving my life keda bakima sanshi ba, sonshi kike ko? Yanada kyau sosai wlh gashi dan gayu gashi mai kudi har ana nunashi a TV, sonshi kike”? Girgixamata kai Du’a tayi tace “a’a kawai nasanshi ne tun a kano, shine yataba cironi daga rijiya saisa dana ganshi nace sainaje namai godiya” gyadakai Razika tayi da gamsuwa tace “to Allah sa shiyace yana sonki wlh danaji dadi” dan daure fuska tayi tace “ni banson maganan nan” yatsun kafarta dahar jan dasukayi yasoma washewa takalla tace “bazakije office ba? naga yatsun harsun washe kinga yau Monday fashi ranan Monday is a serious offense” Yatsun itama takalla tace “yadena zafi, tayani zabomin kaya kinga banda lafiya saina shirya natafi” hannu Razika tasa ta dungure mata goshi tace “kewai mai wayau ko” tai maganan tana zuwa gaban wardrobe dinta wani ja da bakin abaya taciro mata sabo fill tana kallonshi tace “wowwww abayan nan yay bala’in kyau, Hajiya tasai miki”? murmushi tayi tana girgixa kai tace “Aneesa tazaban min ranan damukaje shopping yay kyau” warware rigan Razika tayi tace “wlh kam yayi kyau kai yayi bala’in kyau ma, oya tashi kizo ki shirya” tashi tayi tana kallon yatsun nata jin sundena mata zafi, wucewa Razika tayi tafice daga dakin tace “saikin fito” tom Du’a ta amsata tana kokarin cire rigan dake jikinta sanan ta ijiye ta shirya cikin rigan kafin tazo gaban madubi tatsaya tana kallon kanta for the first time yau taga kyanta da ake fadi ja da bakin color ya bala’in mata kyau, zama tayi tana daukan ribbon parking kitsonta tayi a tsakiyan kan yay kaman acucu gashin goshinta sun wani irin bala’in kwanta, sanan tai rolling gyalen abayan, man baki talakata ta shafa a lips dinta dayay wani pink sanan ta tashi tana hada jakanta tadau pad tasaka dakomi da Grandma takoyamata sanan tazura wani flat takalmi mai budadden sama daya bayyana fararen cute kumbunan kafanta, ahankali tasa hannu tabude kofarta tana lekawa gabanta nafaduwa ganin babu kowa yasa takarasa karasawa wajen bene tashiga tafiya ahankali, Grandma kadai tagani zaune tana fere apple dawani karamin wuka, dago kanta tayi jin sahun tafiyanta, kasa daurewa tayi sabida yanda tai kyau tace “Masha Allah tubarkalla Du’a kinyi kyau sosai har kafan ya warke ne”? murmushi tayi tana zama kusada ita tana gyadamata kai, Hajiya tace “to dama banda shegen shagwaba naki ruwan lipton wani konewan kirki ne, kedai kawai rakin ki yay yawa, tashi ki tafi aiki yau Monday aka ciki taran latti baruwana wanan da Ogan ku yadawo ai kunbani” dan zaro idanunta tayi sai yanzu ma ta tuna Sharif yacemata this Monday Ogan su zaiyi resuming office, zumbur tamike tace “bye Grandma” murmushi Grandma tayi tabita da kallo sabida yanda yarinyar tai kyau tace “ayi addu’an fita daga gida Allah tsare” tsalle tayi kaman yar yarinya tace “tom” “kidena tsalle” Grandma tafadi tana murmushi ganin yarintarta.
