KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Sosai Du’a kejin hayaniya wanda tunda tazo gidan bata tabajin irinshi ba, tashi tayi dagakan gado gabanta nafaduwa hakanan ahankali tabude kofanta muryan Grandma taji dasauri tafito, jin maganganun da Grandma take duk akanta ne yasa tai hanyar stairs din tana tafiya ahankali, hango Mamin ta da Abban ta, da Ammi da Dad, saiga Grandma a tsaye tana masifa sosai yasa taji jikinta yafara rawa, su Mami sunzo su komarda ita, wani irin kuka ne yazo mata dasauri tasa hannu ta toshe bakinta tahana kukan fitowa, saikuma tajuya da gudu tai dakinta kaman mahaukaciya tana wani irin kuka kaman wacce ke hauka, memory gidansu yahau flashing akanta, rawa jikinta yafara sosai tace “no….no oooo” wani irin bude kofan sip tayi jakan goyonta na makaranta sabo da sum sayo ta fizgo kome tagani turawa take ajakan, gyalen abayan dake jikinta tadaura ta yana akanta sanan ta goya jakan tana kuka sosai, fitowa daga dakin tayi tana kalle kalle saikuma tasake komawa dakinta tai wajen window dakin, bude window tayi tana kallon kasa dan abene take, wani irin fashewa tayi da kuka tana goge idanunta da bayan hannu tace “bazan koma gidan nan ba, bazan koma ba, nooo” kawai tahau kan window kaman wanda aljanu suka shiga, runtse ido tayi kawai tai jumping tundaga saman nan har kasa aiko tafado timmm kan grass carpet din dake wajen wani irin bugewa tayi ahannu da kafa amman bata damuba ta tashi tana kuka sosai tana wani irin dingishi tana tafiya da gudu gudu sauri sauri ko kallon maigadinsu batayiba tabude gate tafice, tana fita tawani irin kwasa dagudu rikewa kafanta yayi hakan yasa tai kara, da kyar ta tashi bamatabi takan kakkabe jikinta ba ta kwasa da mugun gudu tana dingishi, Asad da fitowanshi daga Gate kenan da motanshi zashi office lokacin itama tafito ganin tafadi tasake mikewa tana gudu still tana kuka yasa yatabe baki, saka sit belt dinshi yayi ya danna waka yaja motan yana gudu ahankali.
???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
EPISODE 4️⃣3️⃣
kafin yakai gate din estate dinsu harta wuce tayi titi tana gudu sosai, fita yayi daga estate din yana jiran traffic light abashi go ahead yawuce, kaman ance yakalli side din left dinshi, ganin yanda take gudu tana dingishi tana kuka sosai yasa yadanyi jim kaman mai tunani, maganan Ammi ne yafadomai rai datamai ranan nan what if kanwar kace su Rahima da Aneesa, yatsine fuska yayi ya karya kwana yaja motan dawani irin mugun gudu, saura kiris yabugeta akan titin hakan yasa ta tsaya chak ganin mota yasha gabanta tana goge hawayen fuskanta tana kallon motan dayake tinted dan bata iya ganin naciki, saukar da glass din motar yayi yana kallonta fuskanshi babu ko alamun strictly yace “get in” girgixa mai kai tayi jikinta ko’ina narawa saikuma tafashe da mugun kuka sosai akan titi tace “dan Allah dan Allah kabarni natafi, Dan Allah Dan Allah Dan Allah narokeka Ya Asad” tunda take bata taba kiran sunanshi ba sai yau, jin yanda ake bugamai horn akan titi yasa azuciye yabude marfin motan dawani irin gudu tajuya zata tafi sabida dingishin datakeyi yasa taku daya yayi ya dauketa tana ihu ko kallon mutanen dake titi baiyiba yabude baya ya jefata ciki yay locking car, sanan yashiga gaba yaja motan dawani irin mugun gudu.
