MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kallonsa Daddy yake ransa na Fari,Aransa yana ta Fadin masha Allah,waya ya daga ya kira Hajiya binta yace akawoma Bako Ruwa da lemo,ai ba’a dauki muntuna ba,sai ga Atika da Tire niki niki da lemuka da Ruwa ta ijiye gaban Saleem bayan ta duka ta gaisheshi,ya amsa bai kalli ma inda take ba idonsa na kasa.
Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Bari na barka kasha Ruwa ka huta kafin nazo muyi mgana ko..? Mirmishi Saleem yayi baice komai ba har Dadddy ya Fice daga Falon jikinsa na rawa,Da kallo mai kama da harara Saleem ya bisa kafin ya saka hannu ya dauki Ruwan swan ya tsiyaya akofi yasha,Ajiyewa yayi yana sakin ajiyar zuciya Lokaci daya yana bin Falon da kallo Yana mele baki
Bai jima ba,sai ga Daddy ya dawo yana ganinsa yayi kasa da kai kamar wani na gari,nan ko zaginsa kawai yake aransa,domin hardashi abada Gudummuwar Wulakancin da Malika tayimai,kusa dashi Daddy ya zauna yana Dafa kafadansa kai tsaye yace”Sannu da zuwa,hop kazo lafiya..?
Saleem ya amsa da cewa”Alhamdulillah..”Alhaji Abdulmalik yace”Masha Allah nasan dai mahaifinka ya sanar dakai komai ko..”,?Gyada mai kai kawai Saleem yayi,kafin ya cigaba da Fadin”Toh naji dadin hakan,yanzu Abunda nakeso dakai kamar yaushe ne kake bukatar ayi auren …?
Saleem yaji ransa Fes,ammh sai ya basar yana Kara sadda kai yace”Daddy duk yadda kuka tsara ni awajena Daidai ne..”girgizamai kai Daddy yayi kafin yace”A”a ba ahaka Saleem ai kaine zaka zauna da ita,kai ya kamata ka sanar damu zuwa yaushe kakeson ayi komai agama..”Shuru yayi kafin yace”nan da Wata daya yayi Ko…,?
Daddy yace”Yayi sosai ma,Allah ya nunamana yanzu kana wani aiki ne…? Saleem yace”Ina aiki a zamfara ne,karkashin wata headquter,a mtsayin Acp…”Washe baki Daddy yayi yana buga kafadansa yake Fadin”Wow Bravo…Ashe magajinn kumo ne,gaskiya am so happy to hear dat,Allah ya taimaka..”Yana mirmishi ya amsa da Ameen.
Gyara zama yayi yana Fadin”Kana da muhallin ma”ana wajen da zaku zauna…? gyada kai Saleem yayi kafin yace”Eh inada dan madaidaicin gida anan zamfaran…”Shuru Daddy yayi kafin yace”Toh babu laifi,ammh akwai Abunda nakeso na sanar dakai,bawai don zaka auri yata ba A”a don kaima kana mtsayin Dana ne ko ba malika zaka aura ba,zan maka dukkan Abunda yakamata..”
Saleem ya jinjina kai yana Fadin”Hakane Daddy…”Yace “Toh Abu na Farko Shine bani son ka kashe sisinka amganar auren nan bayan sadaki,duk wani Abun bukata,kama daga lefe da gidan da zaku zauna duk zan tanadar muku kaji..”Mirmishi Saleem yayi kafin yace”Ayi haka Daddy…’Kafadansa ya dafa yana Fadin”Karka damu Dukkanku ya”ya ne,so yanzu sauran mganr zamu tattauna da mahaifinka kaji ko,Allah yayi maka albarka yakuma baku zaman lafiya..”Afili ya amsa da Ameen ammh cikin ransa ba Ameen ba yake fadi ba,yana ayyana yadda rayuwarsa zata Cutu matukar Allah yabasu zaman lafiya da wanchan tantiriyar yar iskan.
Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Yanzu zaka Wuce ne,ko akirama ita ku gaisa ne?.”(Shima dai kawai ya Fadane kada Saleem din yagano ita malikar bata sani ba…) Saurin Girgiza kai saleem yayi yana mikewa yace”A”a Daddy rabu da ita,zan dawo insha Allahu,yanzu ma ina Sauri ne aiki yayiman yawa a office ni zan koma…”Daddy yace”Haba ka tsaya kayi lunch mana!Saurin girgiza kai yayi yana Fadin”ngd daddy…”
Bai hanashi ba illah Shiga ciki dayayi ya kira Hajiya binta suka gaisa,wanda itama ta yaba da Saleem din,kuma aranta tana ganin Malika ta samu daidai da ita,har bakin mota Daddy ya rakasa yabashi rafar kudi yan Dubu ammh Saleem yaki karba sai da yaga ya nuna baiji dadi ba kana ya karba,har ya Fice daga gidan yana dagamai hannu da Fatan Allah ya kaishi lafiya.
