KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Kaman jira Asad yake ganin sun fito yasa ahankali yafito daga motan, Kaka dake kallonshi tace “to mudai zamu tafi, saduwan alheri gobe war haka mun tsufa a kano, ga yarmu nan Asad amana, daga ganinka nasan yaran kirki ne karka yarda ka chanza inba hakaba nima zan chanza maka” dan murmushi yayi yana kallon Aneela da dasauri tazo takama hannunshi tace “Uncle idan mukai hutu nadinga zuwa” gyadamata kai yayi ahankali yana murmushi sanan yasa hannunshi a aljihu yaciro wrapper kudi yan 1k sababbi guda biyar zai sama Aneela a hannu dawani irin sauri Kaka tasa hannunta ta fizge tace “gani Babba zaka bama yar karaman yarinya kudi” dan karamin murmushi yayi yace “wanan na yarane, ga naki nan zan baki” wani irin washe baki Kaka tayi tace “auuuho to ungo Aneela jebama Ya Nana kowa yadauki bandir dai dai banda cuce” dasauri Aneela tawuce wajensu Nana, sanan yasa hannu yadauko dollars sababbi yan 100 100 yabama Kaka guda goma, karba tayi dagudu tana kallon kudin tana kara goge idanu, sanan yabama Aisha kanwar su Abba dasauri takarba tace “Allah amfana” sanan yabata guda goma again yace “gashi kibata” dudda bai kalli Mum ba tasan Mom yake nufi tace “Allah ampana” gama kallon kudin tass tayi sanan tamikama Asad tace “ni ka chanza min bansan kallan kudin nan ba” dariya duka yaran sukahau yi banda Mom da idanunta sukai jajir wato ita Asad yama maida banza, 50k yadauko yakara mata akai, godiya tahau mai sanan tace “kumuje mu shiga mota” wucewa duk sukayi sanan ahankali Asad yajuya yakalli Mami dake tsaye abayansu tanadan murmushi, akunyace yakarasa gabanta sanan ahankali yadan duka ya amshi handbag dinta, murya chan kasa cikeda ladabi yace “Allah ya kiyaye hanya Mom” cikeda so dakuma kunya Mami tace Ameen har gaban motan yarakata, dakanshi yasa hannu yabude mata gaban motan duk Mum na kallo, murmushi Mami tayi tashiga sanan yadauki jakanta yabata amsa tayi yamaida kofar yarufe yace “Allah ya kiyaye hanya Mom” direbansu yajasu, Kaka tace “wato harda budema Mamar matanshi kofa ni bai budemin ba, lallai wanan yaron, naga yana tura abu ajakanki meyasa miki” dasauri Mami tabude jakanta, envelope yasamata mai kyau aciki that is sealed, dasauri Kaka tace “mugani” karba tayi ta tattaba tace ” wlh kudi ne, yaron nan takadiri ne, wato yafifitaki sama damu ko ai shikenan ungo kayanki” karba Mami tayi tamaida jaka batare data budeba, Sheshekan kukan da duk sukaji yasa kowa ya waigo Mom suka gani tana kuka tasa bakin gyalenta akan idanunta dasauri Nana tace “Mom menene bakida lafiyane” hannun Nana ta ture tabarke da kuka sosai dan takasa rikewa tace “wlh wlh Allah ya isa bazan taba yafewa ba, an cutar dani an cutar da y’ata, anrabata da mijinta dan gidan arziki ita kuma tag do tazo tai auren kudi anan, wlh bamu yafeba, musamman nazo bikin nanne dannaga waya kwashi yarinyar nan nai dariya nai shewa amman ni za’a gumama bakin ciki wlh Zainab dagake har yarki van yafemuku cutata dakukayi ba” kaman jira Kaka take tace ” wlh tir da halinki, kin shiga uku da bakin ciki, gayamin tunda kike kintaba zuwa bikin dakika dawo gida da uban kudi, kinsan yanzu nawa muka samu akan Du’a kuwa bari namiki lissafi, ranan dasuka zo gaidamu shida suka bada miliyan biyar, ranan sa lalli suka manna miliyan kusan shadaya shida abokan shi, budan baki aka bada miliyoyi