KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Da sallama Ammi tabude kofar falo Hajiya na zaune kan kujera tana karanta news, ganin Ammi da Du’a datai butu butu ga jacket daure a wrist dinta idanunta sunyi ja yasa tasauke jaridan dake hannunta takalli Sharif dake tsaye gefensu saikuma ga Asad da tana kallon fuskanshi taga kalan bacin ranshi, juyawa Ammi tayi takalli Asad cikin fushi tace “shigo nan, shigo ciki kayi bayani da bakinka” ahankali yashigo ciki yazo ya tsaya gaban Hajiya daya kasa hada ido da ita kanshi akasa, cikeda masifa Ammi tace “i said talk Asad”! hannu Hajiya tadagama Ammi tace “Zainab yahaka! Ba’a ma Babba fada agaban karami” tajuya takalli Du’a dake tsaye tace “wuce sama kije kiyi wanka ki chanza kaya” gyadama Grandma kai tayi tawuce ahankali saida takai sama sanan Hajiya tajuyo takallesu Sharif takalla tace “Ya akayi Sharif bakacemin Du’a will stay late zaka dawo da itaba, lafiya kuka tasomin d’a haka kunamai ihu aka” tai maganan tana murmushi kaman bata gane komiba, cikin wani irin kunci Ammi tace “Hajiya wanan ne d’a” tanuna Asad da kanshi ke kasa tace “inda yaci d’a dabai wulakanta Du’a haka ba, kinsan meyayi kuwa….” daidai da abu daya Ammi bata boyema Hajiya ba tafadi mata tace “wlh yau Asad na kunyatani” dariya Hajiya tayi tace “yanzu akan wanan ne kika taso yaron nan haka kina humiliating nashi agaban kannenshi Sharif da Du’a haba Zainaba” sake baki Ammi tayi tana kallon Hajiya, juyawa Hajiya tayi takalli Asad ahankali tace “Asad” dago kanshi ahankali yayi cikeda kunya ya kalli Hajiya murmushi tamai tace “thank you Allah yamaka albarka” sanan takalli Ammi tace “wlh wlh Asad baiyi kuskure ko kadan ba, hasalima mai laifin Du’a ne” Hajiya tadanyi shiru tace “nagaya muku sabida Du’a na jikata banso kubata wani special treatment yanda Asad will punish other employees that should apply to Du’a too as well, tambayan means of identity na mutum da bank account is normal procedure dakowani organization keyi, idan batadashi yanada right yacemata tawuce tatafi duk randa tayi tadawo I love that yes! Asad shows leadership skills awajen, laifin Du’a is boss dinta yabata punishment she could have pleaded kan ya yakuri zatayi gobe that’s 1, secondly is dataje office din Sharif takarbi wayanta daganan zata iya gayamai shima yay pleading da Asad tazauna, thirdly is kodama yakoretan zata iya hanging around a mosque canteen kowani waje zuwa 4 direban ta yazo yadauketa su koma gida” Hajiya tai murmushi tace “Alhamdulillah I can now say that Du’a tafara girma, this girl spend about 8 zuwa 9yrs indoors ko falo haka ba’a barinta tasauko, tun Du’a na JS2 mahaifinta yay grounding nata, saisa idan ka dauko Du’a kasata cikin age mates dinta zaka gani she’s totally different in the sense sunfita wayau sunfita iya da sanin komi, Du’a bata taba experiencing something like this ba, so it’s time at 21yrs tasan what is life and what is life all about, thank you Asad, I promise zan kaita tabude bank sanan zamuje tayi national identity card sanan zata dawo” tunda take maganan Ammi ke kallonta harta gama tace “Hajiya yanzu bazaki ma Asad fada ba kan abinda yayi inda tabace fa” cikeda wasa Hajiya tace “idan mutum yay abin fada kinsanni nafi kowa iyama mutum fada but trust me this time Asad baiyi komi ba, and listen what all of you did today dagake Sharif Asad just shows ko bayan raina u all will stand for Du’a and support this my innocent child sanan kutayani training nata, so wlh harga Allah har cikin raina banji haushi ko riki Asad ba rather I am thankful dayake treating nata without sentiment and that’s what I want bansan sabida ni aki ayi abinda yakamata” wani irin makirin murmushi Asad yayi kawai yaje yazauna kusada ita ga mamakinsu kawai rungumeta yayi yana murmushi sosai, murya chan kasa batare dasu Ammi sunji ba yace “I am sorry Grandma I didn’t know that she will leave the whole building daban korata ba I am not that cruel” murmushi sosai tayi tana kallon Ammi dake kallonsu baki bude, tace “Yaya za’ayi ba’a shiga tsakanina da yaran nan sai hakuri Ammin su” wanan karan dariya Ammi tayi har cikin ranta takeson Hajiya, Hajiya mutum ce wlh she’s super duper educated ga iya zama da mutane ga sanin yakamata.
