KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL
KYAWUNA JARABTA TA COMPLETE HAUSA NOVEL BY M SHAKUR

Ance rana bata karya ko, yau asabar ranan biki, gabaki daya Du’a farkawa tayi kaman ma batada lpy, kana ganin fuskanta kaga fuskan wacce jira kawai take ko murmushi ne kamata tafashe da kuka, gashi tayi wani arnen kyau tai fresh, yau magungunan da kalan wankan turaren da aka mata daban ne, biyonce makeup artist aka dauko tamata makeup ta shirya cikin wani white gown aka gyara gashinta da Solange tamata akai parking aka mata dauri da head dinta aka zubo da gashinta ta tsakiyan ashoki, subhanallah, yau duk kunyan Mami dataga yarta rungumeta tayi sai kawai tahau kuka, shigowa Asad yayi shida friends cikin shadda da za’ayi couples pictures photo shoot, duk iskancin shi da boye abinshi saida ya rungume matarshi agaban kowa yana ganinta su Rahima sukahau ihu, Mami kuma tashiga daki kunyan siriki, sanan ahankali yariketa yamanna mata peck a forehead aka dauki hoton, kana ganin Asad kaga akwai wani special happiness dayakeji na musamman yau, kusan 2hrs akayi ana hotunan sanan suka sake mata manni shida abokanshi tunda ba dinner zokaga kudi afalon Grandma harda dollars dan da Asad da Yayan Mami da matarshi dasukazo jiya da daddare dukda dollars suka mata manni, Mom da yaranta sai suka dawo yan kallo. Sha’aini akayi nagani nafadi manyan mata na minitoci da ministers duk sunzo bikin manya gidaje biyun nan sun cika makil, tun around 1 Du’a tafara kuka sabida yanda duk wanda zaizo fada ake mata akan zaman aure, gabaki daya batada joy tai zuru zuru tai wani shegen kyau kuma.
Wuraren 5 sabida Asad ja’irin yaro ne mara kunya motocin abokanenshi sukai layi kofar gidan Grandma wai sunzo daukan Amarya, da Ammi taji labarin salati tahauyi tace “jama’a yau naga da, wai Asad harya tura motoci yo saikace wani gari za’a kai Amarya”
Wani sabon wanka Grandma tasa Mami tamata na turare bayan tai sallan magrib sanan aka kawo wani lafiyayyen lafaya aka sama ta sarkan gold aka shiryata tsaf aka lullube mata fuska sanan Mami tafito da ita aka kaita wajen Kaka fada tamata sosai sanan tace dare yayi tagaji amman gobe zatazo yaduba gidan nata, sanan aka kaita wajen Abba da kannenshi fada suka mata sosai dayasa tasha kuka sosai, fitoda ita akayi ana waka ana rawa aka kaita gidan yan uwan mijin, Ammi rungumeta tayi sanan tamata kyauta na darham dubu daya suma ne kawai Mom batayiba sanan aka mata wazai, Ammi tasa tai sallan isha’i sanan aka fito da ita, akofar gidansu taga Grandma tsaye tana magana dasu Sharif dawani irin sauri ta fizge hannunta Grandma jitayi anririketa ana kuka sosai, tace “Grandma dan Allah ni awajan ki zan zauna please Grandma, dan Allah bazan ba” duk dauriyan irin na Grandma saida tadan koka rungumeta tayi sosai tana mata wasu maganganu akunne, sanan takaita tasata amota tarufe sosai Du’a ke kuka kaman zata mutu, Grandma ma Hawaye ta shirya tana tsaye aka wuce da Du’a amota zuwa gidan mijinta, Kaka da Mami ne kawai basu bitaba ita Kaka gajiya ce dan dataje, amman Su Mom da Nana duk sun bisu.