Wani irin mahaukacin kuka take a motan shi kaman yana yankata, takasa shiru, saida yay tafiya mai nisa sosai sanan yakai wani filin kwalo dake kan titi yay kwana ya shiga dan babu kowa ciki, parking motar yayi awani irin zuciye yabude motan yafito yabude bayan motan hannunshi yasa yawani irin fizgota waje sanan yabugata dajikin motan yasaka mata mugun tsawa. “shut up!” ko tari bata karaba gabaki dayan kukan datake daya kusan taushemai kunne hadiyeshi tayi jikinta na bala’in rawa, rasa yanda zatayi yasa kawai saita zube agabanshi tai kneeling looking so helpless and pitiful da zakaji kaman ma kamata kuka, kaman karaman yarinya harwani jiniyan kuka take cikin muryan bala’in tsoron shi tace “Ya Asad dan Allah kayakuri kataimakeni allow me to run, dan Allah Ya Asad karka bari su komar dani kano, dan Allah karka bari su komardani kano, dan Allah dan Allah dan Allah ya Asad dan Allah karka bari su komarda ni kano, dan Allah kataimakeni” yanda take rokonshi jikinta narawa kanta akasa dan tsoron shi ma yahanata ta kalleshi yasa yabitada kallo saikuma yay shiru still kallonta yake, yakai kusan 1min ahaka bazaka taba iya tantance yanayin shi ba yace “stand up” tashi tayi tana sauke ijiyan zuciyan kuka tana kuka, gaba yabude mata yace “shiga ki zauna” shiga tayi batare datai musu ba ta zauna, maida kofan yayi yarufe sanan yazagaya ta side dinshi yabude yashiga yazauna yadade yana kallon filin kwallon yanajin yanda take rera kuka ahankali tana sauke ijiyan zuciya sanan yajuyo ya kalleta yanda riganta yay budu budu duk kasa sabida faduwan datayi, dauke kanshi yayi yamaida gefe yana kallon filin kwallon yace “maisa bakison komawa gida” kaman jira take tafashe da kuka tace “Abban mu baya sona, Mum bata sona, su Ya Hawwa da Ya Nana duk basa sona, Kakan mu bata sona,Ya Hamad kadai kesona agidan” murya chan kasa batare daya kalleta ba yace “waye Ya Muhsin waye Ya Hamad, maisa kowa baya sonki” gabaki daya tabashi labarin gidansu dudda in a childish way ne but he understood everything, sosai take kuka tace “Ya Asad dan Allah kataimakeni kaji, dan Allah karka bari su Abba su koma dani kano dan Allah kataimakeni” tafashe dawani irin kuka mai tsuma rai tana daura kanta akan cinyoyinta, yakai kusan 2min kallon football field din dasuke ciki yake sanan yajuyoda kanshi wani makirin murmushi yasaki for the first time sanan yace “kinason in taimaka miki”? Dawani irin sauri tadago kanta da jajayen idanunta takalleshi dasuke cikemda hawaye, gyadamaikai tayi ahankali tana goge hawayen da bayan idanunta, yana kallonta still yace “are you sure kinaso na taimaka miki”? gyadamai kai tasakeyi cikin muryan kuka tace “eh” tabe baki yayi sanan yadauke kanshi daga kallonta yace “idan kinaso na taimaka miki dole ki koma gida and face ur father and ur Mum” girgixamai kai tayi wani sabon kuka yana zuwanmata tace “wlh zaku komar dani gidan nan dan Allah Ya Asad kayakuri kataimakeni karsu tafi dani” dan juyoda kanshi yayi yakalleta, zubamata mayun idanunshi yayi dayasa taji tahadiye kukan datakeyi tana kallonshi cikin wani irin murya yace “do you trust me”? hakanan taji idanunshi na compelling nata dan batasan lokacin data gyadamai kai ba tace “eh” ahankali yana kallonta yace “I will help you, I have a plan but dole ki koma” gyadamai kai tayi badan tasoba, juyawa yayi yasa hannunshi abayan yazaro wani rag, jefa mata ajiki yayi yace “first thing first clean ur body” dasauri tadauki tsumman ta goge jikinta tass dashi, wani kalan earpod taga yadauko dabatasan na mene ba, gani tayi yayi connecting nashi to wayanshi sanan yajuyo ya kalleta yace “saukar da this thing kasa” yanuna mata gyalen kanta baki, kallonshi tayi ganin yamaida hankalinshi kan wayanshi da abin daya rike a hannu yasa gently takai hannunta taja gyalen abayan kasa, yan kananun kalabanta suka wani bayyana, ga kwantaccen suman gaban goshinta, juyowa yayi ahankali yakalleta, murya chan kasa yace “come closer” matsowa tayi kusadashi ahankali hartanajin saukan numfashin shi kan fuskanta, dauke idanunshi yayi dagakan fuskanta yadaura kan fararen kunnuwanta, ahankali yadauko abin guda daya yakai kunnenta yasamata aciki yana kallon yanda takeda gashi har akunne a kwance, murya chan kasa yace “the other ear” juyoda kanta tayi fuskanta yataba kafadanshi ajiyan zuciya tasauke, gently yasaka mata sanan yakoma sit dinshi yazauna hakan yasa itama yakoma tazauna, ahankali yace “I will help you, namiki alkawari baza’a tafi dake ko’ina ba inhar u do what I will tell u, idan kuma bakiyiba u are on the own, I have one condition koda wasa karki sake kafadama wani ko wata cewa nine na taimakeki understood” yay maganan yana kallonta dasauri ta gyadamai alamun eh, yace “duk ranan da kika fadima wani what happen ranan nida nataimakeki ni din still zansa amaidaki Kanon” dasauri ta girgizamai kai, kunna mota yayi yaja yace “zanuje yanzu, I will drop u outside zaki shiga direct wajensu zaki ki gaidasu, daganan I will be telling you kome zaki fada musu sanan kome sukace zan baki amsan abinda zaki fada musu, remember say exactly what I said kingane” dasauri tasake gyadamai gabanta na mugun faduwa dan gani take kaman wayau yake mata, har gaban gidan sanan yakashe motan yajuya yakalleta yace “gyara gyalen karsu hango abun nan, and don’t show them any sign cewa magana ake miki a kunne” sake gyadamai kai yayi, ahankali yace “sauka kitafi” kallon fuskanshi tayi hawaye taji zasu zubomata murya chan kasa tace “Ya Asad dan Allah karka bari su tafidani kano dan Allah kataimaka min” yadade yana kallonta kafin ahankali yace “I will help u Du’a, now go, remember kome nafada miki repeat my words exactly” gyadamai kai tayi tabude kofan tasauka ahankali tabude gate tashiga gida bayan tabar jakanta a motan shi, saida yaga tashiga gida sanan yaja motar shi zuwa gidansu horn yayi aka budemai yay parking awajen parking lot dinsu sanan yay locking motar yana gyara zama ya kara wayanshi saitin bakinshi yanajin sautin karan bude kofan datayi dakuma hayaniya dake tashi afalon.