Saleem na tuki yana cin dariyan Ladabin karyan dayayima su Alhaji Abdulmalik,domin harga Allah baya wani ganin mutumcinsa,kawai yana mai na yan Duniya ne,ammh ina Abun girmawa anan wajen,yana babba ammh sam baida Tunani yabar yarinya na Abunda taga dama,ammh no wahala karshenta ya kusa zuwa,domin dama yace wata daya ne don ayi komai a Wuce wajen,Yaci burin yadda Adare daya malika ta chanzamai rayuwa,shima yayi al”kwarin chanzamata shi awannin goma ne bama sai an kai ga cikar dare ba,kudin daya bashi yake kallo yana harara,yana fadi afili,”Dole mana kabani kudi,Tunda za”a Tusa min Ragowar arna,yaga yaro shar zai makalamin tsohuwa,yo tsohuwa man wanda naba shekara daya,ai ta tsufa…”yafada yana sakin tsaki yana cigaba da hararan kudin kamar sune Alhaji Abdulmalik din.
***
Saleem bai kira Abbi ya sanar dashi Abunda ya wakana tsakaninshi da Alhaji Abdulmalik dan kasuwa ba,shi da kanshi ya kira Abbi ya sanar dashi komai kuma yana kara yabawa da Saleem din,Ada Abbi yaso yayi Turjiya game da Cewar dayayi sadaki kadai yake bukata,ammh sai shi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ya nuna daga Saleem din har Malika shi uba yake garesu,saboda yana da hakkin yimusu dukkan Abunda ya kamata,nan yake sanar dashi ya tsaida mganar auren nan da wata daya,.
Abbi yaji dadin karamcin Alhaji Abdulmalik har ya nuna yana so yan”uwanshi baffanninshi da suka rage akumo zasu agabatar da neman aure,Alhaji Abdulmalik ya dakatar dashi da cewa basai sun zo ba ai duk Abun na gida ne,su bari Ranar daurin Aure sai suzo tare da Sadaki,babu komai shi ya riga yaba saleem malika har Abada,da wannan mganar sukayi sallama cike da Farinciki.
Abbi baya da zabi illah sanar dasu Ummi halin da’a ake ciki,wanda Hajiya ce kadai ta nuna murnanta Afili ,ammh Saleema da Ummi Kamar su fasa ihu saboda bakinciki,Saleema ta bude baki tana Fadin”Haba Abbi yanzu Fisabillahi in yaya Saleem baida hankali da Tunani sai ka biyemai,yanzu don Allah duk matan Duniya yarasa wazai aura sai Wannan yar iskar…?
Tafada idonta cike da kwallah,hararanta Abbi yayi yana Fadin”Kul na sakejin kina kiranta yar iska,iskancin me tayi miki toh zan sabama miki wlh in bazakima dan”uwanki Fatan alheri ba juz keep ur mouth shout tunkafin na saba miki wawiya kawai…”,Yafada cikin Fushi.
Saurin mikewa tayi tana kuka ta Wuce zuwa dakinta,Ummi dake zaune batace komai ba,Hajiya ce ta kalli Abbi tana Fadin”Wai ni kabiru Meye dalilin da yaran nan basu son Auren nan,kodai ba diyar kirki bane…? Ummi tayi Saurin taran hajiya tana Fadin”Wlh bs diyar kwarai bace Hajiya,Yarinyar kwata kwata batayi kama da…”
“Aisha…..”Abbi ya katseta da tsawa yana kallonta,shuru tayi da bakinta tana Jin wani daci aranta,Bai kara mgana ba ya tashi ya haye sama ammh daga yanayin kallon da yayimata Jikinta yayi sanyi,tashi tayi tabi bayanshi batare data kara cema hajiya komai ba,.
Hajiya tabe baki tayi ta mike tana Fadin”Allah ya kyauta…”Daga haka ta shige dakinta Ranta fes Domin Dama babban burinta shine su Saleem suyi aure tagaji da ganinsu haka ba iyalai.
Shiko Abbi yana Shiga daki sai ga Ummi ta biyo bayansa tana Shigowa ya tasomata yana Fadin”Haba Aisha meyasa kike haka? ke yanzu Abunda kikayi Yayi kama da Abunda uwa tagari zata aikata,kada kimanta kema kinada Diya mace,in aka aibatata zaki ji dadi? kada ki manta Allah shi ke shirya wanda yaso ya batar da wanda yaso,nasan kuma kina da sani kan hakan bayan karatunki na Shari”a low kina da karatun Addini daidai gwargwardo,why kika aikata haka?
Yafada yana kallonta kur da ido ganin yadda jikinta yayi sanyi ne yasa ya juyamata baya yana Fadin”Kin bani mamaki Aisha,wlh ayadda na sanki mai hankali da hangen nesa banzata zaki ki bada goyon bayan Saleem yayi jihadi ba,baki Tunanin in ya aureta ya natsarta da ita,dani da ke dukkanmu munada lada? Gaskiya ban zan boye miki ba u already disoppoiting me Aisha…”