Wani anguwa sukayi acikin Asokoro District, anguwan shiru babu hayaniya gaban wani dankareren gida da ita kanta Mom gani tayi yafi na Grandma da gidan iyayen mijin dayake Minister ma kyau, wani security mai uniform ne yabude gate din motoci suka shiga, Allahumma Barik! Mom taji Nana dake kusada ita tafadi sabida haduwa gidan, parking aka yiyyi suka fito, Babban kanwar Grandma da Grandma ta damka mata amanan Du’a da matar Muhammad Yayan Mami ne suka fitoda Du’a daga mota kanta na kasa, gasu Rahima da Mariya banda Aneesah, gawasu yan uwa, da kanwar Su Abba itama sai kalle kalle take baki yaki rufuwa ana rawa ana wakokin kawo amarya bismilla akasa tayi sanan tashiga gidanta da kafan dama jama’a suka bita, wani irin mad penthouse ne gidan, ya ilahi! bene biyu ne dana farkon falonta, sama nabiyun nashi, bango Mom tadafa jin tana nema tasume to kodai mijin ne suka mata kayan dakin nan! Dudda su Mami nada kudi ina uwarta taga irin wanan kudin, nan ko batasan Muhammad da Grandma ne suka mata komi ba, kayan da Abba ma yamata a guest house aka dankasu kayan kitchen ne aka debo aka kawo aka danki dasu a store dinta, kuma Abba yay kokari yamata set na gado da kujera guda daya daya masu kyau sai kayan kitchen. sama aka kaita tana wani irin kuka sanan aka zaunar da ita akan lafiyayyen gadonta, wani kunu da Grandma tabama kawarta a flask cewa ana zuwa abata tabude tace “gashi shanye Du’a Grandma dinki tace na makesure kinsha, please kidena kuka idanunki sun kumbura dayawa” gyadamata kai tayi sanan takarbi flask din takai baki, itadai batasan kynun me wanan ba amman all abinda takeji is dabino, kwakwa, dakuma abu kaman yogurt kunun dai dadi, kira yaran duka sukayi wajen dakin suje suga gida, ga gidan kamshin turaren wuta sanan da kanwar Abban ta, da kawar Grandma da Matar Baffa Muhammad, da Mom dake wajen dabata cewa komi suka shiga yimata fada sosai ana mata nasiha mai ratsa jiki, kaga Du’a saita baka tausayi, wuraren 10 abokanen ango dake jiransu awaje suka keko sukace munzo tafiya da manya, baki Kanwar Abba takama tana murmushi tace “Baza abarmu mu kwana ba ai shikenan, kumuje su Nana sa zauna ayi siyan baki kafin adawo dasu” sosai Du’a tahau kuka saukowa tayi daga gadon zata bisu amman suka sake maidata suna bata hakuri sanan suka tafi, su Nana suka shigo dakin, zama kusada ita Mariya da Rahima sukayi, Rahima tace “common Du’a kukan ya isa haka idanunki sun kumbura” make mata kafada tayi tana kuka kaman wata baby tace “ni wajen Grandma zan koma” kallon junansu sukayi harda su Nana sanan dukansu suka kwashe da dariya Du’a takara fashewa da kuka, zasuyi magana sukaji anyi sallama, dasauri kowacce ta gyara, Rahima tace “anzo siyan baki ba mutunci, idan basu bamu 10M ba bazasu ga Amarya ba” zaro idanu Nana tayi jin yanda ake kiran kudi, Rahima da mariya suka tashi sanan suka kalli su Nana ganin sun zauna yasa tace “kutaso muje” tashi sukayi suka bisu kasa, wasu hadaddun classic men ne gayun abuja afalon a zazzaune harda Asad dake sanye da wata white shadda yakafa hula yay wani irin bala’in kyau yana daddanna wayanshi, kana ganinshi zakasan shine angon but yanda yakeyi bazaka dauka shine angon ba, yana zaune yana jinsu Rahima tadage aiko saida takarbi 10M din sanan tace “bari nakawo muku Amarya” “Ke” sai alokacin Asad yay magana, duk kallonshi akayi harsu Nana, kofa yanuna mata yace “kuwuce kubarmin gidana I am sleepy” kafin ma Rahima tai magana abokinshi su Jabir sukahau mahaukacin ihun shakiyanci afalon, Sharif ma murmushi kawai yayi yatashi yace “kunga kutashi muje mu sauke yaran nan mutafiyan mu tunda mu dan iskan nan yake kora, don’t worry mumadai mun kusa shiga daga ciki” yatsine fuska yayi kaman bada shi akeba yadanyi murmushi kadan yacigaba da danna wayanshi, yana zaune awajen duk suka fice, saida yaji karan motansu da fitansu da rufe gate din sanan yatashi ahankali, rufe kofan falon yayi da key sanan yawuce kitchen wani hadadden warmer yabude yadau plate yaciro wani grilled chicken yasa a plate da fork sanan yadauka a tray yafito daga kitchen din yay sama, dayazo falon farko saida yaji sound na kukanta tsayawa yayi yana sauraron yanda take kuka ahankali tana kiran sunan Grandma sanan yawuce saman shi, gawani irin mad palour awajen da akamai wani design aka zuba wasu beds kujeru awajen da complete wall TV, falon anyishi kaman cinema, wani daki yabude Ya Rabb! dakin komi is off white gadon ciki zaka dauka gadon sarki ne, ijiye tray yayi kan lallausan carpet din wajen sanan yabude kofa yafito yasauka, ahankali yabude kofar dakinta da sallama abakinshi, dago kanta da sauri tayi takalleshi gabanta nafaduwa, hada idanu sukayi ahankali tasa bayan hannunta dayasha lalle ta g0ge fuskanta lips dinta narawa.