MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


Saleema ta cika alqawari tazo bikin Nadira,wanda Sai dai Zahra ta ganta kwatsam suka kama aikama juna kallon mamaki,Zahra ita tafarama Saleema mgana inda ta bata hannu suka gaisa tana tambayanta su Ummi,itako Saleema Karema Zahra kallo take yadda Rayuwa ta Horata Duk ta yi sanyi kamar ba ita ba,Ace yau Ana bikin Nadira ammh Zahra na Zaune waje daya cikin Natsuwa ba iyayi ba hayaniya ba Rawan kai,lalle Ruwa ya Daki babban Zakara kuma Gani ga wane ya ishi wane Tsoron Allah.

Saleem bai samu Zuwa Daurin Aure ba,ammh Abbi yazo Har suka Hadu ta Saleema ta biyoshi suka koma Katsina tare,dama tana son Zuwa weeked,amota take ta bama Abbi lbrin yadda taga Canzawar Zahra,Abbi sai yayi amfani da wannan Damar ya dingama Saleema Nasiha wanda suka kashemata jiki sosai takuma yi alqawarin yin amfani dashi…

Anyi taro lafiya an kai Amarya Lafiya,ta tare agidan Mijinta dake kusa da Asibitin murtala,,Tsakaninsu da Gidan ya Nadir Babu Nisa,Flat hudu ne Uku na matanshi daya kuma nashi ne,to cikin dayan ne aka Saka Nadira komai dai achan achan sai wanda ya gani,Sai inda ma kayi Ra”ayi ne zaka So ganin wata kishiya,ammh sai ka Wuni a Shashenka bakaga Gilmawar kowa ba,kowa na barayinshi sai ko in An hadu agaisa,kowacce cikinsu ta iya kama girmanta da kuma Salon kishinta yayinda itama Nadira ta iya jan kankanta da kuma Salon Jawo Hankalin Mijinta gareta,ammh batare data Cutar da abokan zamanta ba

Momyn ladingo..”

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

36

…………….”Lokacin da Bikin Saleema da Sadiq ya rage Saura Wata daya Takardan Transfer din Saleem ta Fito an maidashi Headquatersu ta Katsina, POLICE HEADQUATER AIRPORT ROUNDABOUT KATSINA STATE Murna wajen Malika ba”a mgana dama Tafison su koma katsina da Zama ta gaji da zaman Zamfara.

Nan da nan suka Fara parking din kayansu na Sawa,Domin komawa katsina,wanda Malika keta murna har Maman Abba na mata Tsiyan zata tafi ta barta,dariya tayi tace haba ai ko Birnin Sin ta koma suna Tare bazasu taba Rabuwa ba,Sati daya da Samun Tranafer din Suka gama duka parking din Abunda zasu dauka sukayi sallama da makota,shima Saleem din already yagama Sallama da Headquater nasu,bayan ya mika Sauran aikin zuwa ga hannu sabon Acp wato Shugaban wajen na yanzu.

Maman Abba ta zama kawar alqawari don da ita suka dumguma Zuwa katsina gidan da Daddy yabama Saleem wanda koda suka isa Hajiya ta tura musu su Dose sun gyara gidan,sun musu abinci,babu Abunda ya samu gidan,domin ana kula dashi Sosai,ga motocinsu guda biyar Nashi Biyu na Malika biyu wanda Daddy ya mallaka musu sunanan a mazauninsu Rufe da Tamfol,dama already makulayan motocin na hannun Saleem..

Malika da Maman Abba sun zaga lungu da Sako na gidan suna yabawa,Tare da jinjinama Daddy irin Kudin daya kashema gidan,komai na Zabinta an saka mata shi,harda Abunda ta Fiso arayuwarta Swimming Fool,Wayyo Dadi kashe Malika Duk da haka sai da tayi kwallar Tunawa Da daddyata ammh bai Hanata Nuna Murnan Tafi jin dadin wannan gidan Fiye da gidansu na Zamfara ba.

