KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Sosai Dad ke satan kallonshi ganin yana murmushi harma yadau fork yanacin abincin dabai taba expecting zaiciba yasa yay murmushi aranshi yace “yaro man kaza, badai ur mother is ur weak point ba, I will shower her with love agabanka just to win u back, watch and see how I will brush ur life Asad…”

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

    ✍️ M SHAKUR 

EPISODE 3️⃣6️⃣

Murmushi Sosai Dad keyi yakalli su Rahima dake musu video yace “it’s okay children now let’s all eat and pray Allah should always keep this family happy and united” zaunarda Ammi yayi yazauna agefenta yana feeding nata abincin, saida suka gama tass sanan yashare baki yakalli duka yaran yace “so the smallest lady in this house birthday is on Friday, zamuyi celebrating, what time kikace kinaso ayi celebrating din”? yay maganan yana kallon Aneesa dake washe baki kaman anbata kyautan kujeran makka tace “Dad da daddare, I wanna make it dinner, all my friends yan Nile will be coming” murmushi yamata yace “it’s fine, ur Mum tacemin zata shigo on Thursday jibi kenan, dan haka afara shirye shirye” yakalli Ammi yace “kiyi calculating komene kuke bukata and let me know” dan murmushi tayi tace “birthday ai nata ne itada kawayen ta, babu abinda nake bukata” gyadamata kai yayi cikeda gamsuwa yace ” in that case, tashi mutafi sama abinmu muyi hira” yay maganan yana kama hannunta sukai sama yarinyar suka shiga ihu, dasauri Aneesa ta taso tazo kusada Sharif tana satan kallon Asad dake daddanna waya tace “Ya Sharif kaga Du’a itace Babban kawata” dan zaro idanu yayi yana tura baki yace “su Aneesa manya yaushe Du’a tazama best friend dinki kuma” dan murmushi tayi tace “run randa nafara ganinta tanada kyau” bayan Asad yataba yace “tashi kaji mutafi dakinsu I am so tired” tashi Asad yayi yana maida wayan dayake aljihu yawuce yabi bayan Sharif suka fita daga flat din Aneesa nabin Asad da kallo, wani irin dariya Mariya tayi tace “yarinya kinada aiki” dawami irin sauri Aneesa tajuyo takalleta danjuyamata ido tayi tace “dake nayi kike wani kallo na tashi nidai mu gyara dinning muje mu kwanta.

Suna fita Sharif ya matso kusada Asad yace “is that really Dad kodai mafarki nakeyi ne Asad” tabe baki Asad yayi yace “ohon mai” dasauri Sharif ya harareshi yace “common kaikuma saikace wani shaidan, look at what happen publicly Dad yabama Ammi hakuri fa, you know Dad ya chanza Alhamdulillah wlh naji dadi sosai, please kaima kayafemai kawai let’s all live in peace and harmony” tabe baki Asad yayi batare dayace komiba yabude flat dinsu suka shiga tare.


Wuraren 9 bayan angama breakfast Dad ya kwashi Rahima da Mariya yace zaiyi dropping nasu a school daganan yawuce office Sharif shima yawuce aiki, daga Asad wanda yamakale adaki sai Aneesa da Ammi ne agidan, shi karan kanshi yarasa meke damunshi he’s not just in the mood for office ne maybe gajiyane dan last week he work all through aikin TV.