Daure fuska Sharif yayi yakaraso yana kallon Grandma yace “Hajiya ni wlh kobazaki mai fadaba ni zanyi duk randa yakara something like this Allah saimun kwashi yan kallo” dariya sosai Hajiya tayi tace “to Oga Sharif tuba Asad yake” lekowa Asad yayi yamai gwalo Sharif yay kwafa, tashi Ammi tayi tana kakkabe jikinta tace “tunda mu aka watsama kasa a idanu bari mu nemi hanyar gidanmu mutafi, kai kuma Asad zamu gamu agida” tawuce Sharif biyeda ita, Ammi takalli Asad tace “Ammin ka tai fushi tashi kabita” gyadamata kai yayi yatashi yafita.
Assalamu Alaykum, inaso mu gina al’umma masu tsoron Allah da tsoron hakkin dan uwanshi musulmi, I was very kind and generous nayi pages talatin da daya (31) pages awanan littafin as free, dan Allah kudubi Allah badan niba badan halina ba karku karanta idan baki biya kin shiga group ba, dan idan kikai gaskiya Allah zai bimin hakkina.
Kudin karatun this novel is 500 kacal, pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting.
you can chat me up directly a watsapp by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
EPISODE 3️⃣4️⃣
Tashi yayi yawuce yafita binsu da kallo Hajiya tayi cikeda murmushi sanan ta tashi dinning taje dakanta batare data kirasu Razika ba tazuba tuwo da miyan kuka da man shanu da nama a plate tawuce sama, bude kofanta tayi ahankali tashiga daidai tana karasa saka riga dan fitowanta daga wanka kenan, akan carpet dinta nakasa Grandma ta zaune tray sanan ta zauna tanuna mata gefenta tace “come and sit” karasowa tayi ahankali tazauna, abincin tanuna mata tace “what stain ur cloth Du’a” Murya chan kasa tace “MP ne bansamu na chanza pad ba” gyadamata kai tayi tace “maisa baki nemi Sharif kin karbi wayanki kin sanardani Asad yakoreki ba” hannu takai jin hawaye yazo mata murya chan kasa tace “kawai dayace I should get out yakoreni abin saiya dawomin da memory gidanmu yanda ake korana sama duk inda naje shine kawai nafita dagudu ina kuk…….” saikuma tasake sakin kukan shiru Grandma tayi tana kallon Du’a dan from what she’s seeing now Allah ne yaciro yarinyar nan yakawota nan danda depression yakashe Du’a tanada real bad memory of gidansu not good ones, idan ance mata yarda tahaifa Zainab zata iyama yarta haka kokuma zata iya tsayawa tanagani ama yarta haka bazata taba yardaba saisa haryau fada take da Mami, haushinta takeji sabida abinda sukama Du’a, matsarda tray abincin Hajiya tayi ta matsa jawota tayi tasata ajikinta tana bubbuga bayanta sosai tai kukanta takoshi murya chan kasa na lallashi tace “I will say and say this again to you Du’a keda komawa gidan ubanki wlh sai inda karfina yakare kinbar gidan nan har abada, kin barshi kenan so stop crying and leave you life, gobe zamuje mufara yin national Id card akwai wanda nasani zai miki yana fitowa sai mubude bank ko duka duka next week kin fara aiki kinji” gyadamata kai tayi, Grandma tace “good girl, Allah yamiki Albarka kinji” ahankali tace “Ameen” Grandma tace “ina kikaje hope nothing happened to you” girgixa mata kai tayi tace “bansan sunan wajenba mai taxi yakaini babu abinda yasameni yunwa kawai yasa nadinga bacci” dan dariya Grandma tayi tace “Alhamdulillah zokici abinci to maza” da kanta Grandma tasa hannu yashiga feeding yarinyar hakan yasa kuma taci abincin sosai kaman ba Du’a ba, tana gamawa paracetamol tadauko tabata tasha sanan tasa taje tawanke hannu tazo kanta tadaura kan cinyarta tana bata shawarwari kan yanda zatai handling any situation datake ciki ko data shiga ahaka bacci yay awon gabada ita.