Motan Grandma tashiga zama tayi driver yajata sai alokacin ma ta tuna batai breakfast ba, har campanin yakaita, yau kawai taji tana having wani irin wired feeling kaman tace sujuya su koma gida kartazo aikin.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
free page
EPISODE 2️⃣ 9️⃣
Parking driver yayi awajen parking motoci yana kallonta ta glass haryau yakasa daina mamakin inda Hajiya tasamo kyakkyawan yarinya haka a jika, yasan Zainab(Mami) baka ce to kodai mijinta irin fararen yan shuwa arab dinnan ne, bude kofa tayi ahankali tafito sanan tajuya tadauki wayanta da jakanta screen din wayan dayay haske ta kalla ganin 15mins after 9 nasafe yasa taji jikinta nadan rawa dan bata taba latti ba kuma batasan ko boss din nada kirki ba karya mata fada, maida kofan tayi ahankali tarufe tace “thank you Uncle” dan haka take kiranshi sanan tajuya tafara tafiya zuwa entrance sanan tashiga ciki, Sharif tagani tsaye gaban kantan reception yana sanye cikin cooperate kaya ba suit ba amman wando da riga yay tucking ga belt dayasa mai kyau yana duba Rolex din dake daure a wrist dinshi kaman akwai abinda yake jira, kaman yaji ajikinshi kallonshi ake yasa yadago kanshi yakalli entrance hada idanu sukayi ajiyan zuciya yasauki sanan yasakin mata wani irin cute smile yana dumfaro ta, saida yakai gabanta ya tsaya ahankali yace “you look ahhhhh mema zance”? Yay dan shiru yana kallon sama yadaura yatsanshi daya kan kumatunshi kaman mai tunani saikuma yakalleta ganin yanda take kallonshi irin ta kosa taji mezaice dinan yasa cikeda tsokana da wasa yace “you look like indon kauye” gabaki dayan murmushin datakeyi bacewa yayi tai raurau da idanu kaman zata fashemai da kuka hakan yasa yay dan dariya yace “just teasing you” saikuma ya tsareta da idanunshi da for the first time tunda tasanshi suke shiri sosai tana kallonshi kaman yayanta taji wani iri hakan yasa tadauke kanta, murya chan kasa yace “you look damn cute Du’a kaman in saceki in gudu” murmushi tadanyi kanta akasa dan tasanshi da wasa still tana wasada yatsunta, for a moment yamanta inda suke tsaye all yake gani wasa her tsaye agabanshi, ahankali yadan waiga yabi wajen da kallo sanan yajuyo yakalleta yace “I’ve been calling you baki dauka maisa” dago kanta tayi takalleshi ita bamatasan tayaya yasami number taba, saikuma tanunamai wayannata dake hannunta tace “anan ka kirani”? Wayan ya kalla yace “yes, I gave u about 3 to 4 calls I think” wayan tajujjuya takalla dan ko kadan bataji ringing ba ahankali tace “banji ringing ba” hannunshi yamika mata yace “let’s see maybe kintaba wani waje ne” bashi wayan tayi yakarba yabude ganin ba key saikuma ya kalleta yace “bari zan miki setting nashi anjima wayan nason update, yanzu dai our Boss yazo he’s in his office, maisa kikai latti, our Boss is such a wired dude fa” yay maganan kaman mai whispering din gulma da hakan ma yasa tai murmushi, tsayawa yayi yana kallonta yace “instead of kifara tsoro kinyi latti murmushi kike ko zaiyi deducting a salary ki sanan yau saikin biya bashi time din dakikaci by adding extra hours kan lokacin tashinki, oya let’s get going” yay maganan yana tafiya tana biyedashi abaya yace “zai miki tambaya, so yanzu idan kinje as normal yanda any boss zaiyi he will ask u few questions ma sababbin staff nashi, yadan miki tambaya karkiji tsoro be very bold and answer him kinji” gyadamaikai tayi suna hawa stairs, yace “and idan yace maisa kikai latti me zakice? Uhmmm kuma banaso nakoya miki karya”? yay maganan yana tunani yadaura yatsanshi akai yana tafiya, dasauri tana kallonshi itama tana tafiya tace “zance mai nakone akafa” kwalalo idanu yayi ya tsaya yana kallonta, gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya tace “wlh dazu nadebo ruwan tea shine yazube akafana yay zafi sosai saisa nai latti” tunda take maganan yake kallonta saida tagama ahankali calmly yace “kinyi kuka”? Gyadamai kai tayi da zuciya daya tana raurau da idanu tana tafiya, chak yatsaya heart dinshi nawani irin racing he feels kaman yajawota ya rungumeta ya