KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL

KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Amugun zuciye yay sama, direct dakin dayasan nan ne dakinsu Ammi yayi dan baitaba zuwa zaman ba dan Dad baya barinshi zuwa ko nan da chan, wani irin bude kofan yayi cikin fushi yashiga dakin yana maida kofan yarufe yana kallon Du’a data zauna kan gadon su tai crossing legs tana daddanna wayan Ammi tanadan murmushi kaman bamatasan mutum yashigo dakinba, baiyi wata wata ba yay gabanta yana zuwa wani irin fizgota yayi tsaye tareda kwace wayan Ammi ya yar yawani irin bugata da bango ya matse yana wani irin kallonta da idanunta dasukai mugun sha, cikin kakkausar murya dake nuna tsananin kunci yace “wlh duk randa kika kara fitowa waje babu hijab ko mayafi ajikinki I will shoe you the other side of me” dudda gabanta na mugun faduwa dan ko shaidan yaga fuskan Asad din saiyaji tsoro daurewa tayi tahana kanta kuka takalleshi, cikin dakewa takalli gaban riganta daya rirrike tace “saken mini riga Asad!” wani irin kallonta yakeyi batare daya saketa ba, wani kalan ihu tamai dayar muryanta tace “I said kasaken mini riga!” ahankali yana wani irin kallonta kawai yaji yana sakin gaban riganta ahankali kaman wanda ke tsoro kafin yakarasa sakinta gabaki daya, gaban rigan nata takalla sanan takalleshi ido cikin ido tace “tell me nawane sadakin dakamin wayau kabiya ka aureni I will call Grandma tamaka refunding kudinka duka, u feel sabida ka biya sadaki ka aureni bawai ina sonka ba u can do anyhow with me kana shouting kana yelling on my head kadaukeni kaman wacce batasan darajan kanta bane dakuma value kanta ba, enough I am tired of all of this, you think I am still that Du’a da aka wulakanta agidan iyayenta tahakura tahadiye and now kaima kanason kadinga anyhow dani, okay listen Asad, aure is not by force, I don’t wanna leave the rest of my life everybody na stepping on me ana cin zalina, if you are not ready to treat me with some respect please please ka kama gabanka, I don’t care after all bawai sonka nake ba, so this should be the last time dazaka kara zuwan min da this nonsense hauka display dakamin anan” tai maganan tana wucewa tai wajen kofa, kofan tabude ahankali sanan tajuyo takalleshi yanda yake kallonta jikinshi ko’ina yay freezing tanunamai waje tace “get out Asad!” Omg jiyayi wani kalan abu ya chakin mai zuciya, jiyayi kafafuwanshi da duk wani gaba na jikinshi ya sage kaman zai fadi akasa yakeji yakasa daina kallonta, kallonshi tayi eye to eye tace “I said get out kabarmin dakina Asad, as far as I am concern dagayau banda miji I don’t want arrogant, wicked and crazy man like you as my husband babu abinda zanyi dakai I said get out” tasakemai ihu sosai hawaye na gab da zubomata daga idanu amman tahanasu zubowa, ahankali yadaga kafanshi dayay sanyi sosai yafara tafiya kaman wanda zaizube akasa kafin yazo tagabanta still yana kallonta yawuce yafita daga dakin ahankali wani irin buga kofan Du’a tayi da mugun karfi sanan ta jingina da kofan tana wani irin kuka tana shafa wuyanta dayake mata zafi sosai hakama bayanta dan sosai yabugata yakuma shakemata wuya, tadade ahaka sanan ta share fuskanta tass takarasa gaban wayan Ammi daya yar akasa ta tsugunna tadauka wlh wayan yafashe, fashewa da kuka tayi sosai wani irin mahaukaci ne wai Asad.

“Du’a” taji muryan Dad ya kwalamata kira, dasauri tamike tana shashare fuskanta tace “na’am Dad ina zuwa”.