Maman Abba kwana daya tayi ta juya Zuwa Zanfara wanda Malika da Saleem suka Mata Sha tara na arziki don Ta nuna musu kara Sosai,Malika bata da Wata damuwa yanzu don Gata ga hajiya,ko banza tana jin kamshinta ba kamar da,da ko kamshin Wani na gida bata ji…

Saleem ya kai Trasafer letter dinshi Zuwa Sabon Headquater su,yayi wasu cike cike kafin Yafara Zuwa office cikin kwanciyar Hankali,dawowar Malika katsina yasa Hajiya ta dawo mata da Dose suna tayata wasu abun don Cikin malika yana da girma Sosai,Dawowarta katsina yasa tafara Zuwa Asibiti Awo asibitin Federal Medical centar katsina, Tunda da suna Zamfara maman Abba ke Zuwa har gida tana mata,Cikinta Watanshi Takwas yanzu ammh sai ka tsaya ka kara kallon yadda yayi Wani girma yana neman Rufe Malika gashi ya Kumburata Sosai Afuska da jiki,tafiya dakyar tashi Dakyar ammh kuma ahaka take Shirin Tafiya Abuja bikin Saleema,wanda Saleem yayi mata bakam Saboda yaga Malika bata da Hankali baisan ina zata da wannan Tulelen cikin ba taje tabama mutane aiki.

Malika batayi Shawara da Saleem ba Ta Turama Ummi Zunzurutun Kudi har Miliyan Talatin,wai gudummuwar bikin Saleema,dana ya marwan Tunda wanchan Lokacin bata bada komai,Sai ga Ummi ta kira Saleem yana office tana tambayanshi Cike da mamaki yake Sanar da ita bai sani ba,yana wajen aiki ammh in ya koma zai tambayi Malikar ita ko koda Ummi ta mata waya tana tambayanta wannan kudin na miye Dariya kadai tayi kafin ta Sanar da Ummi Gudummuwarta,Bakin Ummi bude take Fadin kudin Sunyi yawa,malika tace Allah Ummi basuyi ba,sai dai inda bazaki ki karba ba,Ummi kasa mgana Tayi, illah godiya datayi ta zubama Malika,shikanshi Abbi Dayaji yayi ta mamaki har yayi tama Saleem Fadan yazai bar malika ta dinga Wasa da kudi haka,yakamata ya zauna da ita su Tatauna Abunda ya dace su Dinga yi da Ribar Dukiyarta bawai Shanshanci ba,kaji Abbi????.

Saleema dataji sai gata har katsina Tazo godiya,Malika bata bi takan Godiyar datake mata ba,sai ma Tambayanta datake wata irin mota take so kuma take Sha”awa Saleema bata kawo komai ba tace Vibe motar tana burgeta,gyada kai kawai Malika tayi aiko ko Sati basu da wannan mganar ba sai ga motar Saleema ta iso daga kwatano,Saleema sai da tayi kukam Dadi Saboda Farinciki Ummi da Abbi da hajiya sun kasa mgana,Shikamshi Saleem bai sanin Malika zatama yan gidansu kyauta sai dai yaji lbri daya yi mata mgana Sai tace Gift din Aure ne tabama Saleema da ya Nuna mata kashe Kudin yayi yawa sai da Malika ta maida Abun Fada,tana Tunanin Yanzu don ta bama Ummi yan kalilan kudade,kuma ta Siyama Saleema mota sai yazama Abun mgana,Bataji dadin haka ba,Dole Saleem ya kwaso Rantsuwa da magiya da lallashi ya Dora kafin Malika ta Hakura.

Saleem ya Fara Hawa daya daga cikin motocin da Daddy ya mallakamai Tun yana Raye prado din,Na Malika ko ya saka Aranshi zata koma hawa motar kanta,ammh sai dai ta koyi Tuki don Shi bazai yarda da Wani Direba don wannan ai Salon iskanci ne,kai kana nam Bude da baki wani gardi na gane maka mata,kowani kwalliya tayi yana ankare ta madubi yana Hadiyan yawu????,Ammh bai sanar da ita ba ya bari sai Allah ya Sauketa lafiya.

***.
Biki na Saura Sati daya Bakin lagos suka Sauka Ya marwan da Joda,Ashe joda itama da dan matashin Cikinta har ya Fito,inaga Tun Haduwar Farko tayi gamakatar dashi akofar daki????Malika na jin Joda tazo itama tace zata Tafi,Saleem yace kadama ta sa rai Joda ta Fita lafiya babu inda zata sai ana gobe Daurin Aure zasu Tafi tare,Ranar lahadi su dawo tare,don bazai barta tana yawo da wannan Abun cikin ba,Dole Malika ta Sadadu da,domin Ta tuna karonsu lokacin bikin Joda,shiyasa wannan karon bata Tada Hankalinta ba,in tayi Duba da gaskiya Saleem ya Fada tayi Nauyi da yawa koda Tama je daWurin babu Abunda zata iya,sai ma karama jama”a Nauyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button