da kannenshi suka barma su Nana yaranki sabida su yan gidan arziki ne basu damu ma dakudi ba, yanzu kalli kyautan daya mana, ko kudin nan muka hada muka bawa mijinki saiya bude babban kampani, nidai Allah yawa Du’a albarka gashinan naga arziki sabida ita, babu irin zigani dabaki kan yarinyar nan ba, kika cemin mayya ce, tana zuwan miki da daddare, aljanna ce, mecece yanzu ba gashinan ba itace tai aure har mijinta ya bare ta ba, inda aljana ce ko mayya da saidai muzo muga hawan mijin takashe shi amman gashinan shine yamana wanan kyautan, bazan kara biyemiki ba, Du’a jikata ce, yar Muhammadu ce da Zainaba kiyi ki mutu shegiya mai bakin hali matsalan yaran talakawa irinki kenan yar wahala kawai” Kaka tadinga kwapkeapa mata mari Mami uppan batace musu ba sai murmushi kawai <datayi, takara yarda da komin duhu sai anyi walkiya a ga haske Allah baya bacci.

7️⃣0️⃣

Saida yaga fitansu sanan yajuya ahankali yakoma wajen motarshi yabude abubuwan daya sassayo mata ya kwaso sanan yamaida motan yarufe sanan yawuce ciki, ahankali yabude kofan falo yashiga, wani kalan sassanyar ijiyar zuciya ya sauke, dakin nawani kamshi an gyara ko’ina fess fess ga kamshin turare natashi, maida kofan yayi yarufe sanan yahayo stairs din yana tafiya da dan sauri tsabagen yanda yakosa yasa fuskarta a idanunshi, ahankali yasa hannunshi yabude kofan dakinta da wata yar sallama chan ciki yana kallonta, tana kwance kan gadon wanan karan tana sanye cikin wata hadaddiyar riga na skirt na wata Jan atampa mai bala’in kyau, Mami ta mata kwalliya tasamata kwalli da red lipstick, ta gyara mata gashinta tai parking sanan tai styling jelan gashin dayasa tai wani irin mahaukacin kyau, ko kadan bamataji shigowan shiba sabida game din datake bugawa awayanshi wanda tagani na car race dayake sound din is on ko kadan karan yahanata jin shigowan shi, kana ganin yanda take buga car race din kasan she’s just playing it ne amman tanajin jiki dudda yanzu tadanyi karfi ma compare to dazu, kamshin turarenshi dataji yana ratsa hancinta yasa ahankali ta tsayar da game din datake bugawa sanan tadan juyoda kanta ahankali, hada idanu sukayi da sauri tadauke kanta tai wani lamo akan gado tareda ijiye wayan nashi, maida kofan ahankali yayi yarufe sanan yakaraso ciki, ahankali ya ijiye kayayyakin anan gaban gadon sanan ahankali yahau kan gadon hawa samanta kawai taga yayi batare daya hada jikinshi da nata ba yana wani irin kallon fuskanta yanda ta runtse idanunta dasauri tana numfashi ahankali da baki, dan murmushi kadan yayi yanda yaga tayi kafin ahankali yace “open ur eyes” bude idanunta tayi ahankali akuma tsorace takallai, ahankali yana kallonta still yace “baki iya gaisuwa ba” dan turo baki kadan tayi tareda dauke kanta takalli gefe sanan ahankali tace “ina yini” yatsanshi daya yasa yadawo da fuskarta saitin nashi yana kallon idanunta dasuka dan sabe amman ba sosai ba yace “yaushe kika tashi” murya chan kasa kaman wacce batason yin maganan ashagwabe tace “dazu” lips dinta dayaji red lipstick yabida kallo, hadiye miyau yayi sanan ahankali kaman wanda baitaba ganin mace tasa Jan jambaki ba yasa yakai yatsar shi yataba lips din nata sanan yace “who put this on for u” cikin yar siriruwan murya tace “Mami tamin wanka” yana kallon yanda take magana kaman yahadiyeta yace “u look prett…..” kasa karasawa yayi saikuma yatashi daga