8️⃣5️⃣

Bayi tashiga dasauri ta wanke fuskanta tass tasa towel ta tsane fuskan but dudda haka idanunta sun nuna alamun tayi kuka sanan tafito daga bayin hartasa hannu zata bude kofa tafita hakanan kuma saita kasa fitan, dawowa dakin tayi taja hijabinta dake kan dadduma tasaka kawai sanan tafito tasauka kasa tana kakalo murmushi ganin Dad a falo zaune kan kujeran shi ga Sharif agefenshi sai Ammi dake zaune tanamai slicing fruits, ganinta yasa Dad yace “Allah sarki yarinya baiwan Allah gashinan har idanunki sunyi ja, yasaki kuka ko” dasauri ta girgiza kai tana karasowa gabanshi tace “gani Dad” murmushi yamata sosai yanuna mata kujeran gefenshi yace “zauna I have something for you, Sharif daukomin wata yar jaka nan adakina” Ammi murmushi tayi tana yankan abubuwan datakeyi, Dad yasake duban Du’a y’ace “Asad wutan masifan dake cikinshi yasa yadawo kaman mahaukaci ma, kinga barinma gidan yayi ko ina yaje oho, Allah yasa shiba ba on garin bane balle indamu zai bace, dan gidansu koma ina yaje dolen shi yadawo dan inada zuwa asibiti gobe” fitowa Sharif yayi da jakan dashi baimasan lokacin da Dad yadauko jakan ba, hannu Dad yamikamai yace “bani kagani Sharif nama matar d’ana kyauta” bashi yayi, budewa Dad yayi sanan yaciro wani sabon MacBook a kwalinshi yamikama Du’a yana murmushi yace “taaadaaaa, it’s yours my pretty daughter inlaw” murmushi sosai Du’a tayi tace “Dad laaaaaa, oh My God, Dad yayi kyau nagode” takalli Ammi ta tashi dasauri zatai wajenta dasauri Dad yace “ina zaki ai bamu gamaba” dasauri tawaigo takalleshi tace “zanje na nunama Ammi ne” murmushi Ammi tayi tace “koma yagama baki saikizo mugani yar Dady” dan murmushi Sharif yayi abinshi yawuce dinning dan hada coffee, sake bude jakan Dad yayi yaciro wasu hadaddun bangles na zinare guda biyu yace “ga warwaron zinaren ki kawo hannunki mugani” dasauri tamika ma Dad hannunta tana murmushi feeling so happy, ahankali Dad yakama hannunta yarike yana mamakin taushi fatanta sanan yasamata warwarayen ahankali yana murmushi shima yana kallonta yace “haka nakeson kidinga murmushi kina farin ciki kullum karki damu da Asad, gani gakuma Ammin ki we will never let u be alone” tsabagen farinciki bama ta tsaya tai godiyava ta tashi taje wajen Ammi da tagama yanka fruits din tanuna mata hannunta da kwalin Mac book din tace “Ammi kinga abinda Dad yabani” murmushi Ammi tayi tashafa kanta tace “tubar kalla akashe lpy Du’a” murmushi tama Ammi ahankali, cikeda so Ammi tace “to jeki boye adaki” gyadama Ammi kai tayi ta tashi tai hanyar stairs tai sama abinta ta ijiye, jitayi anbude kofan dakin dasauri tajuyo Ammi ne tashigo murmushi tayi tace “kina daki ma kina yawo da hijabi, cire kihuta” ahankali tacire hijabin ta ijiye Ammi tadan saci kallon wuyanta sanan ahankali takalli wayanta dake kan gadon tace “bani wayata Du’a nai dan waya” kallon wayan Du’a tayi sanan tajuyo takalli Ammi ahankali tasaukar da kanta tashiga wasa da yatsunta murya chan kasa tace “Mum sorry nafasa wayanki fadi yayi daga hannuna, wayan bamata kawowa” shiru Ammi tayi saikuma ta kakalo murmushi tace “shine kike magana haka, don’t worry anjima zansa Sharif yasayomin kin sha maganin dama hadamiki”? Gyadama Ammi kai tayi tace “eh nasha” murmushi Ammi tayi tace “to zauna kihuta abinki gobe nafita idan sun tafi asibiti tunda basa zuwa damu muduba gari ko” gyadama Ammi kai tayi da sauri tana dan murmushi Ammi tajuya tafi, tai hanyar dakin Sharif dake nan saman.

8️⃣6️⃣

Sharif na kwance yana waya ayanda yaga Ammi ta shigo tafada kan kujeran dakin tadaura hannunta akan idanunta tana goge kwallan daya zubomata yasa dasauri ya ijiye wayan yatashi zaune yace “Ammi menene jikin Dad yatashi ne?” Girgizamai kai tayi tama kasa magana sai share kwalla datakeyi, dasauri yazo gaban kujeran datake zaune yana kallon fuskanta yace “Ammi menene, why are u crying” ahankali tace “Sharif is Asad” saikuma tafashe da kuka cikin kuka tace “narasa wanda zan sama Dad dinku ba lafiya, Sharif yazanyi da Asad eh? wani kalan murdadden yaro ne Asad”? Ahankali Sharif yace “Ammi mai Asad yamiki kuma” murya chan kasa Ammi tace “ina kitchen na aika Du’a takaima su Baban ku juice, wlh Sharif ina kitchen saida naji tsawan da Asad yadakama yarinyar nan ya kadata daki, shine nafito dasauri koda nafito naga shima yayi sama hakan yasa ban bishi ba, yanzun nan nashiga dakin kaga yanda wuyan yarinyar nan yay jajir abunka da fara fata, wayana itama yafasa, is Asad beating dat girl!” dasauri Sharif yakalli Ammi ahankali yace “no Ammi Asad bazai daki matarshi ba haba saikace baida hankali” shiru Ammi tayi tace “Sharif bansan wani kalan hali Asad kedashi ba, kwanakin baya I was so happy dan nadauka yafara sonta, wanan dayafara dukan yarinyar wlh bazan yardaba nama iyayen yarinyar nan alkawari zan riketa amana, I love Du’a dabazan taba bari kodan cikina yaci zalunta ba, bani wayanka kagani” ahankali Sharif dake kallonta yadauki wayanshi daya bari kan gado yabata, karba tayi tai dialing number Asad takirashi yakai sau biyar amman bai dagaba zata kara kiranshi na shidda ne Sharif yakarbi wayan yace “Ammi please let him be, zai dawo, shima kanshi yayi zafi” cikin fushi sosai Ammi tace “yazo yabani takardan ta dudda yariga yamaidata bazawara but that’s not the end of life” wani kalan kallo Sharif kemata ganin ranta abace yasa baice mata komiba kawai sai hakuri daya cigaba da bata, wasa wasa har dare yayi dayan dare yayi Asad baidawo gidan ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button