KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Bai wani dadeba yadawo dakin da bowl na hadadden pepper soup da cow head, kafinma ya iso ta tashi tsaye dasauri tace “Ya Hanad kaman pepper soup ko” bata plate din yayi yace “mayyan nama kawai” dan tana balain son nama tun tana yarinya, murmushi tayi takarba dasauri tazauna tashiga ci ya tsaya shikuma yana kallonta, she looks so happy hakan made him so happy, dan yarinya ce da dawuya kaga she’s happy saisa anytime she looks happy happiness dinta is infectious sai kawai kaji kaima ka kamu da farin ciki. Juyowa tayi takallai tana tana naman kaman wata yar baby looking so adorable ganin ita yake kallo yasa tamikamai last piece na meat din tace “zakaci” hararanta yayi yace “marowaciya sai yanzu zaki bani to banci” dan dariya tayi tace “yakuri bari naci wanan gobe saimuci tare, Ya wai yaya ake dafa nama ne”? “Har yanzu ba’a barinki ki shiga kitchen?” Gyadamai kai tayi tace “ba Kaka tahana ba” gudun karta tunakomi dan yanzun nan kuma tahau kuka tasa yace “zan sayo nama saina koyamiki a kitchen din side dina” sosai tashiga jin dadi tana tauna namanta bude kofa akayi dasauri dukansu suka waiga, Mum ce fuskarta amurtuke, wani mugun kallo tama Hamad tace “mena gayamaka? Zokabar dakin nan” tai maganan tareda nunamai kofa, tashi yayi ahankali batare dayamata gaddama ba yazo yabita gefenta yafice, shigowa dakin tayi tazo har gaban gadon Du’a data sauke kanta kasa tana rikeda bowl din pepper soup din data cinye tace “ke bazakiji da bakin jinin ki kinemi yanda zakiyi ubanki yama yarda cewa ke yarshi ce ko yadinga lissafawa dake cikin yaranshi kina nan kina nema kisama dana bakin jininki ne, sabida kinga yanda ubanku keji dashi first son dinshi ga ilimi ga kyau shine zaki biyo tanan, to ta Allah batakiba bakar mayya kawai, kijechan kiji da kanki, na tsani uwarki amman naga matsalan da haihuwanki kesata ciki wlh har tausayamata nake, wayama sani ko wani aljaninne yadura mata cikinki dan naji ance tayi aljanu datana gida da kyar namijin dare yamabarta tai aure” ahankali tashare hawayen daya zubomata sharr babu abinda ta tsana irin adinga kiranta da yar aljanu ko mayu, Mum tasake wurgamata mugun kallo tace “wawiya dakikiya kawai babu abinda tasani sai zaman daki, kannenta ma sunfita iya karatu sunfiki iya komi Babanki yamaidake gidahuma yaryar aljanu kawai” wanan karan fashewa da kuka tayi sosai takai hannunta tadaura kan fuskanta tana kuka, murya chan kasa ta yanda Baza ajiba tace “niba yar aljanu bace” da sauri Mum dake tsaye kanta tace “me kikace Du’a? Mayarmin da magana kikayi? Did you just talk back at me eh?”.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
Don yin magana directly da M Shakur click on this link wa.me/+2347012181461
M Shakur nada group din Matan Aure wanda idan kinason kishiga is just 1k.
hakama idan kinason advert shima M Shakur duk tanayi.
free page
EPISODE 3️⃣
Girgizamatakai tayi ahankali gwaninban tausayi alamun bada ita takeba, cikeda mugun tsana tace “haka zaki kare rayuwanki awanan dakin, agabanki yayyinki da kannenki duk zasuyi aure ke kina nan adakinnan har tsufa bazakiyi aureba saidai ko indaga dangin ubanki aljanune wasu zasuzo kuyi wup dake, mai bakin jini kawai mara kunya” tana maganan tawuce tafice daga dakin, sosai tafashe da kuka, har bakin suka tafi su Nana suka dawo dakin nan kuka take bata denaba, dayake sun saba bawai sabon abubane kukantaba saisaima babuma wanda yabita kanta saima shirin kwanciya dasuka shigayi suka gama Hawwa takashe wutan dakin, haka taci kukan nan har batasan sanda bacci yay awon gaba da itaba.
