KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Binta kowa na falon yayi da kallo, ahankali Grandma da ranta ke abace tace “me kikayi anan” hawayen daya zubomata ta share tana gyara tsayuwanta tanajin maganan da Asad yayi sanan takalli Grandma tace “nazo wajen Abba da Mami ne inason magana dasu” kowa kallonta yake, barinma Dad dako kyafta ido ba yayi yana kara kallon halitta irin na ubangiji Baba baki Mama baka, y’a balarabiya, zama tayi ahankali agabansu ahankali tace “Abba ina kwana, Good morning Mami” anatse Babanta yace “Du’a ya kike? Maganan me zakimin bazaki iya bari anjima ba idan mugama magana da kakanki” girgizamai kai tayi ahankali sanan takalleshi tace “Abba Grandma batada lpy sosai, banson sabida ni wani abu yasameta” tsareta da ido Abba yayi sanan ahankali yace “okay to ina jinki menene” shiru tayi kusan 2min takasa magana hakan yasa Abba yace “speak up Du’a, yauzan koma kano” bakinta duk suka gani yafara rawa sosai kaman tana kokarin fighting abinda zata fadi, saikuma ta runtse idanu gam kaman daga sama duk sukaji maganan kaman saukan aradu. “Abba ni aure nakeso!” ba Abba kadaiba da Mami har ita Grandma saida tadan jinkirto daga kujera tana kallon Du’a jin maganan daya futo daga bakinta, tadauki kusan 1min idanunta a runtse sanan tabude idanunta ahankali tadago kanta takalli Abba dake kallonta asanyaye murya chan kasa hawaye na taruwa a fuskanta tace “Abba wlh ni aure nakeso, da inkoma Kano gwara nai aure” tai maganan ahankali dayasa Abba kasa koda motsin kirki hakama Mami dasu Ammi daduk ke falon, ahankali Mami tace “Du’a! Aure kikeso?” Tamata tambayan da mugun mamaki, gyadama Maman nata kai tayi ahankali tace “aure nakeso Mami” Abba da yaji ranshi yasosu sosai da kalamanta yace “Du’a kinsan mekike fadi kuwa? Aure kikeso, wazai aureki? wakikeso to ki aura eh”? Wanan karan shirun datayi yamafi nada sosai lips dinta kerawa takasa fadin maganan dake bakinta hakan yasa Abba da ranshi ke abace yadaka mata tsawa yace “I told you I don’t have all day I still have to go back to kano yau, wakike so Du’a!” Yasaka mata tsawa dabatasan lokacin da maganan tafito ba. “Ya Asad!” Tai shiru tana wani irin sauke ijiyan zuciya kaman kirjinta zai fito sanan tace “Ya Asad nakeso Abba!” Wani irin kwalalo idanu Dad yayi, Ammi batasan lokacin dawani irin kayataccen murmushi ya kufce mata a labba ba, surprise look Grandma kemata danyau Du’a takasheta da mamaki, Abba dake kallonta yace “waye Ya Asad” ahankali tanuna Ammi tace “ga Babanshi da Maman shi anan” wanan karan saida Grandma itama tai murmushi bama tagama kai karshen murmushin ba tace “Abba dan Allah ka auramin Ya Asad ina sonshi sosai” wanan karan Abba jiyayi duka karfinshi yakare Du’a humiliated him to the core dabaisan lokacin daya dago kanshi ahankali yakalli Dad ba ahankali Akuma natse yace “waye Asad”? hada idanu Grandma da Ammi sukayi kafin Abba yamayi magana Ammi ta mike zumbur dasauri tace “I think har yanzu baitafi office ba, bari naje gida nakirashi kaganshi Baban Du’a” tafita daga falon dasauri batare data jira amsansu ba Abba da kowa na falon yazubama Du’a idanu.

