KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

5️⃣9️⃣
DUK WACCE TAKARANTA LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA.

THIS BOOK IS 500 PAY INTO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK SAIKI TUROMIN EVIDENCE OF PAYMENT TA WATSAPP NUMBER NA 07012181461.

YOU CAN CHAT ME UP DIRECTLY BY CLICKING ON THIS LINK
wa.me/+2347012181461

Sai wajajen 6 aka waste daga gidan Grandma har kawayen ta duk suka tafi yan aiki ne kawai suka rage, kaga Grandma ko ubar Amarya albarka, kawo akwati kawai amman tayi gayu kaman adauketa, karan kiran sallan magrib yatada Du’a daga bacci datayi anan kasan dakin security, jin gidan yay shiru yasa ta tashi ahankali tabude kofa tafito tashiga ciki, taga aike aketayi gidan ya kacahme ga akwatuna ko’ina afalon su Razika nata aiki da matan dake mata gyaran jiki itama tana tayasu, ganinta yasa Grandma tajuyo tai wani murmushi tace “oyoyo taho nan yanaganki wani irin, zonan zazzabi kike ne” Grandma tajata jikinta cikeda so tana taba fuskanta da wuyanta jin na zafi yasa taji dadi tace “bacci kikayi ne” gyadamata kai tayi tace “eh adakin security a kasan falonshi nadawo gida yacika kuma banso a ganni” baki Grandma takama tace “shine bakisa ankirani na nema miki waje ki boye ba, oya wuce kitafi sama kiyi wanka kizo kisha magungunan ki amiki turare, gobe su Maman ki zasuzo, jibi za’a fara shagalin biki” gyadamatakai kawai tayi ahankali sanan tawuce sama, dakinta tabude tashiga ganin yawancin kayanta an kwashe barinma na amfanin ta yasa tafito ganin Grandma natahowa yasa tace “menene”? Ahankali tace “Grandma kayana ina suke”? Murmushi Grandma tayi tace “daga gobe a side dina zaki dinga kwana saisa nai clearing abubuwan dakike amfani dasu nakaisu chance, wanan da yan gidanku zasuzo I don’t wanna take any chances wata ta takuraki ko aci zalunki, so u are staying with me all through, tafi kije kiyi wanka kizo” juyawa tayi tashiga dakin nata Grandma tabita da kallo sanan tawuce tana duba sauran dakunan sama datasa agyara sabida bakin dazasu fara zuwa ganin ko’ina fess fess har dakinda Asad ke zama yasa tafito takoma kasa wajen abincin Du’a.

Bayi tashiga zata fara wanka saikuma ta tsaya tai shiru tanason tai wani tunani amman tunanin nabata kunyan yi, wankan tsarki nadaga cikin abubuwan data iya lokacin kafin ma a dena hanata fita, kuma lokacin data fara MP Mami takoya mata wanan, banda haka kwanan nan duk idan lesson Ustaz malamin ta yazo suna fiqihu yana fadamata dalilan dakesa ayi wankan tsarki ciki harda abinda Asad yamata dazu, runtse idanunta tayi taji wani kalan shock tuna abin kafin ahankali tai wankan, wanan uban gashin nata saida tajika, fitowa tayi daga wanka tadaura towel akirji tadaura karami akanta daidai Grandma na shigowa dakin dawani kopi da kula a hannunta, baki tasaki tace “keda za’ama gyaran gashi jibi maisa kika jika kanki” juyawa tayi tai wardrobe dinta tace “kaina ke ciwo” ijiye abincin Grandma tayi tace ” bari naje nakawo miki panadol” kaya tasa sanan tai salla karfi tazo tazauna karfi dayaji Grandma ta sata agaba ta shanye abubuwan data kawo mata tass, tana zaune adaki an hanata komi daga anata magunguna sai azo amata wani abu wankan turare daga baya bacci yay awon gaba da ita.

