KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
EPISODE 3️⃣5️⃣
Wuraren 5 Rahima da Mariya suka shigo gidan daga school ganin Dad a kitchen yana girki yasa duk suka rungume shi cikeda murna oyoyo Dad, murmushi yamusu yadau glass cup ya tsiyaya musu juice din daya hada yace “take this now, dinner is at 7 kuje dakinku kuhuta, Aneesa na gidan Hajiya wai taje wajen kawarta, today am cooking everyone’s favorite dish in this house, tun 1 nake kitchen kunga Ammin ku ma her majesty nace tazauna and just be watching me ita kebani energy” yanuna musu Ammi dake zaune tanama yaran murmushi, cikeda murna sukace “Dad u are the best” wani irin fari yamusu da idanu yace “I know that girls kuje kuhuta” duk juyawa sukayi sukai dakinsu, shima Sharif daya shigo gidan around 6 bala’in mamaki yayi ganin Dad shi kadai yanata setting dinning, rungumeshi Dad yayi yacemai yaje yay wanka sutafi mosque yagama komi, sosai yake mamaki kannema Ammi idanu yayi irin iyye dinan sanan yawuce yatafi side dinsu, ganin Asad zaune afalo yana aiki a system yasa yadaure fuska yawuce, dan murmushi Asad yayi yace “are you gonna be staying angry for forever”? juyowa Sharif yayi yakallehshi batare dayacemai komiba, kannemai idanu Asad yayi yace “yes I want to know sabida insan kozanje na nemo wani brother ne ko saya akeyi in siya atoh” kwafa Sharif yayi yajuya yahau stairs yace “try it kagani wlh” dan dariya Asad yayi yace “I love u too” sake juyowa yayi yadaure fuska yace “who said I love you” dan sosakai Asad yayi yace “I thought u just said that” hararanshi shima Sharif yayi yacigaba da tafiya abinshi saida yakai gaban dakinshi sanan ya tsaya daga murya yayi yace “apology accepted, lemme shower nasauko muje mosque” daki yashiga wanka yayi yafito yasa wasu simple kaya sanan yafito Asad yagani dahar yay alwala yasaka wani simple riga da wando na yadi milk yasha guga, fita sukayi daidai Dad na fitowa shima daure da alwala yace “wait for me boys” tare suka jera zuwa masallaci Sharif ne kawai ke amsa hiranshi Asad ko uppan baice mishi ba, ana sallanewa baima tsaya zikiri ba yafito dan baiso sujero tareda Dad.
Shigowa sukayi gidan shida Sharif suna hira, falonsu suka shiga yahau kwalama kowa kira. “Wife, Children time for dinner a sauko” yay maganan yana zuwa sama, dakinshi yashiga baijima ba yafito yasauko kasa, dukansu suna zaune a dinning harda Ammi Asad ne kadai baya wajen, dan jim yayi saikuma yakaraso yazauna yana musu murmushi yakalli Ammi yace “jekira Asad Sweetheart, today is a special night, I’ve come back nama kowa girki yau, call him” gyadamaikai tayi ta tashi daga wajen, Rahima dake murna sosai tace “Dad nabude warmer meka dafa” tamika hannunta zata bude dasauri yace “bar bar bari, it’s a suprise bari Asad yazo kowa zai bude abincin shi” duk murmushi yaran suke, Mariya tace “Dad I’ve missed ur food sosai wlh kai chef ne” Aneesah tace “ni wani zubin kasa gane abincin wa yafi dadi tsakanin shi da Ammi” dariya kowa yayi daidai lokacin Ammi tabude kofan falo tashigo Asad biyeda ita yana tafiya ahankali fuskan nan nashi babu alamun wasa, ahankali Dad yasauke ijiyan zuciya ganin yazo sanan yatashi dasauri yajama Ammi chair yace “come sit Sweetheart yau ko tsinke bazaki dagaba kaman yanda nai promising” dan murmushi Ammi tayi tana mamakinshi zama tayi ahankali ya tsaya tabayanta yadaura hannayenshi kan kafadarta yanadan satan kallon Asad dayaja kujera kusada Sharif yazauna yana kokarin ciro wayanshi, murmushi Dad yayi yace “tom bari mufara zan bude abincin kowada kaina I will start dana love of my life, my wife that always support me and help me keep this family together” murmushi duka yaran suke banda Asad dako kallonsu baiyiba, hannu yasa yabude warmer dake gabanta lafiyayyen tuwon shinkafa ne da miyan taushi da nama, murmushi Ammi takakalo tace “wowwww, ohh banmasan mezance ba, thank u hubs” cikeda siyasa yace “don’t thank me peck me anan I prefer that” yay maganan yana nuna mata kunatun shi dan yadauko ta saitin kunnenta, ahankali tai pecking nashi, yaran sukahau ihu barinma Aneesa, komawa gefe yayi yazauna yana gyara zama yace “children u can all open Warners din dake gabanku” kaman jira suke dasauri suka shiga bude bude kowa was in awe dan Dad ya dafa fav nashi, ganin Asad ne kadai ke budeba yasa yace “saura kai Son, open it” yay maganan yanamai murmushi dasauri duka yaran suka kalleshi, Sharif dake gefenshi yace “bude muga mai Dad ya dafa maka kagani yamin fatan doya banmasan ya akayi yasan is my fav ba” dan dariya Dad yayi yace ” I know everything, open Asad” ta kafa Sharif yataba Asad akarkashin table din hakan yasa ahankali ya ijiye wayanshi yakai hannu yabude warmer rice da bean da mai da yaji da yankaken veggies wowwwwohohoo duka yaran suka shiga ihu dan kowa yasan Asad da shinkafa da wake, murmushi sosai Dad yakeyi yace “you see all na gayamuku babanku is the best” dasauri yaran sukace sure u are dad.