Yau Monday sabida taci kuka batai bacci dawuri ba sai wuraren 8 ta farka, koda ta tashi babu kowa adakin saidai sababbin novels datagani manya guda uku agefenta dasauri ta tashi zaune ta dauka tana dubawa, sunan Novel din farkon The Noisy Naigbour, na biyun sunanshi the killer tree, saina ukun Disastrous Love, wani kalan murmushi tayi sanan ahankali tace “thank you Ya Hamad” ajiyesu tayi tawuce bayi alwala tadauro sanan tafito tai sallan asuba tabude Al Qur’ani tana koya Haddan da Abba yabata, saida ta tabbatar ta haddace shafi daya darabi sanan ta tashi, dakinsu ta shiga gyara musu wanda yanzu zata iyacewa a rayuwa that’s the only thing data iya gyaran daki shima da karfi da yaji takoyama kanta, ta gyaramusu gado sanan tawuce bayi tayi brush tayo wanka tafito ta shafamai sanan tasaka wani riga da skirt na atampa daya mata kyau tai parking gashinta da kyar sanan tadauki novel kaman barauniya tabude kofan dakinsu ahankali sanan tasakai taleko kadan ganin babu kowa yasa tafito duka, sanan tashiga sadadawa tafara tafiya ahankali zatai stairs. “Ina zaki”? kaman daga sama taji muryan Mami dasauri tajuyo, hada ido sukai da Mami data fito daga dakinta tana kallonta, saukar da kanta kasa tayi tana kara kankame novel dinta ahankali tace “Mami good morning” batare data bata amsaba tace “wuce kikoma dakinku ga Uwani nan zansa takawomiki break” gyadama Mami kai tayi ahankali sanan tajuya zata koma dakinsu bintada kallo Mami tayi harta shige sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tawuce tasauka kasa, hada mata breakfast tayi kunun gyada da kosai, samin kanta tayi da daukan wani karamin plate tajuyemata ragowan naman da Abban su yarage sanan ta kwalama Uwani dake wanke wanke kira dasauri Uwanin tazo tray tabata tace “kaima Du’a abinci adakinsu” karba tayi tawuce sama bude kofa tayi tashiga tana kallon Du’a data bude novel tana karantawa, har gaban Du’a tazo sanan ta tsugunna ta ijiye tray din still kallon Du’a take, ahankali Du’a ta janye novel din datake karantawa daga kan fuskanta jin kaman ana kallonta hada ido sukayida Uwani, almost 2yrs Uwani na aiki a gidansu but she thinks yaune 3rd time datake ganin Uwanin hakan yasa cikin yar muryan nan nata tace “kece uhmm yama sunanki U….uuuuu….” takasa tuna sunan dasauri Uwani tawashe baki tace “Uwani sunana mai aikin gidan nan” gyadamata kai Du’a tayi sanan tasake maida fuskanta kan novel din tacigaba da karatun dan ko kadan batada surutu kusan cikin duka yaran tafi gado halin mahaifinta indai rashin surutu ne.
Sosai Uwani takasa motsi daga wajen sai wani irin kallon Du’a take dabamatasan tanayiba, bude kofa Mami tayi ahankali ganin yanda Uwani ke kallon Du’a dabamatasan tanayiba dan ita karatun novel dinta take bilhakki yasa ta dakamata tsawa. “Uwani” firgigit ta farka daga dogon tunanin datake haka itama Du’a tadan firgita jin muryan Mami hakan yasa duk suka kallo Mami, cikeda bacin rai Mami tace “kin manta kinbar aiki a kitchen ne zoki wuce kifita” dasauri ta tashi ta taho tace “yakuri Hajiya” fita tayi Mami kuma ta watsa watsama Du’a data zubama mahaifiyar nata manyan fararen idanunta harara sanan tajuya tafice, tai kasa danso take tadaura girki, kitchen ta shiga tana duba naman data saka a wuta itakuma Uwani tacigaba da wanke wanke tana tunani sai chan tajuyo ta kalli Mami da hankalin ta kekan juya naman datake dake wuta tace “Hajiya” “ya akayi Uwani”? Mami tamata tambayan batare data kalletaba, tsayarda komi Uwani tayi tace “Hajiya kunada y’a haka maisa kuke boyeta wanan yarinya taki haka aiko shugaban kasa tafi karfinshi, maisa kuke kulle ta adaki haka” tunda tafara maganan Mami takasa cigaba da juya naman datake ta tsaya chak harta gama maganan datake sanan tace “ki tsaya a huruminki Uwani inba kinaso mu sallameki mu nemo watabane” dasauri tace “yakuri Hajiya tuba nake, kawai daman abin ya tsayamin araine” juyawa Mami tayi tacigaba da aikinta bata karabi takanta ba.