Wuraren 9 event planner da akabama contract din birthday din Aneesa yazo yakawo lodin kayan souvenirs dinta, power bank, water bottle da set na makeup brushes ne da duk aka rubuta happy birthday ajikinsu saikuma hadaddun jakunkunan da zasu saka su aciki, ana kawowa tazura hijabi tafito Ammi dake falo tace “sai ina kuma” cikeda murna tace “Ammi zanje in taho da Du’a ta tayani hada this souvenirs a bags dinsu” haba Ammi takama tace “iyye masu birthday a dawo lpy” dagudu tafita tana murna gidan Hajiya tayi, da sallamanta tashiga falo Hajiya na zaune wani irin gudu tayi tafada jikin Grandma tace “good morning Hajiya Naaa” “jama’a na shiga uku, wlh nakusan hana yaran Ammi shigomin gida hakanan bazaku takaitani ba” dariya tayi ta tashi daga jikinta tace “wlh ko kinsa kwado saimun karya, ina Du’a Hajiya? Ankawo souvenirs dina zamuje gida muyi packaging nasu ajaka ne” tabe baki Grandma tayi tace”jetana sama, ni wlh ku tattara kutafi chan wajen Ammi ma yafimin, wanan hiran birthday naki ya isheni Aneesa” dariya tayi tace “Au haka kikace shikenan aiko bazan bari tadawo na agidanmu zata kwana yau” tai maganan tana hawa stairs, dakin Du’a tabude ahankali, zaune taga Du’a tasanya wani farin Paris t-shirt fari kall ga zanen effiltower tower ajiki, da bakin english skirt mai belt data saka dayawani irin fitoda hips dinta, kanta babu dan kwali amman tai parking kalabanta atsakiyan kai tana zane a drawing book tai bala’in kyau, dayake hankalin ta yay nisa bamataji shigowan Aneesah ba, ahankali Aneesa tamaida kofan tarufe sanan takaraso tasa hannu ta fizge drawing book din dawani irin sauri Du’a tadago kanta, kafin ma tai magana Aneesa takama hannunta taja cikin sauri tace “tashi kigani Du’a” tashi tayi Aneesa tasaketa tashiga waige waige bakin hulanta datagani kan gado tadauko tazo dasauri tashiga samata akai tace “ankawo abubuwan gift muje kitayani muyi paking ajaka” tai maganan tanayin hanyan wardrobe wani karamin dark blue hijabi ta janyo mata tadawo tabata tace “sa muje” kallonta Du’a tayi kaman mai tsoro tace “gidanku” gyadamata kai Aneesa tayi tace “eh” ahankali Du’a tamake mata kafada tace “ni bazani ba kunya nakeji” dasauri Aneesa tace “babu kowa agidan fa dagani sai Ammi daga Ya Sharif har Ya Asad duksun tafi office, su Rahima sun tafi school sunada presentation dukansu, nida Ammi ne kawai kinga kuma babu mai tayani please sa hijabin” tai maganan tana karban hijabin tasaka mata bata jira amsanta ba taja hannunta suka fita daga dakin sukai kasa, a falo suka tarar da Grandma ganinsu yasa ta tabe baki tace “agais nidai bye ku gaidamin da Ammin ku” sosai Aneesa ke jin dadi tace “zataji ai gashinan ma zan kai Du’a gidan mu daman bata taba zuwaba muje kiga gidanmu” Du’a naji tana gani tajata suka fita daga Gate dinsu suka shiga next babban gidan dake kusada su, bin gidan take da kallo gidan Babban gaske dan yamafi na Grandma girma ga tulin motoci ga security daban daban dayawa da abinma saiya bata mamaki saikace gidan yan sanda.

Ahankali Aneesa tabude kofan falo tana rikeda hannun Aneesah, ganin su yasa Ammi dake zaune kan kujera tace “Du’a nake gani agidana wato sabida kawarki ce zakizo gidan nan ba sabida kizo ki gaidani ba ko” akunyace tasauke kanta kasa hakanan take bala’in jin kunyan matan murya chan kasa tace “ina kwana Mum” “lpy lau Du’a, how are u” ahankali tace “Alhamdulillah” tashi Ammi tayi tace “come kin tsaya daga wajen ga kayayyakin nakunan ai am cikamin falo dasu” karasowa ciki Du’a tayi ta tsaya, Ammi tace “bari naje sama na kwanta feel at home ko” gyadamata kai Du’a tayi Ammi tai sama abinta, hijabi Aneesa tacire tana linekwa daga ita sai kayan bacci, karasowa kusada Du’a tayi tazare hijabinta tace “bari naje na ijiye mana hijaban adakinmu nazo kigani mufara” wucewa sama tayi hakan yasa Du’a tazauna ahankali akasa tana kokarin jan hulan da Aneesa tasaka mata gaba dan bai rufemata gaban kai da kyau ba ana ganin kitsonta tagaba da kwantaccen gashin goshinta, saukowa Aneesa tayi tazauna kusada ita tace “kinga wayan nan bags din kowanne zamusa 1 water bottle dinan, da powerbank dinan dakuma set na makeup brush dinan, ke gashima baki makeup ai wlh gobe saikinyi, gobema zamuyi aiki da yawa zanje na karbo kayan da zansaka awajen hudayya, kema harda naki zan karbo” bude idanu Du’a tayi tace “nawa kuma” gyadamata kai Aneesa tayi tace ” Ya za’ayi birthday na guda nayi dinki banma best friend dina ba” dan murmushi Du’a tayi ita bata tabayin friend ba saisa idan Aneesa nakiranta best friend saita dinga jin abun wani bambaran.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button