Gida Ammi ta shiga, ganin Ammi yasa Asad yayi kaman irin zai tada motarnan yafita ne dawani irin sauri ta bubbuga kofan motan tace “Asad wait wait” saukar da glass din motar yayi yace “Ammi what is it am late fa office zani” dasauri tace “Asad wait kashe motan kaji I have something very important to tell you, kashe kashe kafito” yanda yaga jikinta narawa yasa ya kashe yafito yana kallonta yace “is everything okay maiya faru Ammi”? Hannunshi takama tarike duka biyun tace “look at me Asad we don’t have much time but we will go into deep details later,Asad kasan nina haifeka ko, nai rainon cikinka na haifoka na tarbiyantan dakai zuwa what u are today nataba tambayanka kabiyani ko kasakamin”? dasauri yace “no Ammi” ahankali tace “tom I need u to do something for me, taimako zakayi kuma duk wanda yataimaka ma wani Allah zai taimaka mishi, at this point wata yarinya her life depend on u wlh Asad, please Asad dina, and just know this bazan taba saka kai abu mara kyau ba so u should trust me” kallonta yake kaman wanda bai gane komiba yace “Ammi maizanyi” danshiru tayi kaman wacce ke shakkan fadamai tace “inaso ka auri Du’a jikan Hajiya” dawani irin sauri ya fizge hannunshi yay baya dasauri sauri yace “no way! Ammi, kinsan mekike fadamin kuwa” cikeda damuwa Ammi tabiyoshi hannunshi tasake rikewa tace “Asad bamu da time ana jirana naso dakaine dan girman Allah that’s just the only thing I need u kamin right now, any other thing we will discuss it later, at this point kawai u need to save her ne please Asad dan girman Allah idan kana kaunata ni mahaifiyarka, Asad dan darajan Allah karka zubamana kasa a idanu, As……” Ammi! yawani irin kirata da mamaki, cikeda damuwa tace “Asad lemme kneel for u toh halan sainai hakan zakayi” takai gwuiwanta zatasa akasa, dasauri yarike mata hannu yace “Ammi don’t kneel for me” kaman zatai kuka tace “Asad I have to kneel for u inhar hakan zaisa kayarda ka taimaken ka auri yarinyar nan nagayama we will discuss d matter later yanzu kawai ina bukatan ka ceci rayuwanta ne inba hakaba tafiya da ita za’ayi, gwara na duka maka Asad na rokeka” tai kaman zatakai gwuiwanta kasa dawani irin sauri yariketa yace “ohhh ohkay Ammi naji basaikin kneeling ba” dasauri ta tashi takalleshi tace “zaka aureta”? Yatsine fuska yayi yace “yes Ammi for now just to save her kuma sabida ke” wani irin ihu Ammi tayi ta rungume shi tana kissing fuskanshi tanamai addu’a kafin taja hannunshi sutafi.

Sallama Ammi tayi tabude kofa tashiga Asad biyeda ita kanshi akasa yana cikin suit din aiki, kallo daya Abba yamai yagane yaron dan yaga program din dayayi na youth a channels television news, zama Asad yayi kanshi akasa anatse yace “ina yini Abba” ahankali Abba yace “Alhamdulillah kaine Asad”? Gyadamai kai yayi ahankali yace “tell me about ur self Asad” danshiru Asad yayi sanan ahankali yace “sunana Asad Abdullahi Kitse, I am 33yrs old, nai karatu a UK inada 2 degree my first degree is medicine I am a Doctor, sai na biyun business Administration, currently yanzu bana aiki as a Doctor, business nakeyi inada company kaina” yay shiru daidai nan, gyadamai kai Abba yayi sanan yadaga kai yakalli Grandma dake kallonshi yace “kin yarda da tarbiyan Asad Mama” gyadamai kai tayi tace “a hannuna Asad ya girma nasan waye Asad, na aminta da tarbiyan yaron nan dari bisa dari” gyadakai Abba yayi babu ko alamun wasa tattare dashi yakalli Asad yace “zaka auri y’ata Du’a Asad”? shiru Asad yayi, ahankali Mami tataba Abba, kabarda hannunta yayi batare daya kalleta ba still yana kallon Asad yace “zaka auri y’ata Asad”? kaman Asad bazaice komiba har lokacin kanshi akasa ahankali yace “eh zan aureta Abba” gyadakai Abba yayi yakalli agogon dake daure a hannunshi yaja daya saura, dagakai yayi yakalli Dad dakenan azaune kaman ruwa yacishi yace “bismillah mutashi mutafi masallaci, Asad bismillah” tashi Dad yayi, Asad ma yatashi duksu Grandma na kallonsu suka fita daga gidan, suna zaune nan shiru afalo aka tada sallan azahar akayi sai sukaji sanarwa ana adakata jama’a akwai daurin auren da makocinmu Sanata Abdullahi Kitse yakeson ku shaida, kafin kaceme kawai su Grandma sukaji ana an daura aure tsakanin Asad Abdullahi Kitse da Du’a Muhammad akan sadaki dubu dari.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button