KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

???? KYAWUNA JARABTA TA ????

     ✍️ M SHAKUR 

EPISODE 4️⃣4️⃣

Ko minti biyu basu karaba sai gasu sun shigo gidan da Sallama, Amsasu Grandma tayi suka shigo, kan Asad akasa kowa yanemi waje yazauna, Abba yadade ahaka sanan yay gyaran murya yace “Du’a” dago kanta tayi ahankali takalleshi, anatse yace “zonan gabana” gyadamai kai tayi ahankali jikinta duk yay sanyi sanan ta rarrafa zuwa gabanshi ta lankwashe kafa, hannunta yakama ahankali yarike yana kallonta yace “Du’a you always feel am unjust towards you, and kinsan wani abu u are right Du’a” Yaydan shiru sanan yace “koma yaya kike u are my daughter and hakkinki ne nakira sunanta cikin yarana so” yadan sakin mata murmushi for the first time tunda yashigo gidan yace “I hope this time around I am just dan namiki abinda kikeso, kince kinason aure kuma amatsayina na mahaifinki na aura miki wanda kikeso wanda Kakarki tayaba da tarbiyanshi bama ita kadai ba ko a masallacin anguwan yanzun nan mutane dayawa sun yaba halin Asad din hakan yakara samin natsuwa hankalina ya kwanta danhaka” yay maganan yana zare hannunshi daya daga rikon dayama hannayenta yatura hannun a aljihu yaciro wrap na sababbin 1k guda daya yadaura akan hannunta yace “ga sadakin kinan Du’a naira dubu dari, Allah ubangiji yamiki albarka” batasan mesa na hakanan taji kuka yazo mata kodan sabida wanan ne karo na farko da Abba kemata magana mai tsayi haka oho amman dai jitayi kuka yazo mata, dagakai Abba yayi yakalli Asad yace “come Son” wani irin murmushi Ammi tayi, ahankali Asad kanshi nakasa yataho gaban Abba shima, hannunshi Abba yakama sanan yadauki na Du’a daya rike yasa asaman nashi yace “ga Y’ata Du’a nan nabaka amananta, ka riketa tsakani da Allah karka cutarmin da ita, ka kulada cinta, shanta, suturanta da lafiyanta dan yanzu duka sun tashi daga kaina ko kan Kakanta sun koma kanka Asad, zuciyata ta aminta dakai dan haka nabar muku ita, yanzun Du’a matarka ce halak malak sai yanda kace sai yanda kace ayi za’ayi dan haka, idan kunso kuyi biki ko taro duk ba matsala takace Allah ubangiji yamuku albarka, zan koma gida zan sanarda Kakanki tachan cewa na aurar dake zan sanarda yan uwanki, kibi mijinki kimai biyayya Du’a, Allah yamuku albarka” yay maganan yana zare hannunshi dagakan nasu yanadan murmushi sanan yakalli Mami da idanunta sukai jajir yace “tashi mukama hanyan tafiya” sanan yatashi yakalli Dad dakawai binsu yakeda ido dankomi yafaru akan idanunshi kaman mafarki ne yabashi hannu yace “surukina sai munyi waya, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa” dasauri Dad yatashi yana kakalo murmushi yabashi hannu da fara’a yace “Ameen Ameen, zamuyi waya muje namaka rakiya” gyadamai kai Abba yayi yakalli Grandma dake zaune awajen ahankali cikeda girmamawa yace “kiyakuri Mama dakomi, zamu tafi” dan murmushi tamai tace “babu komi baban Hamad agaidamini da yara dan Allah barinma mijina Hamad” murmushi yayi shida Abba suka wuce suka fice, dakin yarage saura Mami data kasa tashi da Ammi dakuma Grandma dake kallonta, tashi Ammi tayi tadaga Mami ta rungumeta bakinta tadaura akan kunnen Mami tace “I know what u are thinking right now Zainab karki manta nima uwace, but zanmiki wanan alkawarin inhar inada rai Du’a bazata taba wulakanta na, zan kulada ita Asad ma zai kulada ita amana, namiki alkawarin nan Du’a tariga tai miji bazan miki karya ba she is in a good hands I assure u that” wani irin ajiyan zuciya Mami tasauke dan har kasan ranta taji dadin kalaman Ammi kankameta tayi tace “thank u Anty Zainab” sakinta Ammi tayi tace “yima mahaifiyarki sallama” gyadamata kai tayi sanan takarasa wajen Grandma ahankali ta tsugunna, dauke kai Grandma tayi hakan yasa gently tace “Mama kiyakuri kiyafemin kinji dan Allah” juyowa tayi takalli yarta ta ga mamakinta saitaga tasakin mata murmushi takai hannunta kan fuskanta tace “komi yawuce, Du’a tayi aure tana kuma kusa dani danhaka komi yawuce, tashi kitafi tafiyan ku nada nisa” tashi tayi ahankali Sana tajuya zata fice hartakai kofa tadan waigo tasaci kallon Du’a hada idanu sukayi hakan yasa tai sauri tafice Ammi dake murmushi tabita abaya dasauri, Du’a batasan lokacin data cire hannunta dake cikin na Asad ba tawani irin tashi cikeda murna tai kan Grandma tafada jikinta tana wuntsula kafa Grandma basu tafi dani ba wayyooo Allah na wlh dadi nakeji yayyy, tawani irin kankame Grandma da mamaki yagama kasheta tana murna, tashi Asad yayi ta gefen ido yakalleta sanan yay hanyar kofa batare daya kalli Grandma ba yace “bari naje office Grandma” baima jira respond dinta ba yafita daga falon wani irin makirin murmushi yasaki tareda biting lips dinshi ahankali yace “killing two birds with one stone feels good, ranshi fess kaman fresh madara….