Tunda sassafe aka tashi agidan sai aikace aikace ake itako ko tsinke Grandma tahanata dagawa saima wani special gyaran jiki da akemata nasu dilka da turare, bayan angama wata waxing din dayasa tasha kuka dan saida Grandma ma ta tsaya akanta sanan tahakura, sai wajajen one aka gama komi aka mata wanka Grandma tadauko mata wata sabuwa English atampa cikin wanda tadinka mata milk mai shegen kyau da tsada tasata tasaka, shiryawa tayi ciki aka mata dauri dudda batai kwalliya ba but kana ganinta kaga Amarya to be, dakinta Grandma tawuce da ita tace “Hamad yakirani sun shigo Abuja wai” gyadama Grandma kai tayi ahankali jikinta duk yay sanyi, murmushi Grandma tayi tace “bari nabada nama akawo miki ko kyayi fara’a” murmushi tayi kuwa Grandma tai dariya tafice, tana kitchen tana kokarin debanma Du’a nama aka taji anbude gate, Razika dake kusada ita cikeda murna tace “Hajiya sune” murmushi Grandma tayi tabata naman tace “kaiwa Du’a kiga” sanan tawuce tafita da fara’anta, motoci uku ne, Sienna Abba ce agaba, sai wata karaman mota Honda, saikuma bus din Abba wacce Ya Hamad dake sanye da kayan sojoji keja, sosai Grandma ke murmushi tace “oyoyo oyoyo” yaran ne suka fara fitowa daga mota su Amra, Aneela, Mudasir, da Muhammad suna tahowa wajen Grandma da gudu suna kallon gidan, kafin Mum ta sauko taci wani hadadden atampa fuskar nan ba yabo ba fallasa, saiga Hawwa da Nana dasuka saka kaya iri daya sunyi kyau ba laifi sai kalle kalle suke, saiga Mami itama tadan rake but she is looking okay, sai Hamad daya sauko duk suka taho wajen Grandma, motar tsakiyan kuma wata matace tafito babba ce ba yarinya ba baka tana mika hannunta cikin mota saiga wata tsohuwa tukin tafito rikeda goro a hannunta tana tafiya adudduke ranta abace kana ganinta kasan wanan tsohuwa fitinanniyar tsohuwa ce, ga uban lalitan data daura, saikuma motan Abba wanda yake shine aciki sai kannenshi maza dasuke uwa daya uba daya guda biyu.

Cikeda fara’a Grandma tai gaida dasu Mom da ba laifi basu nuna wani face ba itama ta amsa su, tana rungume su Nana da Hawwa, kana ganinta kaga classic woman sanan takalli Mami dake kallonta asanyaye tace “kaisu ciki daughter” sanan takarasa wajen Kaka cikeda barkwanci tace “kishiyata agidana Allah yakawomin gasasshiyar tsuntsuwa baki barin gidan nan sainasa mai gida ya danna miki saki” tai maganan tana kallon Hamad, hararanta Kaka tayi tace “inkin isa kisashi, kin rabani da jikata wanan ma zaki kwace min shine, nidai ki kaini daki inba sokike kafafuwata su tsinke ba nashayo wanan uban tafiyan” dariya Grandma tayi takalli diyarta data rike mata hannu dake kallon Grandma ganin hadaddiyar mata tace “barni nakaita ciki” takama hannun Kaka sanan takalli su Abba tace “Alhaji kushigo agaisa afalo wanan tsohuwan tagaji” hararanta Kaka tayi tace “dadin abin ban girmeki ba” kwashewa da dariya Hamad yayi tace “zakaci ubanka ne bakin soja kawai” falo suka shiga da already su Mom suna ciki, sun kasa boye kalle kallen dasuke, sunsha jin labari cewa Mami yar masu kudi ne but basusan kudin yakai haka ba, yanzu dama a irin wanan gidan Du’a take, lallai.

Zama duk sukayi dayake falon da girma yaci kowa yaran sai wasa suke, Kaka na zama tace “ina Du’an take” murmushi Grandma tayi tace “zatazo ta gaida ku ku huta kusha ruwa tukkuna ansha tafiya” tai maganan daidai su Razika da Shema’u dasauran yaran suka shiga gabatar da ruwan gora da drinks dabama susan irinshi ba, saida suka gama sanan Grandma takalli Razika tace “Razika kira Du’a” gyadamata kai tayi tajuya tatafi sama.

Duk suna zaune falo harda su Abba duk anyi shiru kaman kowa yakosa yaga Du’a ne, Du’a tafito ahankali kanta akasa tana gyara lullubin babban gyalen da Grandma tabata tasaka, ahankali take tafiya gabanta na faduwa takasa dagokai ta kallesu, daga Mom, Kaka, su Nana da Hawwa sun kasa yarda Du’a suke gani, har shi Ya Hamad ma, kasa rufe baki Kaka tayi tace “jama’a yarinyar nan ce dai wanan koba ita bace”? Hamad dake gefenta yace “Du’a ce Kakus” cikeda masifa tace “yoni wai wagga Y’a kara komawa aljanna take kome” batare da Grandma takalleta ba tace “yarinya tai kyau dai Masha Allah maihadinta da aljanna” daidai Du’a takarasa saukowa, ahankali ta shigo falon takasa kallonsu tsugunnawa tayi atsakiyan falon tana wasa da yatsunta murya chan kasa tace “Abba ina yini, Baffa sannu da zuwa, Kaka ina yini, Inna ina yini, Mom sannu dazuwa, Mami ina yini, Ya Hamad, Ya Nana, Ya Hawwa ina yini, Aneela, Amra, Mudasir and Muhammad welcome” duk maganan nan tayishi ahankali cikin xakin muryanta dayasa jikake dakin yay tsit.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button