lallasheta, jin shiru yasa tawaigo ganinshi abayanta yasa tadan zaro ido tace “menene, ka manta dawani abu ne” dan murmushi yayi yataho da saurinshi yace “no, how’s the leg now? Yadena zafi?” gyadamai kai tayi tace ” yadena” daidai nan sukakai 5th floor, tsayawa yayi daganan yace “our Boss is a bit harsh but don’t get scared okay” gyadamai kai tayi tanadan zaro manyan idanunta, dan yatsine fuska yayi yace “naaaay! I don’t like that face, now smile and go you got this” ???? yamata thumbs up da hannu dayasa tai murmushi sanan tawuce tafara tafiya mutanen dake wajen sai kallonta suke, gaban office dinshi da aka rubuta CEO taje ta tsaya, ga secretary dinshi awajen zaune gaban table tana aiki, ganin ta tsaya yasa tace “you can go in Mrs Du’a” gyadamata kai tayi batare datai magana ba sanan ahankali tadaura hannunta kan handle na kofan harwani kalan sanyi takeji sanan gently tabude kofan kanta akasa, wani irin kamshi da sanyi ne suka wani daki fuskanta dayasa tadan lumshe ido kadan sanan tabude idon kafin ahankali tasa kafanta tashigo sanan tamaida kofan tarufe ta jingina da kofan kanta akasa still hannunta duka biyun kan hannun handbag dinta data kankame gam gam tanajin wani irin sanyi tundaga kafanta har tsakiyan kanta dan sanyin office din yabaci kaman ankure AC gabaki, takai kusan 1min tsaye awurin tana kankame da igiyan handbag dinta kaman her whole life depend on it sanan ta daure still kanta akasa kaman wata munafuka tashigo har zuwa gaban hadadden table din office din ta tsaya gaban kujeran guest tana kara kankame hannun jakan tama rasa takamaimen mezatace a office din mai kamfanin nan, tunawa da maganan Sharif na kartaji tsoron yasa tahadiye tsoron ahankali tabude bakinta cikin muryanta data kara wani irin kankancewa sabida yanda ke faduwa tace “good morning Sir” takai kusan 30sec dagaidashi jin shiru yasa gently kaman wacce idanunta ke shirin fitowa sabida tsabagen rawan dasukeyi tadago kanta takalli kujeran zaman mai office, ido hudu sukayi da Asad dake zaune yana yasanya wani hadadden Italian suit white da blue, wanda keda wani monkey jacket da farin riga ke kasanshi, babu jacket ajikinshi ya rataya kan maratayan da ake ijiyewa a office dan hanging kaya monkey jacket da farin riganne kawai ajikinshi yana zaune kan kujeranshi hannunshi rikeda wasu papers dayake reviewing ga coffee agabanshi yana sipping, sai dayan hannunshi rikeda byro ko kallonta baiyiba, wani irin rawa jikinta yafara ganin Asad mutumin daya cirota daga rijiya a kano, mutumin data gani a TV, mutumin datagani a hotel hall, same mutumin da dazun nan taganshi agidansu shine kuma still take gani anan shine mai kampanin nan, the CEO boss dinta to kodai aljani ne, jitayi cikinta yawani irin murda kawai taji wani fitsari yataso mata yacika mata mara yana shirin zubowa duka acikin yan sakannin data dago kanta ta kalleshi, daurewa tayi ta harde kafafunta gam but still jikinta rawa yake takara kankame jikinta, saida yagama reviewing document din hannunshi yay signing tsaf sanan ya yunkuro ya ijiye papers din kan table sanan ya gyara zama da kyau ahankali yadago kanshi yazuba mata mayun idanunshi akanta, dawani irin sauri tadauke kanta tana kallon gefe tana kara harde kafanta sabida wani irin fitsari datakeji dake neman fin karfinta, cikin muryan nan nashi dababu alamun wasa cikinshi yace “kinyi latti awa daya da minti biyar da sakan lalatin, bayan kinzo aiki latti kika tsaya kina chatting da wani ma’aikaci anan did you know the gravity of laifin nan”? gizgiza mai kai tayi still kanta na kallon gefe, tsawa yadaka mata yace “nobody answers me with motion speak up” wanan karan batasan lokacin data saki hannayenta dake kan jakaba takai tadaura Ata wajajen abdomen dinta dan tana neman sakin fitsarin sosai, lips dinta narawa sosai tace “I am sorry sir…….” yana kallonta still yace “well your salary will tell u if I accept the sorry or not, have a sit” gyadamai kai tayi saikuma da sauri tace “okay” kafin ahankali tasa hannunta taja kujeran gaban table din tazauna jikinta na bari.