Gyaran murya yayi hakan yasa kowa na table din yayi shiru yace “kafin mufara cin abincin there’s something I need to do agabanku” duk tsayawa sukayi suna kallonshi tashi yayi ahankali sanan yaja kujeran dayake kai baya, ahankali yay kneeling agaban Ammi da duka gwiwowinshi biyu akasa, ware ido yaran sukayi cikeda mamaki, hannunshi ahankali yamika ya karbi hannun Ammi dake kallonshi cikeda mamaki dan this part he’s playing batasan na menene ba, chanza fuskanshi yayi zuwa serious regret face yana kallon Ammi, ahankali yace “Children bazan muku karyaba nasan Ammin ku hid everything from u all but nama Ammin ku laifi sosai da idan natuna abinda namata inaji na tsani kaina” yay dan shiru yana sauke ijiyan zuciya ta gefen ido yake satan kallon Asad dayaga har lokacin kanshi nakan wayan dayake dannawa hakan yasa yasake gyara murya yace “kunga Zainab is the best wife da kullum ina addu’a Allah yabama Asad da Sharif mata tagari kaman Ammin ku, tamin komi she has been patient and understanding dani she never complains, tanamin kome nakeso but dudda haka I hurt her” yasakeyin shiru yace “namata babban laifi da I can’t even tell u people abinda namata but all I know is I regret everybit of abubuwan dana mata, how can I hurt this beautiful woman mai beautiful heart datake rainanmin yarana tana basu best tarbiya how can I” yay maganan muryanshi na narkewa dayasa kowa yay tsit har Asad dake danna waya daina dannawa yayi but still bai kallesu ba, ganin haka yasa yace “matar nan tamin komi, and I am a bad person Nagano kuskurena and I am very very sorry, saisa I am using this chance nabata hakuri naroketa tayafemin agabanku and I want to promise her bazan karaba nabar halin nan har abada and I will be that husband datake so nazama, I will stay by her side and support ba bazan karaba, bazan karaba Zainab, kinyafemin?” yay maganan ahankali yana kallonta dayasa takasa koda motsi kallonshi kawai take dan batasan ko this part is real or fake ba, Ahankali Asad yadago kanshi yakallesu, dukta gefen ido yake kallonshi, wani irin narke fuska yayi yace “I am truly very sorry I will never hurt u again, kinyafemin?” Jin Ammi still tai shiru yaranma sunyi tsit yasa yajuyo yakalli yaran da idanunshi dasukai ja kaman wanda ke shirin yin kuka yace “kutayani rikon Ammin ku please tayafemin nasan namata laifi but I am on my kness begging” yay maganan ahankali yasake juyawa yadaura kanshi akan cinyanta yay shiru, kallon Ammi Sharif yayi ahankali yace “Ammi forgive Abba let’s move on and forget the past right Asad” shiru Asad yayi baice komiba, Rahima tace “Ammi please” su Rahima ma suka shiga cemata please dan murmushi Ammi ta kakalo takai hannunta tadaura asaman kanshi ahankali tace “nayafemaka Baban Asad, Allah ya yafemana gabaki daya” wani irin rungumeta yayi yaran sukahau ihu harda Sharif, Dad yace “thank you Thank u so much wife, Allah yabarmu tare mu aurar da yaranmu, wait I have a gift for u” yay maganan yana tashi tsaye da sauri kitchen yashiga saigashi yafito dawani jan box da akai wrapping, bata yayi yace “open it” karba tayi tasauke kan table dasauri Rahima tace “wlh I must video this, Dad is the best Allah ya iya soyayya, Allah yabani miji kaman Dad nima nai sona” kallonta Asad yayi saikuma yacire kai yamaida kanshi kan Ammi yaran kuma suka fara video, cire wrapping shit do tayi saiga wani jan box ahankali tabude wani lafiyayyen sarkan zinare ne da tsayinshi zaikai cikinta da dankunne da warwaro da zone da akalla worth dinshi zaikai 55M, wani irin ihuuu su Rahima sukahau yi suna buga dinning table din, Ammi kasa rufe baki tayi ganin saka har sarka, matsowa Dad yayi yace “bari nasamiki” daukan sarkan yayi ahankali sanan yadawo ta bayanta duk yaran na video sanan yasamata awuya ahankali sarkan har kan cikinta tsawonta gashi yama Ammi bala’in kyau ihu yaran sukahau yi, dan murmushi kadan Asad yayi yadau fork yasa a warmer yace “Zinariya left shine yanzu kagane worth din Ammi na”.