samanta da sauri sanan ahankali yasa hannayenshi biyu yadagota yace “sit up” wani iri tayi da fuska kaman zata fashe da kuka sabida kuka, hakan yasa yamaidata ya kwantar yana kallon gaban riganta yanda ya kamata yana ganin saman boobs dinta ahankali yakai hannunshi yay placing saman boobs din ta saman riganta yace “sorry” dayake zafin datakeji shiyafi komi damunta bamatasan yadaura hannunshi saman kan boobs dinta ba, saima hawayen data share dahar sun zubomata, murya chan kasa yace “I’ve got some milkshakes for u zaki sha” gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi na, janye hannun nashi yayi sanan yabude jakan yadauko wani strawberry milkshakes hadda wani fluffy cake, daurasu yayi kan side drawer sanan ahankali yadagata kadan ya manna ta jikin bango gadon yasamata pillow, wani kara fashemai tayi da kuka, dazu fa da Mami na dagata tana shiryata da bamata mata ahankali kaman yanda Asad kemata ahankali kaman yar kwai batai kuka bafa sai yanzu ne take kuka amugun shagwabe itama bama tasan mesa take wani nannarkemai ba, hannunshi yasa kan fuskarta yana goge mata hawayen yace “shiiiiii” kana ganinshi kasan duka damu amman he’s still maintaining class dinshi, saida tadan huta sanan yadau karamin throw pillow yadaura akan jikinta sanan yadauki milkshake din yakama hannunta yasa mata yana kallonta yanda take sauke ijiyan zuciya yace “sha kiji ko da dadi” ahankali takai bakinta woww sanyin shi har cikin ranta takeji ga dadi dan ita dama mutum ce mai bala’in son madara, ganin yanda takeso tanama sha yasa yay dan murmushi ya ijiye mata cake din sanan yasauka daga kan gadon yace “bari naje masallaci” fita yayi daga dakin tadan zaci kallonshi sanan tacigaba dashan milkshake dinta, dakinshi yafara zuwa, sauda yafara gyara ko’ina yama dakin tsarki, danhar carpet saida ya chanza yakawo wani sabo daban yasaka sanan yashiga bayi yay wanka ya chanza kaya zuwa riga da wando masu taushi yafice zuwa masallaci, anayin magrib nai dadeba yadawo gidan ahankali yabude dakinta tana zaune yanda yabarta tasha milkshake din sosai amman still bata shanyeba tadaura kan side drawer cake din dan tsakuran shi kadan tayi shima ta ijiye tana buga car race awayanshi yakai kusan 2min yana kallonta sanan yashiga cikin dakin tareda maida kofa yarufe, baice mata komiba closet dinta yashiga hijabinta ta yadauko ya ijiye kan gado sanan ahankali yazo gabanta, hannunshi yasa yakarbe wayan daga hannunta hakan yasa takalleshi ahankali adan tsorace wani mayen kallo yamata yace “muje kiyi alwala kizo kiyi salla” ahankali yadauketa dan kara tayi sanan ta kankameshi sosai, wlh kadan yarage bai zubarda su ba dan baya yayi kaman zai fadi jin yanda tawani matseshi ahankali yashiga bathroom da ita, alaulan ma shiya mata sanan yafito da ita yazaunar da ita kan gado, da kyar tazauna yana share hawaye sanan yasamata hijabi yace “prat ina zuwa” fita yayi daga dakin, bawani dade ba yadawo da wasu magunguna akan tray da bottle water saikuma allura guda daya, aijiyewa yayi yana hada alluran, tana sallamewa hijabinta yacire mata sanan ya kwantar da ita ahankali yadan ja skirt dinta yamata alluran kafin yadagota ya balle magungunan yabata da ruwa tasha sanan ganin <ana kiran isha’i yasa yasamata hijabin yace “pray bari naje nai isha’i” sanan yajuya yafice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button