Saida Abba da Mami suka wuce amotansu sanan Dad yajuya yakalli Ammi yace “what have you done dayasa Asad yace yes to this marriage dan nasan Asad ba son yarinyar nan yakeba, mekikayi Zainab” wani irin murmushi Ammi tayi da zuciyanta daya tace “rokonshi nayi, Alhaji Du’a is a very good girl, ga tarbiya gata so calm, bata bude idanu ba, kuma I am sure ko Asad bayasonta now he will grow to love her trust me and zasuyi making a very nice and healthy family, I just made the best decision for him tr……..””Malama kimin shiru” Dad yadaka mata tsawa cikeda fushi yace “what kind of nonsense is all this eh? kinzaci aure abin wasane dazaki lallaba yaronki ya auri yarinyar da batama taba burgeshi ba” ahankali Ammi tace “to inda bai aureta da yanzu sun tafi da yarinyar data kara shiga depression haba Alhaji this girl is so innocent da kallonta kadai zaisa mutum yaji bakison anything that will hurt her, Asad save this girl and muna nan dakai zaisota” cikin kunsan rai Dad yace “just stop with this nonsense idan Asad yashigo gidan nan zan tambayeshi dakaina idan bayasonta this night zansa yarubuta saki yabama yarinyar mutane and free her tunkafin wani abu ya shiga tsakanin su” Cikeda lallashi Ammi takama hannunshi tace “listen Alhaji badanniba dan Allah na yarda idan Asad bayasonta yasaketa but ba da zafi zafi hakaba mutanen nan zasuzo su tafi da ita, adan bari all this heat yalafa tukunna, inhar yasaketa yanzu zasuzo sutafi da ita kano ne that is inma basu maidata kauyen da Mamanshi ke zama ba so please kabar komi ya lafa, dansuma am sure yasami Mamartashi da sauran yan uwanshi kan yama yarinyar aure wani sabon bala’i ne zai barke, amman kaga yanzu da auren nan Asad keda iko da ita kome zasuyi suyi bazasu iya taba tafiya da ita ba kaji” shiru Dad yayi yana kallon Ammi yakuma yarda da maganan ta dan yanzu suna tafiya da yarinyar he stand no chance so dole ya yanke decision din dat is in his interest, kallon Ammin yayi yace “naji bazan sashi yasaketa ba just for now sha sai komi yalafa, my poor boy uwarka tasaka a poor kona” dariya daga Ammi harshi sukayi suna shiga gidansu Ammi tace “he will come around”, Dad yace “muje nafadima Turai da kaina nakira Dadda shima nafadamai kafin suji agari” dasauri Ammi tace “wlh amman mubari sai anjima idan ana dinner lokacin kowa na nan, yanzu zokatafi office” gyadamata kai yayi baima shiga cikin gidan ba yashiga mota direban shi yajashi sukatafi Ammi tawuce ciki ranta fess one thing is koma yayane bazata taba bari auren nan ya lalace ba saima tafara tunanin hanyoyin da she will make it work, abubuwan dazaisa danta yaso Du’a sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button